← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 93

Sashe 4

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abinda yace sai tayi murmushi cikin jin dad’i tace, “har naji dad’i, da ina ta jin tsoro ko laifi nayi maka shiyasa baka kwana a nan ba. Baby kai kasan haramcin da yake cikin abinda kake son yi Allah ya hana, abinda mutanen annabi lud suke yi kenan a zamanin sa Allah ya hallakar dasu, meye riba ko dadi’i ga abinda Allah baya so?.” Murmushi yayi jin abinda take fad’a wai zata yiwa wa’azi ya shafa kansa yace, “haka ne kam babu riba, yanzu dai ya wuce. Ki shirya kayan ki da misalin karfe biyu jirgin mu zai sauka a Abuja.”

Ta kalle shi da mamaki tace, “Amma kace a nan ni zan zauna mai zai kaini Abuja kuma?.” Yayi murmushi yace, “taya zan iya aiki an Abuja babu ke? Aikin gaggawa ne ya taso min Zamu je mu dawo, ina tabbatar miki da zarar mun dawo ma Paris zamu wuce.” Murmushi tayi ta rungume shi shima ya rik’e ta yana girgiza kai yana ayyanawa a ransa lokacin Fiddausi ya k’are sai dai wata ba ita ba kuma.

A bangaren Yusuf duk yadda ya kai da son daurewa yaje wajan Yaya Adam abin yaci tura, gabadaya ya rasa abinda zai yi yaji dad’i jin sa yake kamar bashi ba zuciyar da tayi nauyi sosai. Ko ya ya rufe ido Ameena yake gani zuciyar sa na mararin ta sosai amma gangar jikin sa tak’i bashi had’in kai akan hakan. Gabad’aya ya rud’e ya rasa gane inda rayuwar sa ta saka a gaba balle ya San inda ya dosa.

Asiya ce ta shigo falon tana bin falon da kallo tare da tab’e bakin ta ta rasa meyasa tunda Ameena ta tafi yafi son zama a b’angaren ta ko me yake ji a ciki oho masa. kallon sa tayi bayan ta zuba masa harara sannan tace, “Wai ni me kake ji a b’angaren nan ne wanda babu shi a nawa?.” Sai a sannan ya d’ago kai ya kalle ta yaga tana bin falon da kallo sai zaga shi take yi.

Dawo da kallon ta tayi gare shi tace, “ka tashi mu koma can bana son zaman da kake yi a nan.” Kamar bazai mata magana ba yayi banza wayar sa tayi k’ara yana dubawa yaga sunan Abbah gaban sa ya fad’i har ta tsinke bai d’auka ba aka sake kira dole ya d’auka ya saka a kunne daga can b’angaren Abbah yace, “Yusuf ka kaiwa Adam takardar sakin k’anwar sa kuwa?.”

Yusuf yace, “ban kai ba Abbah, amma zan kai.”
“Yaushe? Kai bana son iskancin banza da wofi fa, ni zaka mayar karamin mutum ina saka ka abu kana cewa zakayi har yanzu baka yi ba?.”
“Kayi hak’uri Abbah zanje yanzu in sha Allah.”
“Ka tashi ka tafi yanzun nan in ba haka ba wallahi baka je yanzu ba sai ranka yayi mugun b’aci. Baka son yarinya ka sake ta kai takarda kuma ya gagara? Wanne irin iskanci ne wanann?.” Kafin Yusuf ya sake magana Abbah ya datse kiran.

Yusuf ya dafe kansa da hannaye duka biyun gabad’aya ya rasa abinda yake masa dad’i ya furzar da iska daga bakin sa idanun sa a kulle har lokacin ya kasa koda motsi balle yayi magana. A bayyane yace, “ya zanyi ni Yusuf? Komai ya tsaya min cak.” Asiya tace, “lafiya?.” Kallon ta yayi baice komai ba ya d’auke kai. Asiya da take kallon sa take jin abinda yake cewa a waya tace, “ina zaka je yanzu?.” Ya kalle ta bai magana ba sai kawai ya tashi ya hau sama bai jima ba ya sakko ya fita ba tare da yace mata kanzil ba ta bishi da kallo kafin itama ta fito daga b’angaren zuwa nata b’angaren.

#Mai daki
#Book3
#paid
#500

Book3
03

             Yaya Adam yana zaune a falo shida matar sa da yaran sa da kuma Ameena suna kallo,  dan Indai yana gıda to Ameena tana kusa dashi baya bari ta ware kanta ko kad'an balle ta zauna tana tunanin da baya so yaga tana yi. Duk motsin da za'a yi sai ya kalli Ameena sai yaga kallon tv take yi wani abun tayi murmushi wani abun kuma tayi akasin sa. Wani abun tayi magana wani abun tayi shiru ko tace Uhum kawai. Aisha sai hira take janta da ita a haka ta dan sake suna hira amma ba sosai ba.

Bud'e k'ofar falon akayi aka shigo da sallama duk suka amsa suka kalli wanda ya shigo yana tsaye daga bakin kofa yace, "Ranka ya dad'e kana da bak'o a waje." Yaya Adam yace, "Bako kuma? Daga ina?."
"Bai fad'a min daga inda yake ba ya tambaye ni kana nan nace eh yace dan Allah nayi maka magana."
"Sai kuma ka baro wajan ka barshi shi kadai?."
"A'a ai bai shigo cikin gidan nan ba yana daga waje na kuma kulle gate din."

Yaya Adam ya ajjiye Zaytun da take cinyar sa mik'e yace, "Shikenan muje" ya fad'a yana niyar fita Zaytun ta rik'o shi alamun zata bishi ya d'auke ta suka fita tare. Yana fitowa k'ofar gidan yaga Yusuf a tsaye a jikin mota ya hard'e hannayen sa a kirji kansa a sunkuye yana kallon kafar sa kamar wanda bashi da lafiya.
"Kaine kake nema na?" Yaya Adam ya fad'a yana kallon sa. Yusuf ya kalle shi sai yayi saurin d'auke ido daga cikin nasa yace, "Barka da dare Yaya."

"Daddy!" Zaytun ta fad'a da farin ciki tana mik'a masa hannu, sauke ta Yaya yayi daga jikin sa sai kuwa ta k'arasa inda Yusuf yake ya d'auke ta yana mmurmushi shima da farin cikin ganin ta yace, "Ammata kin manta dani."
"Daddy ina ka tafi? Ina chocolate?." Yusuf ya girgiza kai yana kallon ta yace, "na kawo miki." Yaya Adam da yake kallon sa Zaytun ta kalle shi cikin maganar ta da take fita zaka gane mai take cewa tace, "Abba daddy ya zo da chocolate."

Yaya Adam yayi murmushi yace, "ai ya kyauta." Yusuf ya kalle shi ya kasa magana balle ya aiwatar da abinda yazo yi zuciyar sa bugawa take sosai ko kallon Yaya Adam yayi sai gaban sa ya fad'i Yaya Adam yace, "Daman ganin y'ar kane ya kawo ka kenan?." Yusuf ya girgiza kai alamun A'a gabad'aya ya rud'e  ya rasa ta yaya zai bashi takardar sakin Ameena Gashi kuma harga Allah yana so ya ganta amma yasan babu damar hakan, zuciyar sa na fad'a masa hakan ba daidai bane akwai  rashin kyautawa a cikin tunda kamar mahaifi yake a wajan ta bashi takardar sakin Ameena tamkar cin fuska ne.

Yaya Adam yayi tsaki yace, "in kana so zaka iya d'aukar ta ka tafi da ita daman taka ce ni tawa tana cikin gida." Yusuf yayi shiru ya rasa abinda ma zaice ganin hakan Yaya Adam yace, "ina fatan ka tawo da takardar sakin Ameena ko? Dan na fad'a maka kar na ganka a nan in ba takardar ka kawo min ba." Gaban sa ya fad'i ya kulle ido ya bud'e ya furzar da iska daga bakin sa.
"Daddy wani a nan". Zaytun ta fad'a tana saka hannun ta a daidai zuciyar sa dan sosai take jin yadda take bugawa a hannun ta hakan ya bata mamaki shiyasa ta fad'a masa.

Yusuf baice komai ba ya motsa daga inda yake ya bud'e gaban motar ya d'auko leds fara babba mai kyau ya dawo kusa da Yaya Adam ya mik'a masa yace, "Wannan na Zaytun ne." Kallon sa yayi ya kalli ledar ya sake kallon fuskar sa kafin yayi magana yace, "Dan Allah ka karb'a Yaya." Bai mu sa ba ya karb'a ya bud'e ledar a nan yayi karo da takarda fara a kai ya saka hannu ya d'auka ya bud'e yana dubawa.

Baice komai ba ya saka takardar a aljihun sa yace, "Kar na sake ganin k'afar ka a k'ofar gidan nan daga yanzu, in Kana da ra'ayin ganin y'ar ka zaka iya aikowa a d'auke ta amma bana bukatar sake ganin ka daga nan har karshen duniya. Zaytun tawo" ya fad'a yana mik'a mata hannu sai ta kwanta a jikin Yusuf alamun bazata zo ba tana alamun zatayi kuka.

Yaya Adam yace, "Shiekan kaje da ita" ya fad'a yana niyar juyawa ya koma gıda. Yusuf gabad'aya ya rasa abinda yake damun sa gaahi bakin sa yayi masa nauyi in ya tafi da Zaytun wajan wa zai kaita? Bata saba da Asiya ba sannan in ya kai ta wajan Ammah bai  san me zaice ba, shi bazai iya zuwa gidan su da ita ba Allah ya sani dan kowa yana ganin ta yasan abinda ya kawo shi ya karb'a ta kunyar hakan yake ji shiyasa gwara ya barta.

Da sauri yace, "A'a Yaya kaje da ita kawai, Zaytun ki shiga gida wajan Mummy." Yaya Adam ya tsaya cak ya juyo yana kallon sa Zaytun ta saka kuka tace, "A'a ni zan bika."
Yaya Adam yace, "kaje da ita gobe a dawo da ita kawai tunda tana so" yana fad'a ya juya zai shiga gida Yusuf yace, "Dan Allah ayi hakuri Yaya, nayi kuskure amma" juyowar da Adam yayi ya kalle shi sai ya kasa k'arasawa yayi shiru baice masa komai ba ya shiga gıda ya bar masa Zaytun d'in a hannun sa. Badan yaso ba haka ya saka ta a gaban mota suka bar unguwar yana kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo da tab'a zuciya.

           Yaya yana shiga falon ya samu waje ya zauna ya kalli Ameena da take kallon sa k'aramar yarinyar sa mai shekarun Zaytun tace, "Abba ina Zaytun?." Ya kalli Ameena yace, "taga baban ta tak'i zuwa wajena, nace yaje da ita ya dawo da ita gobe tunda ta ganshi a barta a wajan sa kar tazo tana kuka" ya fad'a yana kallon Ameena dan yaga reaction din ta.

Sai kuwa yaga ta kalle shi da sauri suna had'a ido sai ta d'auke kanta amma yanayin ta ya canja duka gabad'aya jikin ta ya saki yayi sanyi sosai alamun bata ji dad'in maganar ba, ajjiye filon kujerar da ta rungume tayi ta tashi kawai ta wuce daki da sauri dan bata so ma Yaya yayi mata wata maganar.
Chapter 4 · 0% Book details