← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 93

Sashe 19

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak ta tsaya kamar an tsayar da ita bata yi gaba ba sannan bata yi baya ba kallon sa kawai take zuciyar ta na bugawa sosai, kamar an d’aure mata k’afa haka take ji shiyasa ta kasa motsawa sai kallo kawai, ganin ta tsaya ba gaba babu baya ya saka shi ya taso yazo inda yake tsaye yana kallon ta itama kallon nasa take yi yace, “Ya kika kasa k’arasowa ?.” Yadda yayi maganar a hankali kuma yana kallon idanun ta ya saka ta sauke kai k’asa ya saka hannu ya d’ago da fuskar ta sai ya rufe idanun ta yayi murmushi ya saki fuskar ya koma ya zauna yace, “Ki zauna Rukayya.”

A hankali ta zauna ta sunkuyar da kanta k’asa bata ce komai ba tana share hawayen tana mamakin wai ita dashi yanzu mata da miji ne, akwai igiyar auren sa guda uku a kanta sai taji wani abu na yawo a jikin ta shiyasa ta kasa banbance a wanne yanayi take ciki, yace, “Kinga lokaci ko Rukayya? Yazo mana a lokacin da ba mu yi zato ba daga ni har ke.” Shiru tayi ta kasa cewa komai har lokacin ta kasa banbance yanayin ta kamar a mafarki haka take ganin komai da yake faruwa ba gaskiya bane.

Ya gyara zaman sa yace, “Na gode da kika amince dani kika bani amanar rayuwar ki, na gode da kika zab’e ni a matsayin mijin da zaki zauna dashi na har abada, na gode da kika zab’e ni a matsayin abokin rayuwar ki. Ni kuma nayi miki alqawarin bazan bari ki yi hawayen bak’in ciki ba sai dai hawayen farin ciki, bazan ce bazan b’ata miki rai ba saboda dan adam ajizi ne yau da gobe sai Allah amma nayi alqawarin farin cikin da zakiyi sai ya ninka akasin sa a zamana dake. Ban San me kike ji a zuciyar ki ba a yanzu amma ko ma meye ki ajjiye shi a gefe, ki manta da batun Ibrahim din baya da kika sani ki canja masa suna ya koma Mu’azzam a yanzu ina tabbatar miki dashi zaki zauna bada Ibrahim din da kike tunani nara tushe a kansa ba. Rukayya!” Ya fad’a Tana kallon ta.

D’ago kai tayi ta kalle shi idanun ta sunyi ja haka fuskar ta yace, “Subahanallahi kukan na meye haka?.” Ta mayar da kanta k’asa bata ce komai ba yace, “Rukayya ana kukan farin ciki amma naki bai yi kama dana farin ciki ba, in akwai damuwa ki fad’a min a yanzu babu wanda kike dashi da zaki fad’awa abinda yake zuciyar ki sai ni; saboda ni ne mijin ki a yanzu.” Kalmar mijin ki da ya fad’a ya saka ta lumshe idanu har lokacin ta kasa tabbatarwa da gaske ne ba karya ba.

Sai a sananan tace, “Babu komai.”
“Ban amince babu ba, nasan kuma meye yake zuciyar ki.” Ta d’ago ta kalle shi yace, “Eh kin san nasan abinda yake ranki a yanzu, na kuma fad’a miki ni kaina bana son tuna abinda ya wuce amma ke ban San meyasa kike son barin sa a zuciyar ki ba. Bana son abinda zai saka ki a damuwa ko kusa, zan iya yin yak’i da ko meye dan nan na Kore shi daga zuciyar ki farin ciki ya maye gurbin sa. Babu Wanda zai canja abinda Allah ya rubuta, Allah ya rubuta zai jinkirta miki aure har sai Ibrahim yayi aure ya haihu yaron ya girma ya rabu da matar sannan zai aure ki, babu wanda ya isa ya canja wannan k’addarar saboda wani baya auran matar wani, ni ne dai mijin ki bayan ni babu wanda zai aure ki tunda ni Allah ya zana a cikin k’addarar ki. To meye kike damun kanki bayan Allah ne ya rubuto miki? Meye na tunanin wani abu da ya riga ya wuce Rukayya?.”

Ya taso ya dawo kujerar kusa da ita ya karkace yana kallon ta yace, “babu wanda zai goge abinda Allah ya rubuta koda iska ce ko ruwan sama, ni ne a zanen k’addarar ki nima kece a tawa kaddarar. Rabuwa ta da wacce yake zuciyar ki ba komai bane face daman hakan Allah ya tsara dole sai ta bar gidan sannan zan aure ki, inda an samu jinkirin rabuwar har yanzu da ina tabbatar miki da Alalh zai iya Karb’ar rayuwar ta saboda lokacin ki ya shiga dole sai na aure ki shi kuma lokaci baya jira Rukayya.” Hannun ta ya kalla ta had’e su waje d’aya tana ta juya su sai ya rik’e su duka biyun ta kalle shi shima ya kalle ta yace, “Ki goge komai daga zuciyar ki ki fuskanci sabuwar rayuwar da tazo miki a wannan lokacin, indai ni ne baza ki tab’a samun matsala dani ba in sha Allah.”

Hannun ta ta zame daga nasa ta girgiza kai alamun gamsuwa yace, “magana zaki yi min.” Tace, “Haka ne abinda kace, zanyi in sha Allah.”
“Yauwa ko Kefa, sai ki yi dariya na gani.” Bata yi dariyar ba ta sunkuya tana kallon fuskar ta yace, “Kiyi dariya na gani.” Murmushin yaqe tayi yace, “wannan murmushin bai kai zuciya ba.” Bata san lokacin da murmushi ya bayyana akan fuskar ta ba sosai jin abinda yace shima yayi ya tashi ya koma wajan sa kafin yace, “naga alama baki da nutsuwa sosai a yanzu” sai ya mik’e yace, “zan tafi ki samu ki yi bacci ki huta sosai, in Allah ya kaimu gobe zamu tattauna.”

Tashi itama tayi tace, “To sai da safe, a gaida Hajiya.” Yazo kusa da ita da niyar wucewa yace, “Hajiya zata ji in sha Allah. Shikenan abinda zaki ce?.” Sai ta kalle shi suka had’a ido ta sauke ido k’asa domin kwarjini yake yi mata sosai musamman yanzu da fuskar sa take a sake sosai ya sake cewa, “tambayar ki nake, shikenan abinda zaki ce?.” Ta d’aga kai alamun eh yayi murmushi yace, “kin tabbatar?.” Ta sake d’aga kai alamun eh yayi dariya mai sauti yace, “shikenan ki kwana Lafiya” ya fad’a yana niyar fita tabi bayan sa da kallo sai ya jiyo ya kama ta tana kallon sa tayi saurin kawar da kai yayi dariya yace, “Na kama ki kuma Rakiya, ni nasan akwai abinda yake ranki amma a na bar miki bashi zaki fad’a min nan gaba.”

Murmushi ta samu kanta da yi a lokacin ya fita daga d’akin ta sauke numfashi tana kallon sama kamar ne duba wani abun kafin ta fito ta dawo falo ta tarar da Umma a zaune tana ta buga waya tana sanar da y’an uwa an d’aura auren Rukayya, kai da ka kalle ta kasan cikin farin ciki take yin wayar.
Zama Rukayya tayi tana kallon Umman da murmushi domin yanzu ta tabbatar da maganar Ameena da take ce mata Umma ta fita damuwa da tayi aure kawai maganar mutane ce ta saka take takura mata amma sai tafi kowa farin ciki in hakan ta kasance, sai gashi ta ga hakan a bayyane akn fuskar Umma.

Umma ta kalle ta tace, “Rukayya ya naga kamar bakya farin ciki?, ko Umar kika so Abban ki ya zab’a miki ba Ibrahim ba?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “kawai ina jin abun ne kamar a mafarki yake faruwa Umma, wai nima a yanzu matar aure ce ina da miji ko yanzu ya mutu sai nayi masa takaba. Wallahi Umma sai naji kamar ba a duniyar nake ba, sai naji kamar ba nice Rukayya ba wata ce daban aka canja.”

Umma tace, “Lokacin da kike ta fad’a min kenan koda yaushe Rukayya, Gashi yazo da yake lokacin yazo baza ki sake kwana ba tare da igiya uku a kanki ba sai gashi a yau aka d’aura auren ki ba tare an shirya wa hakan.”
Rukayya tace, “Umma ashe daman zaman jiran Ibrahim nake yayi aure ya haihu ya saki Fiddausi sannan ya aure ni? Ashe daman shine ya kawo jinkirin? Ashe saboda Allah ya rubuta shine mijina ba wani ba shiyasa qalubale Kala-kala suka dinga faruwa har sai da akazo gab’ar da muke ciki a yanzu. Allah gwanin hikima in ya tsara babu wanda zai canja sai dai in shine yaso Hakan, da gaske ni matar Ibrahim ce tsohon mijin Fiddausi wanda suka rabu, ashe duk zaman jiran da nake yi a gidan nan shi nake jira, Allah kenan” ta fad’a tana girgiza kanta imani da tsoron wanda ya halicce ta suna sake shiga zuciyar ta sosai.

Umma tace, “Allah al-Hakeem kenan gwanin hikima da tsara abubuwan da zai faru a rayuwar bayin sa. Wallahi sai yanzu na amince da duk wani abu bai isa ya faru ba tare da lokaci yayi ba, lokacin yayi shiyasa babu jira akayi komai aka gama ba tare da shiri ba, kamar yadda Baban ku yace in mutuwa ce ma haka za’a tafi ba tare da an shirya ba gashi auren ki ma ya nuna min lokaci ne sai kuma yanzu yazo. Dan nice naga ishara dan keda mahaifin ki kun amince da hakan nice na kasa amincewa. Rukayya badan na tsane ki ba, sai dan ina so naga kinyi aure kamar yadda sa’anin ki sukayi, kowa a y’an uwa tambayar sa yaushe Rukayya zatayi aure?, in naga wanda shekarun ku suke d’aya da yara d’aya ko biyu wallahi sai naji babu dad’i a zuciyata. Yanzu da nake waya ina sanar da mutane auren ki kowa mamaki yake harda masu cewa zasu zo gobe gidan nan, wallahi Rukayya in kin fini farin ciki a auren nan naki to da kad’an ne, amma in da ana shiga zuciya zan bada dama ki shiga tawa kiga adadin murnar da nake yi. Addu’a da mik’a lamarin ki ga Allah da kika yi sai yayi miki zab’i mai kyau dan na tabbatar Ibrahim miji na gari ne a wajan ki.”
Chapter 19 · 0% Book details