Sashe 36
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajan bikin suka zo ya tsaya ya kalle ta yace, “to k’arfe nawa zaki gama bikin?.” Ameena tace, “wallahi ban sani ba dan ban sani bama ko an fara.”
“To ki saka min number ki in yaso in kin gama sai ki kira ni nazo na d’auke ki.”
“Da ka barshi ma ba sai ka dawo ba bazan rasa wanda zai kawo ni a ciki ba sboda duk na san su.” Fuska taga ya d’aure ya kalle ta yace, “nima kamar Adam yake in baya nan nine madadin sa, ban amince ki shiga motar kowa ba ki bani number ki in kin gama zan zo mu tafi.”
Ameena tace, “To.” Waya taga ya mik’a mata ta saka number nan take ya kira ta shigo yace, “Yauwa jeki.”
“Na gode.” Ta amsa tana fita ta shiga wajan bikin. Kid’a ne yake tashi tun daga bakin gate daga can gefe kafin ka shiga wajan bikin ta hango Ammah da su Yayan Abuja a tsaye sunyi kyau sosai kowa ya sha kwallaiya ba kamar Ammah kamar ba ita ba. kamar baza ta k’arasa ba dan ji take wani iri a jikin ta sai kuma ta daure kafin su gani ta Zaytun ta ganta tace, “Mummy!” Ta fad’a tana yin gudu zuwa wajan duk sai suka kalli wajan.
Nan take farin ciki ya bayyana a fuskar Ammah ganin Ameena ta k’arasa Ammah tace, “ai Humaira tana nan tayi fushi dake.” Tayi dariya suka gaisa Yayan Abuja tace, “ko ni nayi fushi ba Humaira ba, sai yanzu ma zaki zo.” Ameena tayi dariya tace, “na rasa wanda zai kawo ni ne Yaya ya hana ni tukin dare shiyasa na jima ban zo ba.”
Ammah tace, “ai kam ya kyauta dan tsaf a tare ki a kwace motar. Ma sha Allah Daughter kinga yadda kika yi kyau kuwa?.” Ameena tayi dariya Yayan Abuja tace, “Wallahi Ammah, kamar ba ita ba dan baza kice tayi aure tana da yarinya kamar wannan ba, lallai Ameena mai Yaya Adam yake baki?.”
Dariya tayi kawai bata ce komai ba dan wallahi nauyin su yake ji sosai Ammah tace, “Allah kamar ba ke ba, kodan na jima ban ganki bane?.” Ita dai murmushi take yi kawai Ammah ta kalli Yayan Abuja tace, “wai ina wanda nace ya kawo min jakata ne? Wayata tana cikin jakar nasan ana ta kira na ina ya tsaya bazai kawo min ba.”
Mubarak da yake tsaye yace, “Yusuf ne wallahi shi yace gashin an zai kawo miki har yanzu bai zo ba, gashi nan ma.”
“Mtsww! Kuma ku rasa waye zai kawo min jakata sai Yusuf? Meyasa kai baka koma ka d’auko min ba?.” Mubakar yace, “zan koma kika ce fa na tsaya a nan akwai bak’in da zasu zo na basu kati” ya fad’a yana kallon bayan su ko zai ga Yusuf din.
Mubakar yace, “Yauwa gashi nan ma ai.” Zaytun ce tayi wajan sa suka k’araso tare Ameena tana wajan a tsaye ko gezau batayi ba dan tayi alqawarin baza ta nuna ta ganshi ba in kuma ya zama dole baza ta nuna amsa komai ba, kamar yadda zasu gaisa da Mubakar haka zasu gaisa dashi ta wuce. Yana zuwa Ammah tace, “Kai komai sai ka b’ata lokaci.” Baice komai ba ya bata jakar bai ma kula da wacce a wajan ba Zaytun tace, “Daddy ga Mummy” ta fad’a tana nuna masa ita gaban Yusuf ya fad’i sosai ya d’ago ido ya kalle ta yaga bashi take kallo ba ita da Yayan Abuja suke magana kamar ma bata san yana wajan ba.
Juyawa kansa yake yi tun ranar da suka rabu sai ranar ya ganta hankalin sa yaji yana neman barin jikin sa zuciyar sa na bugawa sosai yayi kamar zai fad’i Allah ya taimaka ya tsaya ya dafe kansa baice komai ba. Ammah na kallon sa tana kuma kula da yanayin sa Ameena ta burge ta sosai da bata rud’e ko ta nuna wani abun ba da ta ganshi tayi tsaki tace, “muje ciki.” Tare suka wuce Ameena suna ta hira da dariya kamar bata ganshi ba nan kuwa sarai ta ganshi akwai bata da lokacin masa magana ne. Dakyar ya iya barin wajan ya shiga mota ya tafi zuciyar sa na bugawa sosai ba tare da yasan dalilin faruwar hakan ba.
Ameena ta sake a cikin mutane Ana ta hidima da ita da yawa wanda basu san Yusuf ya sake ta ba d’auka suke matar Yusuf ce har lokacin. Sai gab da za’a tashi ta kira Al’ameen yazo ya mata waya yace gashi tazo ta fito kamar su Ammah suce ta tsaya mama baby yadda zasu yi haka ta fito gashi tace baza taje dinner ba. A waje ta ganshi a mota ta shiga da sallama ya amsa yaja motar yace, “Har an gama bikin?.” Tayi murmushi tace, “eh an gama.”
“Yayi kyau.” Ya fad’a yana cigaba da tafiya har suka zo k’ofar gidan ya tsaya ta kalle shi tace, “Na gode Yaya Al’ameen.” Yayi murmushi yace, “Nima na gode sosai.” Ta kalle shi ganin irin kallon da yake mata sai ga d’suke kai ya fita daga motar ta shiga cikin gidan, sai da yaga an mayar da k’ofar an rufe sannan ya k’arasa nasa gidan yana ji a ransa ya zama dole ma ya san abinda zaiyi ya mallaki Ameena.
Bayan kwana biyu.
#Book3
#Mai daki
#Nana Haleema
Book3
021
Adam da Al’ameen suna tsaye a k’ofar gida suna hira Ameena ta dawo daga makaranta tazo wuce su a k’asa tace, “Ina wuni.” Al’ameen ya amsa yana kallon ta yace, “ya na ganki a k’asa? Ina Salisu din?.” Ameena tace, “Yaya ne ya aike shi ya tsaya a nan farkon layi ni kuma na gaji gida nake so shiyasa nace zan k’araso k’afa shi ya tsaya.” Al’ameen yace, “ai dole, shiga k’i huta.” Ta bud’ egate din gidan ta shiga ya bita da kallo har ta kulle sannan ya kalli Adam yace, “Dan Allah na tambaye ka.”
Yaya Adam yace, “ina jinka.”
“Ina da wata dabi’a mara kyau da ka hana ni tunkarar Ameena da abinda ya jima a zuciyata?.” Yaya Adam yayi murmushi yace, “ai ina jin ni ne zan zo a mutum na farko da zai fara yabon halayyar ka, in ban zo a na farko ba zan zo a na biyu. Ba hana ka magana da Ameena nayi ba Al’ameen kawai dai….” Ya katse shi ta hanyar cew, “Kawai me? Indai har da gaske bani da wata dabi’a mara kyau ka bani dama nayi magana da ita, kai kace min masu sonta suna ta zuwa kai kake dakatar dasu meyasa ni baza ka bani dama nazo ba?. Adam kafi kowa sanin ina son Ameena so na hakika meyasa kake yin abu kamar zan cutar da ita in ka bani ita?.”
Adam ganin Al’ameen ya d’auki zafi sai yace, “Ko kusa Al’ameen, ni kunya nake ji ashe kana abokina babba amini kazo kace kana son kanwata. Abun kamar da raini a ciki.” Al’Ameen yace, “Kai kake ganin haka ni bana gani, kaine sarkin son girma ni babu wannan a gabana wallahi, ka bani dama naje ga Ameena na fad’a mata abinda yake zuciyata watakila ni ne mijin ta na biyu.”
“Shikenan to zan sanar da ita zuwan ka sai ku zauna ku tattauna.”
“Yau nake so hakan ta kasance ba gobe ba.” Adam ya kalle shi yace, “umarni kake bani kenan?.”
Al’ameen yace, “oho maka dai. Kai bafa sai ka bani dama ba, wallahi naga dama zanje na same ta kai tsaye ai Nima Yayan tane ina da ikon bada auren ta sai na bawa kaina.” Yayi dariya ya kalle shi yace, “to a haka zan baka ita baka girmama ni?.” Al’ameen ya harare shi shima yayi dariya baice komai ba ya shiga gida. Aisha matar sa ya samu a d’aki ya shiga yana cewa, “Aisha Al’ameen ya takura akan sai yayi magana da Ameena, ni ban san taya zan fad’a mata Al’ameen yana sonta ba wallahi” ya fad’a yana dariya tare da zama a kan gado. Aisha tayi dariyar itama tace, “Fad’a mata zaka yi ai kawai, Al’ameen irin mijin da zaka aura mata ne.” Ya girgiza kai yace, “dari bisa dari kuwa, Al’ameen mutum ne yasan darajar ilyalan sa sosai. Duk inda kike tunanin Al’ameen ya wuce haka. In ma kud’in ne yana da kud’i fiye da tunanin ki kawai shi ba wani lokacin bai da ya nuna ba ne.”
Aisha tace, “to ka gani ai abu ne mai kyau.”
“hutun mu ya kusa k’arewa zamu koma Kalaba nan da y’an kwanaki in na zan jima ban dawo ba, ban sani ba da ita zamu tafi ko an ina zamu barta?.”
“Tafiya da ita ai bazai yu ba ka manta tana makaranta? Tafiyar da in mukayi bamu San lokacin da zamu dawo ba?. Ai baza mu tafi da ita ba sai dai na zauna a nan mu zauna tare.”
Yaya Adam ya jinina kai yace, “bara na same ta naji ya zata karb’i batun Al’ameen” har zai fita sai kuma ya dakata yace, “in anyi sallah naje yanzu tana hutawa naga ta gaji sosai.” Aisha tace,”ni so nake tayi auren ma wallahi a kwanakin nan.”
“Meyasa kika ce haka?.”
“Saboda a cikin abinda ya raba auren ta harda maganar rashin sauke hakki da bata samu har yake shan magani, duk da yanzu tasan bata da aure baza ta saka abun a ranta da zai dame ta ba amma yau da gobe sai Allah.” Yayi shiru yana jinta yace, “haka ne maganar ki, zan same ta naji ga zamuyi da ita” ya fad’a yana tashi ya fita.
Bayan sallar magriba suna tare da ita a falo Yaya Adam ya kalle ta yace, “Ameena ta.” Ta kalle shi tana murmushi yace, “Akwai bak’on da zai zo wajan ki in anyi sallar i’sha.” Ta d’ago da sauri ta kalle shi ya d’aga mata kai yace, “ya takura akan sai kunyi magana Ameena na dakatar dashi ya dage akan na taimaka na bashi dama ku tattauna. Zai zo anjima Kuyi magana.”