← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 93

Sashe 66

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ibrahim ya amsa da Amin kafin Abba yace, “yanzu da ban ganka ba tafiya zakayi baza mu gaisa ba.” Ibrahim ya murmusa yace, “A’a Abba daman zan shiga mu gaisa.”
“Ni nasan hakan, kar na tsyaar dakai Alalh ya kai ku Lafiya ya dawo daku Lafiya.” Ya amsa da amin Abba ya tafi shi kuma ya shiga mota. Yana zaune a motar ya hango wata mace da hijjabi ash kala ta tana tunkaro inda yake sai da tazo daf dashi ya gane wacece sai ya kulle idanun sa ya bud’e a lokacin ta wuce shi ta shiga gidan su Rukayya.

Numfashi ya sauke ya jingina da kujerar yana girgiza kai Wato komai na duniya fararre ne kuma kararre. A bayyane yace, “badan ma ta rabu dani ba da rayuwata bata canja haka ba, da watakila ina nan ina Shan gorin bani da wannan bani da wancan. Ni na gode Allah ina sake gode masa da ya saka Fiddausi ta rabu dani silar hakan Rukayya ta shigo rayuwata. Allah na gode maka da kayi min chanji mafi alkhairi.” Yana zaune yana murmushi sai ga Rukayya ta fito da Amir da kuma fiddausi Amir Fiddausi ta rik’e shi suna tunkaro motar da yake. Fiddausi yaga ya tsaya tana yiwa Rukayya magana harda hawayen ta sai yaja tsaki yayi murmushi yace, “Rayuwa kenan.” Rukayya ce ta k’araso ta shiga motar Amir tana d’aga mata hannu Ibrahim yaja motar suka bar unguwar zuwa gidan su. T murmushi taga yana yi yana kallon ta itama tayi murmushi tace, “me yake saka ka murmushi haka?.” Ya sake yin murmushi yace, “murmushin mallakar ki matsayin mata nake yi.” Tayi yar dariya tace, “Gaskiya akwai wani abun bayan wannan.” Yayi dariyar shima baice komai ba suka cigaba da tafiya.

Y’an uwa an cika a gidan ana ta murna wannan yana ni abaya za’a siyo min wannan zamzam, wani turare takalmi wannan yace dabino. Shigar su ya saka gidan ya sake rikicewa ana ta murna sha d’aya na rana tana yi aka tafi kaisu airport cikin farin ciki da ko wanne sun yake ciki.

Yusuf yana kwance akan kujera yana abinda ya saba wayar sa sai k’are take yak’i ya kalle ta balle ya kula wayar, gajiya yayi da kiran ya d’auko wayar ya duba ganin bakuwar lamba sai yayi tsaki ya d’auka daga can b’angaren akace, “kana magana daga nan police station na fagge. Muna magana da Yusuf ne?.” Yusuf yace, “eh shine.”
“Mun kama matar ka Asiya da laifin satar sark’a ta kuma je zata siyar.”

“Kar ka sake cewa matata ni ba matata bace ba, sannan ni ban san wa kake magana a akai ba.”
“Asiya dai matar ka domin ita ta bamu lambar ka tace kaine mijin ta, da zaka zo da zaka ga komai ka kuna ji komai.” Yusuf tunani yayi kodai sark’ar Abba ce tunda gashi ance taje zata siyar, tunanin hakan ya saka yace, “shikenan zan turo” yana fad’a ya yanke wayar ya kira Mubakar ya tura shi dan ya karb’o sark’ar ba wai ita ba.

Yusuf ya sake yin shiru bayan ya gama wayar yana tunani abinda yake damun zuciyar sa yayi yawa, zuciyar tayi masa nauyi sosai gabad’aya baya jin dad’in zaman duniyar komai ya fita daga ransa. A bayyane yace, “Yanzu haka zan zauna bani da mafita?, Ina na saka gaba?, Ina zan saka Raina ne?.” Tashi yayi ya canja kaya ya fito ya hau mota ya wuce gidan Usman. Usman yana ganin sa ya girgiza kai yace, “ina kuma zamu je?.”
“Kayi hak’uri dani bani da wanda ya fika. Zan koma gidan su Ameena ne Usman, ko meye zai faru sai dai ya faru amma wallahi sai naje. İn an aiko da gawata kayi min addu’a” ya fad’a yana fita Usman ya biyo shi yace, “Yusuf kar kaje dan Allah, ka manta abinda yayan ta yace ne? In kaje yanzu duk abinda yayi maka kai ka ka siya da kudin ka.”

Yusuf yace, “wallahi sai naje, ko meye zai faru sai naje wallahi. Shiyasa nazo na fad’a maka koda zan mutu a can.” Usman yace, “Shikenan ka jira muyi sallar azahar sai na raka ka.” Yusuf ya juyo ya kalle shi yace, “ni yanzu nake son zuwa.”
“Gaggawa daga shaidan take ka jira muyi sallar sai mu je.” Yusuf ya dawo ya zauna Usman ma ya zauna ya kalle shi yace, “Yusuf kana son Ameena har haka ya akayi kayi sake har ta kubce maka dan Allah?. Yadda ka fita daga hankalin ka ya tabbatar min da kana sonta sosai.” Yusuf ya kalli Usmsn yace, “k’addara da rabon na sha wahala, k’addara da rabon na gane mahimmaci Ameena, k’addara da rabon na gane ita kawai nake so, k’addara da rabon na gane Ameena ba irin matan da za’a samu da sauki bace ba Usman. K’addara da rabon na banbance meye asalin so a zuciyar mutum, wallahi son da nake mata yanzu ya ninka na baya sau babu adadi.” Usman ya sauke numfashi yace, “haka ne. Amma yanzu baka ganin in ka komawa yayan ta yanzu akwai matsala?.”
“Ko meye Matsalar zan jure.” Usman yace, “shikenan to.” Suna nan zaune har akayi azahar suna idarwa suka d’auki hanyar gidan Adam.

A lokacin suna tare da Al’ameen suna tattauna yadda za’a yi bikin a gama kafin ya tafi Kalaba, Adam yace, “tunda a nan zaku zauna sai ta cigaba da karatun ta.” Al’ameen ya kalle shi irin kallon nan na Anya zatayi karatu Adam yace, “Wallahi kana cewa baza tayi ba an soke wannan auren, ai tun farko na fad’a maka da batun makarantar nan kuma ko na gaba wallahi baka isa ka hana ta ba.”

Al’ameen yayi dariya yace, “ikon Allah! kana bani mamaki Adam, nida matata kace min wai ban isa na hanata ba?.”
“Ai fad’a maka nake, wallahi sai taje makaranta ka daina min wani kallo daga wannan munafukin glasses din naka na makafi.” Al’ameen yayi dariya yace, “nima bance zan hana ta ba ai?, karatu zatayi daga nan har taga karshen littafi.”
“Yafi maka dai” Inji Yaya Adam yana haraarar sa.

Al’ameen yace, “Yanzu gobe za’a fara aikin wannan gidan nawa Ina ha Allah.”
“Me za’a gyara? Naga gidan yana da kyaun har yanzu.”
“Amarya da zan saka, ai sai a sake fenti an canja komai na gidan wallahi. Bani da wanda zai gaje ni in na mutu ga mata zan saka wacce zanyi fatan zata haifar min magada. Meye amfanin kud’in in ba’a kashe su yanzu ba?.”

Adam yace, “lallai kanka rawa yake akan yarinyar nan.” Al’ameen yace, “bari ayi auren ma, wannan shegiyar tsawar da kake mata wallahi ka sake sai na baka mamaki.” Adam yayi dariya yace, “wannan kuma kayi kadan, tun kafin ayi d’aran akayi kwandi.” Sukayi dariya su biyun kafin yace, “bara na kira Ameenan muji yaushe ne zasu fara exams din in suka gama ayi bikin a gama.”

Yaya Adam ya d’auki waya ya kira ta yace ta same shi a falo ba jimawa sai gata ta zauna tana sunkuyar da kai Al’ameen yace, “matar ki daina wannan jin kunyar dan Allah, Adam ne fa ba wata tsiya ba in kina haka sai ki saka yaga kamar ma bakya sona.” Murmushi tayi kawai Adam yace, “in baka bini a sannu ba zan nuna maka mahaifin tane ni.”
“In ka fasa baka qauanr Allah, kai dole ma ayi auren nan da wuri wannan gadarar da kake min ni ne zan yi maka ita nan gaba.”

Adam yayi dariya yace, “Kai dai k sani” ya kalli Ameena yace, “Kina ji Ameenatu? Yaushe zaki fara exam?.” Ameena da take murmushi dramar su na bata dariya ta bud’e baki zatayi magana aka shigo falon da sallama sun suka amsa tare da kallon wanda suka shigo. Yusuf yana shigowa ya tsaya cak daga gefe bai k’araso ba Adam ya kalle shi yace, “baka jin magana ko?.” Yusuf ya girgiza kai yace, “bana ji indai akan abinda nazo dashi ne, kayi hak’uri na taka umarnin ka amma wallahi ko naman jikina zaka saka ana yanka bazan daina zuwa ba.”

Adam ya kalli Usman yace, “a gaban ka nayi masa warning meyasa ka bari yazo?.” Usman yayi shiru Yaya Adam yace, “alfarmar da kake ci zaka daina cin ta, daga wannan lokacin lokacin zaka yi dana sanin wani Adam a rayuwar ka.” Kawai Yusuf ya zube a wajan a k’asa kan tiles yace, “koda gawata za’a fita da ita daga gidan nan na amince indai zaka saurare ni. Wallahi bazan fasa cewa ina son Ameena ba, bazan fad’a cewa ina son mayar da ita ba, bazan fasa cewa nazo neman auren ta karo na biyu ba.” Wani irin tafasa zuciyar Adam tayi ya taso a haukace yazo wajan sa ya saka hannu d’aya ya d’ago shi yace, “y’arka da iyayen ka ya saka nake raga maka amma naga abin baka yayi yawa baka san kara ba ko?.”

“Na Santa, itace ta ta saka nazo nan. Meyasa ka kasa yarda nayi na gane kuskurena kuma zan gyara shi a wannan lokacin?.” Bai san ya mare shi ba saboda yadda zuciyar sa take tafasa sai ganin tsallen jini yayi akan tiles wanda ya fita daga bakin sa saboda azaba da zafin Marin. Yusuf sai da kunnen sa yayi dummm ya d’ago bakin sa a fashe ya kalle shi yace, “Wallahi ko yanka ni zakayi bazan daina fad’a ba” ya sake zubewa a k’asa yace, “laifi nayi n sani amma a sake bani dama wallahi zan rik’e Ameena fiye da kowa a duniyar nan, zan bata farin cikin da babu wanda zai bata shi a duniya, zan tabbatar da kwanciyar hankalin ta fiye da ko wanne lokaci a duniya. Duk abinda ake tunani wanda ya gabata ya wuce wallahi bazai sake faruwa ba, a wannan Karon babu zubar da hawaye a kan Yusuf sai saj hawayen farin ciki. Burina, fatana ka amince min ka bani dama.”
Chapter 66 · 0% Book details