Sashe 60
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya sunkuyar da kai ya kasa amsawa Adam yayi dariya kad’an yace, “in ma shi kake nufi ni mamaki abin ya bani, abin da ya faru watannin baya baza’a zo baza hak’uri ba sai yanzu?.” Yusuf yayi shiru Usman sai yace, “Wallahi Yaya Yusuf ya shiga wani hali ne a kwanakin baya banbance daidai da ba daidai ba shiyasa ya kasa zuwa duk da zuciyar da tana so yazo din amma sai ya kasa.”
“Allah Sarki, rashin lafiya yayi kenan?” Yaya Adam ya fad’a yana kallon su daga shi har Yusuf din.
Duk sun kasa cewa komai sai Yaya Adam yayi murmushi yace, “Yanzu ka fad’a min abinda ya kawo ku sauri nake yi.”
Yusuf yace, “wallahi Yaya nayi kuskure nayi kuma dana sanin abinda na aikata, dan Allah dan girman Allah ayi hak’uri a yafe min in akwai dama ina so naga Ameena dan Allah.” Yaya Adam ya kalli Zaytun , “ke Zaitun kira babar ki.” Ta sauka daga jikin Yusuf ta tafi ciki ya kalli Yusuf yace, “in tazo ka bata hak’urin shikenan dai ko?.” Yusuf yayi shiru baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba sai ga Ameena ta fito tace, “Yaya gani.” Ya kalle ta yace, “Yusuf ne yazo baki hak’uri, gashi a zaune ki k’araso ya baki hak’urin ki hak’ura ki koma ciki ba shikenan ba dai ko Yusuf?” Ya fad’a yana sake kallon sa shi kuwa zuciyar sa bugawa take yi sosai jin abinda yake cewa kamar da biyu yake fad’a.
Ameena tayi turus tace, “Wanne Yusuf kuma Yaya?.”
“Yusuf dai baban yarinyar da take kusa dake, Kizo ya baki hak’urin ki koma ci cigaba da karatun ki.” Tace, “to Yaya hak’urin me zai bani kuma?.”
“Nima abinda nace masa kenan ai, amma ki k’araso ki zauna kawai.” Ba musu ta k’araso ta zauna a akan kujera ba tare da ta kalle shi ba Yaya Adam yace, “To Yusuf gata nan bata hak’uri.”
Sai Yusuf ya kasa komai kamar an saka igiya an d’aure masa jikin sa haka yake ji ya kasa ko motsin kirki balle ya kalli Ameena ya kalli Yaya Adam da yake kallon sa ya kalli Ameena da suka had’a ido sai ta kalli Yaya tace, “Yaya karatu nake fa.” Ya kalli Yusuf yace, “ta ta tafi ne baka da abinda zaka ce?.”
Kai ya girgiza ya kalle ta ita kuma ba shi take kallo ba yace, “Ameena!.” Sai yayi shiru a fusace tace, “Na’am.” Idanu ya kulle ya bud’e su a kanta ya sake kallon ta yace, “Kiyi hak’uri akan abubuwan da suka faru, kin san abinda zan aikata kin san wanda bazan aikata ba, kin san halina kin san wanda ba halina ba. Duk abinda na aikata kuskurena ne dan Allah kiyi hak’uri ki yafe min duk abinda nayi miki, nayi miki laifuka da yawa wanda ni kaina bazan iya lissafa su ba amma nasan kin san su, dan girman Alalh badan ni ba darajar wacce take kusa dake a zaune ki yafe min Ameena.”
Ameena tayi shiru fad’uwar gaban da ta jima bata ji ba taji a wannan lokacin abubuwan da suka faru suka dawo idanun ta ta kulle idanun ta bud’e ta dawo da nutsuwar ta a tare da ita ta bud’e tace, “sai yanzu kasan kayi laifi kenan? Sai yanzu zuciyar ka ta raya maka kazo ka bawa Ameena hak’uri ko?” Sai tayi murmushi tace, “to kaje ka jira lokacin da naga damar yin hak’urin zanyi amma yanzu banga dama ba kuma banyi niya ba.”
Sakkowa yayi daga kan kujarar ya sauke guiwar sa a k’asa yana kallon ta yace, “nasan nayi laifi nasan nayi kuskure nasan na b’ata miki na k’ona miki zuciya, watakila ma bakya son ganin fuskata ko kiji maganata, amma hak’uri ki yafe min shine burina shine kuma fatana, sai kin yafe min zanji dadi a zuciyata wallahi. Yafiyar ki nake so a wannan lokaci dan na tabbatar sai kin yafe min zan samu sassaucin abinda nake ji a zuciyata.
“Bazan yi hak’urin ba sai me?.”D’ago ido yayi ya kalle ta sai ta mik’e zata bar wajan ta kalli Yaya Adam tace, “Yaya bana son tunawa da abinda ya wuce meyasa ka bashi damar shigowa har cikin gidan nan? Yaya baka son ganina cikin damuwa meyasa amma ka bar damuwar ta shigo har tana magana Dani?, wallahi ganin sa kawai damuwa ce a wajena domin bana son tunawa dashi balle na ganshi wallahi.”
“Kiyi hak’uri dan Allah, badan halina ba darajar iyayen ki Ameena ki yafe min.”
“In dan halin kane kai kama isa kazo inda nake na fito? In dan halin kane ka isa kazo ka zauna a gabana kana cewa nayi hak’uri?, In dan halin kane shima yayan bazai barka ka shigo gidan nan ba balle ka samu damar zama a falon gidan har kana cewa wai nayi hak’uri to bazan yi ba. Yusuf bazan yi ba akwai abinda zaka yi ne?” Ta fad’a a fusace cikin tsiwa da rashin kunya.
Yaya Adam ya kalle ta yace, “Ameena ki nutsu
mana a gidan Yayan ki kike fa, hak’uri ne kawai in kinga zaki iya sai kice nayi hak’urin shikenan ta ba wani abun yake so ba bayan wannan.” Ameena ta koma ta zauna Yaya yace, “İn zaki hak’urin kice kinyi, in baza ki ba shikenan ai ba abin tashin hankali bane ba.”
Yusuf ya sunkuyar da kai hawaye ya fara sakko masa Zaitun kallon sa take ta kalli Ameena tace, “Mummy daddy kuka” ta fad’a tana jan rigar Ameena tana nuna mata Yusuf da yake hawaye sosai kamar an kunna famfo. Anty Aisha ce ta shigo tana kallon su har zata koma sai Yaya Adam yace, “k’araso mana, tsohon mijin Ameena ne yazo bata hak’uri.” Aunty Aisha tace, “baban Zaitun kenan?.”
“Shi fa, gashi a zaune.” Yusuf ya d’ago idanun sa ya sake kallon Ameena yace, “Kiyi hak’uri ki yafe min dan Allah.” Ameena kallon sa take yi ganin kuka da yake yi sai jikin ta ya d’an yi sanyi rashin kunyar da take ji da ita sai taji ta ragu bawai dan tausayi ba sai dan ganin babba kamar sa yana kuka ga kuma Zaytun ta tafi wajan sa ta rik’e shi itama tana kukan.
Yaya Adam ganin jikin ta yayi sai yace, “zaki iya yin hak’urin ko baza ki iya ba?.” Tayi shiru kamar bazata ce komai ba kafin tace, “zan yi hak’uri kodan saboda Ammah, amma badan shi ko wani abun bashi ba. Zanyi hak’uri saboda y’an gidan su kaf amma badan shi ko shirgin sa ba” ta kalle shi tace, “kar ka saka a ranka nayi hak’uri saboda ka zauna a gabana kana kuka ko wani abun, sam sam wallahi, nayi ne saboda Ammah amma bayan ita kai baka isa na tsaya ma ina magana da kai ba wallahi. Nayi hak’urin shikenan ko?” Ta fad’a tana aika masa da harara.
Yusuf bai iya cewa komai ba Yaya Adam ya kalle ta yace, “koma ciki.” Ta koma ciki ko waiwaiye babu ya kalli Yusuf yace, “to tayi hak’uri shikenan abinda kake so ko?.” Yusuf yana kuka sosai ya kalli Adam yace, “Yaya dan Allah ka sake bani Ameena a karo na biyu, nayi maka alqawarin….” Kallon da yayi masa ya saka Yusuf kasa magana yayi shiru gaban sa ya fad’i sosai domin lokaci d’aya fuskar ta canja daga sanyi zuwa zafiii mai tiriri sai ya sunkuyar da kai yana jira yaji saukar Mari a kuncin sa dan wannan kallon da yake masa bana mutunci bane, na nuna zallar rashin mutunci ne akan fuskar sa.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
Book3
32
Kallon sa kawai Yaya Adam yake b’acin ran da yake dannewa lokacin da suka wuce yaji yana tasowa ya bishi da kallon wulakanci yace, “tashi tsaye.” Jikin Yusuf a sanyaye ya mik’e tsaye Usman ma ya tashi ya kalle shi yace, “Dan na sakar maka fuska na baka dama ka shigo har cikin gıdana shine ka samu damar yi min wannan banzar magana?, ni zaka kalla ka cewa wai kana so na sake baka Ameeena a karo na biyu? Ni kake fad’awa wannan maganar dan baka da mutunci baka da kunya baka san ma kunya ba ko?. Ko cocaine din da aka kama a motar ka daman sha kake? Dan in ba wanda ya sha kayan maye ba babu wani irin ka da zai zo yayi min wannan banzar maganar har cikin gidana.”
Yusuf jikin sa har rawa yake amma ya daure domin yaji ya gani yace, “Wallahi Yaya a wannan karon bazan yi abinda nayi a baya ba, zan rik’e Ameena hannu biyu zan bata dukkan farin ciki da ban bata ba a wancan lokacin, Yaya alqawari na d’auka kuma zan cika ka bani wata damar wallah….” Cikin tsawa ya katse shi yace, “zaka yi min shiru ko sai tsinke fuskar ka da marukan da zai saka kunne ka ya daina ji?. Alqawarin da ka yiwa mahaifinta yana kwance a gadon asibiti yana gangarar mutuwa shi baka cika ba sai nawa zaka cika?. Ni zaka kalla ka cewa wai zaka rik’e Ameena, ni zaka cewa zaka bata farin ciki Yusuf?.” Ya sunkuyar da kai yana kuka sosai Usman ganin haka yace, “Yaya kayi hak’uri, amma ka sake bashi damar watakila a yanzu ba Yusuf din baya bane ya canja bazai sake maimaita abinda yayi ba a baya. Ni shaida ne Yusuf din baya ba na yanzu bane ba wallahi.”
Yaya Adam ya kalle shi yace, “ba da kai nake magana ta ba, lokacin da ya dinga wulakanta min k’anwa baka nan” ya kalli Yusuf yace, “in na sake ganin k’afar ka a k’ofar gidan nan wallahi sai na saka an maka dukan tsiya, in y’ar kace gata nan ka tafi da ita ka bar min tawa a nan daman ai ba da ita taje gidan ka ba. Da kuskure, da wasa, da zolaya ka sake furta min irin wannan banzayen kalaman wallahi Yusuf sai na nuna maka waye Adam, sai na nuna maka waye a gaban ka a tsaye.”