← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 93

Sashe 26

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka Ammah take yi sosai shi kansa Abbah ya rasa ma abinda zaice dan Umman Asiya ta shayar dashi mamaki sai yanzu ya fahimci maganar Ammah da take yi kafin auren ta kan ce basu da tarbiyya yau gashi ya ga rashin tarbiyya daga wajan babar su bama ita ba.
Yusuf ya kasa koda motsi ya sunkuyar da kai k’asa jikin sa yayi masa sanyi sosai kukan Ammah yake ji a har cikin zuciyar sa sai dai ko kusa ya kasa jin haushin Asiya akan abinda tayi masa, yana jin b’acin rai amma kuma daga wani waje daban ba daga wajan Asiya ba.

Abbah yace, "to ai kaji abinda iyayen ta suka ce maka, ko ka daina shan giya ko kuma ka sakar mu ya. Kaga wacce take da gata kenan ba wacce ka dinga wahalarwa dan kaga babu iyaye ba, ban tabbatar da cewa yarinyar da ka bari ka cutar da ita ba sai yanzu, ban tabbatar da cewa ka tafka babbar asara ba sai yanzu Yusuf. Bazan ce ka daina shan giya ba kasa. daidai k'asan ba daidai ba, in ka daina kanka in baka daina bama kanka babu abinda zai dame ni. Abinda na sani ban tab'a zaton a cikin ahlina za'a samu baragurbi kamar ka ba, ban tab'a d’auka za'a samu mai shan tab'a bama sai gashi mai shan giya aka smau gabad’aya. Komai ka aikata rayuwar ka ka cuta Yusuf kaje kayi duk abinda kake ganin daidai ne,
matar dai da ka zab’a tana tare d akai ga rayuwar da ka zab’arwa kanka nan kaje Allah ya bada sa'a." Yana gama fad’a ya tashi ya bar masa wajan Ammah kuwa ta kasa tashi kuka tane sosai.

Magana yake so yayi mata amma ya kasa cewa komai lokacin Humaira tazo ta zauna a kusa da Ammah duk da bata san meya faru ba amma tasan damuwar Yusuf ce ya kalli Amma zaiyi magana tace, "bana son aji komai daga bakin ka Yusuf, tashi ka baki waje ko kallon fuskar ka bana so." Baice komai din ba kuwa ya mik’e tsaye ya fita zuciyar sa nayi masa mugun d'ci yana kuma sake yin alqawarin ya daina shan giya daga wannan ranar, ya raya a zuciyar ss ya kuma yiwa Allah alqawarin bazai kuma Shan giya ba daga wannan lokacin.

Book3
016

Yusuf tuk’i yake yana hawaye yana kuma gogewa da bayan hannun sa gabad’aya duniyar tayi masa zafi sosai ya rasa inda zai nufa yaji dadi a zuciyar sa. Tafiya yake kawai har yaje k’ofar wani gıda ya faka ya kifa kansa a sitiyarin motar ya rasa meye yake damun sa abinda ya sani baya Jin haushin Asiya a gangar jikin sa amma zuciyar mugun tsanar ta yake ji akan abinda tayi sannan kuma yana dana sanin Shan giya a rayuwar sa.

D’agowa yayi ya d’auki waya ya saka a kunne kafin yace, “ina kofar gidan ka dan Allah fito.” Abinda yace kenan ya yanke wayar ya mayar da kai ya kwantar kamar wanda aka yiwa mutuwa. Usman ne yazo yaja handle din motar yaki bud’ewa sai ta dan daki glass din ya d’ago ya kalle shi sai ya danna lock ta bud’e ya shiga ya zauna yana kallon sa yace, “Meyasa baza ka shiga ciki ba?.” Shiru bai bashi amsa ba hakan ya saka ya kalle shi sosai yaga gabad’aya ya canja yace,”kai kuma lafiya kake?.” Yusuf ya d’ago ya jingina da kujera yace, “Usman ban san me yake damuna ba.” Usman ya bishi da kallo yace, “Meya faru?.”
“Yau Ammah tasan ina shan giya Usman, kuka Ammah take a gabana tana cewa Allah yayi wadarai na. Meyasa nake b’ata mata rai ne?. Meyasa dani kad’ai Amma take kuka?.”

Umsan yayi tsaki cike da jin haushi yace, “Au kai tun da baka shirya wa wannan ranar ba ka fara sha giya? Da kai duk baka shirya wa b’acin ran Ammah ba kake kafa kanka a shan giya Yusuf?. Ai na d’auka ka shiryawa ranar ne ta yadda Ammah tana samun labari kasan abinda zaka yi bazata shiga damuwa ba. Ka gode Allah da bata yi maka baki bana dan abinda ka aikata ba abu bane n wasa Yusuf.” Yusuf yace, “nayi dana sani Usman, na tsani kaina, naji abinda ban tab’a ji ba. daga yau in sha Alalh bazan sake ba nayi alqawarin bazan kuma ba.”
“Alqawarin na biyar kenan da kayi min akan baza ka sake ba ka daina?.”

A raunane yace, “zan daina yanzu, wallahil azim zan daina, ban tab’a jin kunya kamar ta yau ba Usman, nan tab’a jin an muzanta ni kamar yau ba. Na kasa had’a ido da iyayena Usman.” Usman yace, “kunyar duniya ma kenan, ka kasa had’a ido da iyaye saboda abinda kayi sai ka tuna da had’a ido da zakayi da mahaliccin ka in ka mutu a wannan yanayin shi kuma ya abin yake?.” Girgiza kai yake cike da Dana sani da nadama da alqawarin dainawa yace, “na daina, nayi alqawari da wanda ya halicce ni, nayi alqawari da wanda yake bani ikon numfashi daga yau ni Yusuf na daina shan abinda shan. İn kuma na sake Allah kar kasa naji dad’i zaman duniya da lahira.” Usman ya kalle shi da sauri yace, “kana da hankali kuwa? Wannan fatan da kake yiwa kanka fa?.”
“Dan ka tabbatar na daina ne Usman, dan ka tabbatar yanzu da gaske nake bazan sake sha ba in sha Allah. daman tsautsayi ne da zaman k’asar turawa, amma na daina kuma in sha Allah.”

Usman cikin jin dad’i yace, “in da gaske kake sai nace Allah yasa hakan, zan fi kowa jin dad’i in hakan ta kasance ai.” Ya sauke numfashi sannan ya kulle ido yace, “Amin. Na gode Usman.” Usman yace, “amma waye ya fad’a musu?.” Ya kalli Usman sai Umma ya sake cewa, “to naga kace Ameena ce kawai ta sani naga kuma yanzu bakwa tare, me zai saka ta fad’a yanzu bayan tun a da bata fad’a ba?.” Yusuf ya runtse ido yace, “in kuka ambaci sunan nan ji nake kamar ana tafasa min jinina wallahi, ni kadai nasan abinda nake ji duk sanda aka ambaci sunan ta, dauriya kawai nake. Zuciyata na son sunan ta amma gangar jikina kamar Ana zuba min ruwan zafi.”

Usman ya bishi da kallo yace, “tofa, to Allah ya kyauta. Waye ya fad’a mata?.” Yusuf ya sauke numfashi yace, “Asiya ce.”
“Sabuwar matar ka kenan, Wato ita baza ta iya rufa maka asiri ba sai ta fad’a, tayi min daidai ai watakila silar shiryuwar taka Kenan.”
“Usman ko kusa bana jin haushin ta, soyayyar ta tana nan a jikina bana so na rasa ta Usman.”

Usman ya bishi da kallon mamaki yace, “wai ita Asiyan?.” Ya d’aga masa kai alamun eh Usman yace, “to waye yace zaka rabu da ita?.” Shiru yayi bai amsa ba yayi shiru Usman ya dinga binsa da kallo kafin yace, “Yusuf anya kana addu’a kuwa?.” Sai kuma Usman ya sake cewa, “to ina kaga lokacin addu’a ma?, kaje aiki ka gaji ka dawo kasha giya ka kwanta ina lokacin neman tsari da bautawa wanda ya halicce ka?.”

Yusuf bai iya bashi amsa ba ya sake cewa, “lamarin ka akwai buk’atar addu’a a ciki ka mayar da hankali akan rok’on Allah komai kake ji zai zama tarihi. Amma sai kana addu’a dan gabad’aya rashin addu’a ya saka kake jin abinda kake ji a yanzu, mai taimaka maka kayi ibadar ka rabu da ita wannan kuma ba abinda tazo yi kenan ba.” Idanun sa ya bud’e ya kalli Usman yace, “zanyi.”
“Ya dai kamata.” Yusuf ya kunna motar yace, “zan koma.”
“Zaka iya tuk’a motar?.” Ya d’aga masa kai alamun eh Umsan ya bishi da kallo yace, “to Allah ya kiyaye” ya fad’a yana fita shi kuma ya juya motar ya koma ta inda ya biyo.

Washe gari da safe Yusuf ya shirya ya hau mota kai tsaye gidan su Asiya ya wuce dan dakyar ya iya yin bacci saboda jikin sa kasa kwanciya yayi saboda babu Asiya. A k’ofar gidan su ya faka zuciyar sa ta hana shi fitowa ya kulle ido ya bud’e ya kira wayar ta a lokacin tana zaune a falo ama shan shayi sai yamutsa fuska take yi ita baza ta sha haka ba sai an soya mata Kwai.
Ganin yana waya ya saka ta kalli Umma tace, “Umma shine yake waya fa.” Umma tace, “Dan banza, d’auki muji.” Ta d’auka ta saka a kunne sai kuma ta sauke tace, “Umma wai yana k’ofar gida.” Umma tayi shewa ta tafa hannu tace, “Momi tashi kije ko shigo dashi, ke kuma tashi ki koma ciki, Fauziyya tashi ki gyara falon kafin ya shigo.” Asiya ta tashi tana cewa, “ni gwara ma na koma na jima ban sha shayi babu madara ba sai yau” ta fad’a tana shiga ciki.

Kwashe kayan falon akayi da gaggawa aka fesa air freshener kafin suji sallamar Yusuf ya shigo, Umma ta masa tana cewa, “maraba, shigo ka zauna mana kamar bak’o.” K’arasowa yayi jikin sa a sanyaye ya zauna a kan carpert yace, “Umma barka da safiya.”
“Barka dai Yusuf, an tashi lafiya.”
“Lafiya lau, a same ku lafiya.”
“Lafiya lau muke.”
Yusuf ya gyara zama yace, “Umma nazo mu koma da Asiya ne, in sha Allah abinda ya faru bazai sake faruwa ba, nayi kuskure wannan shine ma k’arshe.” Umma ta gyara zama tace, “yanzu naji batu ai Yusuf, da ace kana dukan yarinya da cikin ka a jikin ta kamar baka sonta?. Har suka girma ban tab’a dukan su ba sai dukan wasa, akan me ka d’auke ta da haqoranta guda talatin a bakin ta ka ce zaka dake ta?, kaima kasan ai kuskure ne hakan baka yi daidai ba. Kar a sake wannan kuskuren dan anayi na gaba bazan d’auka ba wallahi.”

Yusuf yace, “anyi na k’arshe da yardar Allah.”
“Sai batu akan giya, Gaskiya baba amince yarinta ta zauna da dan giya ba, haka kawai kaje ka shayu kazo ka cillo ta taga ka balla min ita ka cuce ni ba.”
Kamar zai zubar da hawaye haka yake ji, zuciyar sa na bashi umarnin ya tashi ya bar musu gidan amma ya kasa sai yace, “Shima daga wannan baza’a sake ba in sha Allah, ayi hak’uri.”
Chapter 26 · 0% Book details