Sashe 37
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameena tace, “Amma Yaya kace sai na gama makaranta.” Aisha tace, “ko a gidan ki zaki k’arasa karatun ai Ameena.” Yaya yace, “babu wanda zan bari ya aure ki sai anyi yarjejeniya akan zai barki ki cigaba da Karatu. Sannan ai ba auren sa zakiyi ba kawai na bashi dama ne akan yazo ya ganki ba wani abun ba.” Ameena tace, “To Yaya.”
“In Anyi sallah sai yazo ku gaisa.” Ta amsa da to tana zaune bata sake cewa komai ba har akayi kira ta tashi ta shiga d’aki tayi sallah.
Bayan ta idar da wani lokaci taji yana kiran ta hijjabi kawai ta saka suka fito tare da Zaytun Yaya ya kalle ta yace, “Yanzu zai shigo, ki zauna.” Ba musu ta zauna suna ta hira da Zaitun a zuciyar ya tana mamakin itace ta fara zuwa kafin shi maimakon shi yazo kafin ita, Al’ameen ya shigo da sallama tare da k’arasowa ta amsa tana kallon sa da murmushi tace, “sannu da zuwa Yaya Al’ameen .”
“Yauwa Ameena sannu” ya fad’a yana zama Zaytun taje wajan sa ya d’auke ta yana yi mata wasa.
Kallon Ameena yayi yaga da alama bata san shine bak’on naya ba sai yayi murmushi yace, “Zaytun jeki wajan Anty zan aiko miki da alawa.” Da sauri ta shiga ciki tana tsalle-tsalle ya kalli Ameena yace, “Nime bak’on da Adam ya fad’a miki zaka yi.” Da sauri ta kalle shi jin abinda yace wai shine bak’on nata da akace zatayi to ta ya ya?. Ganin yana mamaki sai yayi murmushi yace, “kinyi mamaki ko?.”
Ameeena ta sunkuyar da kai dan ita abun dariya ma yaso bata tayi sa’a ta rike dariyar yace, “Nasan zaki yi mamaki Ameena amma ba abun mamaki bane dan tun kafin ki yi auren farko naso Yayan ki ya bani ke amma sai yak’i.” Murmushi yayi tare da girgiza kai yace, “A karo na biyun ma yanzu dakyar ya bani wannan damar nan, ban sani ba ko gani yake yi na miki tsufa dai shi ya sani.” Dariyar tace ta fito fili tayi kad’an amma bata ce komai ba yace, “Gani nazo ina so na shiga cikin jerin masu son auren ko a wannan lokacin, bazan bari ki kubce min ba kamar lokacin baya ba zanyi abinda zanyi dan ganin na rik’e ki da kyau kin kasa kwacewa.”
Ameena ta d’ago tayi murmushi amma bata ce komai dan ita fa mamakin abun ma take yi wai shine yake sonta, Al’ameen yace, “Na tab’a aure amma matar tawa da abinda yake cikin ta tun kafin yazo duniya sun rasu a hatsarin mota da suka yi, yanzu bani da kowa iyaye sun jima da barin duniya mata ma haka, sai y’an uwa.” Ameena tace, “Allah ya gafarta mata yasa tana aljanna.”
“Amin na gode. Ke nake so ki zamar min komai Ameena, ke nake so ki zamar mata ki zaman min iyaye wanda zan dinga kalla ina farin ciki kamar ko wanne yaro. Ameena da gaske ina sonki so na tsakani da Allah wanda tun kina k’arama yake a zuciyata. Tun wannan lokaci har yanzu soyayyar ki tana nan a zuciyata dan ke na fara so bana tunanin soyayyar ki zata gushe koda mutuwa nayi nasan da ita zan bar duniya a zuciyata. indai kika bani dama baza ki yi dana sani ba Ameena zan kasance miki tamkar Yaya Adam wajan kula da tarbiyyar ki, sannan zan zamar miki tamkar dan aikin ko komai kike so shi zan miki Ameena.”
Shiru tayi bata ce komai ba ya sake cewa, “Tsakani da Allah kina ji a zuciyar ki zaki iya aurena?.” Ameena bata d’ago ba tayi shiru yace, “amsa zaki bani Ameena zaki iya aurena?.”
“Wallahi ban sani ba duk abinda Allah ya tsara min shine daidai a wajena, bani da Zab’i zan iya ko bazan iya ba indai Allah ya iya min Alhamdulillah” ta fad’a a sanyaye bata kalle shi ba.
“Hankalin ki da nutsuwa kamar yadda kika nuna yanzu shine ya sake dasa min soyayyar ko a zuciyata, ina ji a jikina kamar silar aurena dake ne Allah ya kaddara mutuwar auren ki. Ko wacce kaddara tana da sila komai na duniya yana da mafari yana kuma da k’arshe.” Ta girgiza kai tace, “haka ne kam.”
“Ina fatan mafarin k’addarar mu nida ke ya kasance a wannan lokacin, ina nan ina fad’awa Allah ya sa Ameena ta kasance mallakina a wannan lokacin.” Tayi dariya kawai bata ce komai ba yace, “yadda kike dariyar nan da murmushi Allah yasa har zuciyar ki kike yi ba iya fuska ba.”
Ta sake yin murmushi dan ita dariya yake bata ba wani abun ba tace, “Amin.”
“Kar na cika ki da magana ya kamata na tafi na barki amma bana son tafiyar ji nake ina ma mu kasance a haka har abada.” Sai kuma ya mik’e yace, “na tafi Ameenatu ina fatan in na sake dawowa zan samu kalamai masu dadi’i daga wajan ki.” Ta mik’e itama tace, “Na gode sosai, Allah ya bamu alkhairi” ya amsa da amin ya fita yana jin zuciyar sa fess ko babu komai ya fad’i abinda yake zuciyar sa wanda ya jima yana damun sa.
Yana fita Anty Aisha ta fito falon sai Ameena ta kalle ta ta fashe da darıya tace, “Anty wai Yaya Al’ameen ne yake sona, abin mamakin bai ji kunya ta ba ya zauna dani yana fad’a min yana sona kamar ba shine abokin Yaya ba.” Anty Aisha ganin Ameena ta mayar da abin wasa sai tayi dariya tace, “Bafa abin dariya bane Ameena da gaske sonki yake kuma auren ki zaiyi in kin bashi dama.”
“To ni da ba aure zanyi yanzu ba.”
“Za dai kiyi ko wanne lokaci ne zaki yi auren, kuma gwara irin su masu hankali wanda aka san halin su akan wanda ba’a san hali ba.”
“Tab, ni wallahi dariya abin yake bani sosai fa Anti.”
Anti tayi dariya tace, “zai daina baki darıya ranar da akace an d’aura auren ku.” Ameena ta wara idanu tace, “wai!” Sai ta sake yin dariya sosai kafin ta shiga cikin daki tana jin nishadi a zuciyar ta bata san dalilin zuwan sa ba.
Yusuf yana zaune a falon Ammah shida Amma yana cin abinci amma babu wanda yake magana a cikin su ita waya ma take dannawa shi kuma ya saka abincin a gaba yana ci kad’an-kad’an ture abincin yayi ya jingina da kujera ya kulle idanun sa kafin yace, “Ammah zuciyata bugawa take yi ban san dalili ba.” Ammah ta kalle shi cikin kwanakin tausayi yake bata sosai ya gama fita daga hayyacin sa kana kallon sa zaka gano hakan a tare dashi tace, “Sannu, kai ta maimaita Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un zaka ji dad’i.”
Ya lumshe idanun sa baice komai ba tace, “kaci abincin wannan ramar da kake yi da yunwa Yusuf.” Ya girgiza kai yace, “Babu Yunwa Ammah, ba Yunwa bace damuwa ce tayi min yawa.”
“Allah ya yaye maka” ta fad’a tana cigaba da danna wayar ta amma zuciyar ta na tare dashi.
Mubakar ne ya shigo ya shigo Tana cewa, “Ammah dan Allah bani lambar Mummyn Zaytun.” Ammah ta kalle shi tace, “lafiya dai?.”
“Mtsw! Tun bikin Humaira ranar kamun nan wani abokin ango ya ganta aka had’o dashi ya takura min shi ko lamabar tace na bashi, wallahi a kullum sai yayi min magana yafi sau biyar. Naga alamun serious sonta yake shiyasa zan bashi lambar ta na huta da magana dashi.”
Ammah tace, “ai da gidan su ka kwatanta masa yaje yayi magana da Yayan ta kafin ita indai da gaske.” Mubakar yace, “Hakan za’a yi, ai ban san gidan ba” sai yayi gaba yace, “bara na kira Humaira ta bani full address din gidan sai na tura masa na huta Nima” ya fad’a yana ficewa Amma tace, “in ya samu Ameena yayi sa’ar da ba kowa ne yake yin irin ta ba. Wasu ko sunyi irin ta sai suyi wasa da ita ta kubce musu.”
Kallon Yusuf tayi taga ya runtse idanun sa sosai yaja numfashi mai tsaho kafin ya cize bakin sa yace, “Ammah zuciyata tana yi min zafi sosai, ki bani magani dan Alalh, Ammah zafi nake ji” ya fad’a a gigice kamar bashi ba, da sauri ya taso tazo inda yake tace, “Yusuf lafiya kake? Me kake ji a zuciyar taka?.” Nuna mata kirjin sa yake yana jan numfashi sosai kamar ciwo yana hakki yana gumi kamar yayi gudu.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!” Amma ta fad’a hankali a tashe tana buga fuskar sa tace, “Yusuf! Yusuf!! Kana jina?.” Numfashi yake ja a hankali ta d’auki ruwa ta d’aga kansa ta bashi yasha ya kwantar da kansa akan table din da yake zaune yana cigaba da jan numfashi a hankali a wahalce. A hankali numfashin nasa yayi daidai ya bud’e idanun sa da suka yi ja sosai ya kalli Ammah ta rik’o hannun sa tace, “taso ka dawo kan kujera zaka fi sakewa” tashi yayi ya dawo kan kujerar ya zauna ta zauna kusa dashi tace, “Sannu, babu abinda kake ji yanzu?.”
Girgiza kai kawai yayi baice komai ba ta zuba masa ido kawai tana kallon sa bata ce komai ba itama. Abbah ne ya shigo falon ya k’araso ya zauna yana kallon su ita da Yusuf din yace, “to Lafiya dai?.” Ammah ta nuna masa Ysusuf da kana kallon sa kasan ba Lafiya yake ba yace, “bashi da lafiya?.”
“Babu Lafiya, Kaga yadda numfashi sa ya dinga yin sama d’azu kafin ka shigo ? Bai jima da dawowa daidai ba.”
“Yusuf akwai abinda yake damun ka ne?.” Ya kalli Abbah yace, “komai damuna yake Abbah, ina jina kamar ba mutum bane ba ni.”
“Allah ya kawo mafita.” Ammah ta amsa a bayyane shi kuma yayi shiru.