Sashe 21
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon Naja’atu tayi ta girgiza mata kai tace, “kar kije bai san mahimmancin alqawari ba, bai San meye rantsuwa ba kika bishi kin yiwa kanki.” Ya kalli Fiddausi yace, “kar ki amince da abinda take fad’a miki, naga ban kyauta miki ba na d’auko ki daga gidan ki ga d’anki bai kamata nayi haka ba shiyasa zan kai ki gida, kar ki amince da abinda take cewa ki shiga mota muje in ba haka ba baki da damar zuwa ko ina.” Kallon Naja’atu tayi tana hawaye itama hawaye take tace, “Zanje Naja’atu gida za’a kai ni.” A guje ta tashi ga shiga cikin gidan tun kafin ya shiga ta riga shi yayi dariya ya kalli Naja’atu yace, “ki koma malama.” “Sai na kashe ka” ta fad’a tana barın wajan da sauri yayi dariya ya d'auki waya ya saka a kunne yace, "A shirya jirgin yanzu gamu nan zamu tawo da ita" fad'a ya yanke wayar yabi bayan ta ya shiga suka shiga cikin gidsn.
A falon ta ta tsaya daga nesa dashi kana kallon sa kasan bata da lafiya ta rame a lokaci d'aya kamar zuk’e ta tace, "Da gaske zaka kaini gidan mu?." Ya matso kusa da ita tayi saurin yin baya kamar zata fad’i tace, "Kar ka tab'a ni, bana so ka tab'a ni ka fad’a min gaskiya zaka kaini gidan mu?" Sai ta fara kuka hawaye na sauka daga idanun ta wani yana bin wani tana kallon sa.
Yayi murmushi yace, "inda bazan kai ki ba ai bazan miki magana ba, ke kin san ban tab’a yi miki irin haka ba, kije ki shirya kayan ki." Fiddausi jikin ta har rawa yake yi tace, "basai na canja kaya ba zan tafi a haka basai na d’auki komai ba." Yayi dariya ya kalli ta yace, "muje to" ya fad'a yana yin gaba ta biyo bayan sa jikin ta har rawa yake yi sosai zuciyar ta na fad’a mata kar ta bishi amma ta kasa sarrafa kanta domin idanun ta a rufe yake gida kawai take son zuwa.
Mota suka shiga gabad'aya a tsorace take dashi shi kuwa farin ciki yake a zuciyar sa sosai zai samu ninkin kudin da ya samu a lokacin da ya gabata, nan da nan suka isa airport da yake a private jet zasu je babu zancen ticket suna sauka jirgi suka hau ya tashi zuwa k’asar America.
Tafiya ake yi sama da awa d'aya a sannan ta kalle shi tace, "wai har yanzu bamu shiga kano ba?.” Kallon ta yayi yana dariya a zuciyar sa yace, "kiyi bacci ki tashi mu kusa zuwa." Bata son yin magana dashi hakan ya saka ta yin shiru amma a zuciyar ta mamaki take har yanzu basu zo kano ba bayan tasan tafiyar Abuja zuwa kano baya wuce mintina arba’in amma ace har yanzu kusan awa biyu basu shiga Kano ba.
Bacci take son yi amma tsoron sa take ji sosai baza ta iya ba gani tane in tayi bacci zai sake yi mata wani abun shiyasa ta kasa baccin duk motsin sa tana gani bai kuma yi k’ok’arin koda rik’e hannun ta ba. Idanun ta biyu har jirgi ya fara sauka suka fito daga ciki tana bin airport din da kallo ganin kamar fa ba ta Kano bace amma batayi magana ba dan bata son magana dashi kawai ta biyo shi saboda rashin mafita. babbar mota ce bak’a tazo d'aukar su ya shiga amma Fiddausi tak’i shiga sai kallon sa da take yi. Yace, "ki shigo muje." Kai take girgizawa tana ja baya yace, "in baki shigo ba babu inda zaki iya zuwa, ki shigo babu abinda zan miki."
Bata shiga ba sannan bata daina kallon sa ba yace, "Ba'a Nigeria kike ba a k’asar America kike, in baki shigo ba baki da inda zaki je kuma wallahi suka kama ki sai kin je prison." Sai a lokacin ta kalli mutanen da suke yawo a wajan taga duk turawa ne ta kalle shi tace, "Amma ba haka kace min na, meyasa ka kawo ni nan? Me zanyi a nan? Ni gida nake so naje bazan bika ba” ta fad’a tana kuka sosai dana sanin bin sa na mamaye mata zuciyar ta.
"Ki shigo kawai Malama koma meye ai zaki ji."
“Bazan shigo ba” ta fad’a zata gudu yayi hanzarin kamo hannun ta ya jata da k’arfi ta fad’o motar aka kulle aka tafi. Jikin ta rawa yake tana kuka tace, “Allah ya isa, ban yafe ba Allah ya tsine maka albarka.” Bakin ta ya toshe dan bata son maganar ma da take yi duk da ba ji mai motar yake yi ba, kafin su je zazzab’i ya rufe mata jiki.
A harabar gidan suka tsaya ya fito Fiddausi tak’i fitowa ya kalle ta yace, "ki fito mana." Tace, "bazan shiga ba."
"İn baki fito da k'afar ki ba wallahi zan saka sa d’auko ki."
"Bazan shiga ba wallah, ka mayar dani gidan mu bana son zama a nan." Turawa guda biyu ya kalla cikin harshen turanci yace, “a kawo ta ciki" ya fad'a yana yin gaba abin sa kafin tayi aune an d’auke ta a sama an bi bayan sa da ita.
A falon aka ajjiye ta zata fita yayi saurin rik’o hannun ta yaga ba a hankalin ta take ba yace, "ki nutsu Malama bana son hauka da shirme, ba burin ki zuwa kiyi rayuwa a America ba? Yanzu Gashi kin samu meye na wannan rashin hankalin?."
Girgiza kai take yi tana cewa, "yanzu bana so, ka mayar da bai Nigeria bazan zauna ba, bazan zauna ba ka mayar dani. Bana son zaman nan gida zanje, ka mayar dani gida na gaji da rayuwa da kai, ka barni na koma kafin na mutu.” Ganin tana yi masa hauka ya saka shi tsinke ta da marin da sai da gefen bakin ta ya tashe cikin fusata yace, "Ko ki yi min shiru ko na saka ayi miki mugun duka, ina yi miki magana kina yi min shashanci sa'an kine ni? Ban haife ki ba?."
Sai da ganin ta ya d’auke na wasu lokacin kafin ta dawo daidai jikin ta na rawa sosai tana kuka yaja tsaki ya zauna ya kalle ta yace, "kud’i zaki samu kudi zan samu, ki nutsu ki shiga hankalin ki muyi maganar abinda zai kasance kin k’i.” Kuka take yi sosai ta lafe a jikin bango kamar marainiya yaja k’aramin tsaki ya tashi ya fita daga gidsn ya barta a wajan.
Bata san adadin lokacin da ta kwashe a wajan ba a nan baccin wahala ya d’auke ta ta cure waje d'aya kamar almajira, magana ta fara ji a kanta hakan ya saka ta mikewa zaune tana kallon su ta ganshi tsaye shida wani bature sai kallon ta yake yi yana murmushi. Alhaji ya kalli Fiddausi yace, "ke baya jin hausa nasan kin iya turanci, to kiyi duk abinda yake so ki d’auka shima mijin ki ne kamar ni. Ko nawa kike so zai baki, ko me kike so zai miki kar Kiyi masa hauka" ya dawo kusa da iya ya tsuguna yace, "wallahi in kika sake kika aikata akasin abinda nace sai na lahira ya fiki jin dad'i, ki amince masa yayi duk abinda yake so dake ki saka a ranki dani kike tare ba shi ba. Fiddausi in kika yi masa abinda kika yi min wallahi maza zai saka su rik’e ki sai yayi abinda yake so sannan ya kyale ki gwara ma ki hak’ura ayi komai cikin nutsuwa a gama dan nan ba Nigeria bane,”
Fiddausi jikin ta dai rawa yake kawai ta rasa ma abinda zatayi dan kamar bata ma fahimtar me yake cewa sai kallon kawai da take bin sa dashi kamar ta zare. Bata san ya akayi ba taga dai babu mijin ta sai bature da yake kallon ta yana ta murmushi kafin taga ya matso kusa da ita yana shafa fuskar ta.
Abinda ya dawo da ita daga da ita hankalin ta kenan ta zabura ta mik’e tayi baya ya sake biyo ta yana murmushi cikin harshen turanci yace, "meye yake faruwa ne Baby? Tunda na ganki naji ina sonki zan baki duk abinda kike so indai zaki amince dani. Ina son dan Nigeria kamar ki ki amince dani zan baki duk abinda kika nema."
Jikin ta bai daina rawa ba bata daina ja da baya ba yana biyo ta, ganin yadda jikin ta yake rawa a nan ya tabbatar tsoro take ji ya d'auki waya ya Kira Alhaji Bello yana d’auka yace, "ya naga bata amince ba? Bata so ne?."
"Sir kayi amfani da ita koda ta k’arfi ne in akace za'a bita a hankali bazata yarda ba."
"A'a bana son tilasta ta gashi kuma ina sonta" ya fad'a yana kallon Fiddausi da bata ma fahimtar abinda yake cewa dan bata nutsuwar ta.
Alhaji Bello hankalin sa ya tashi baya son rasa wannan harkar yace, "ta haka kawai zaka same ta in ba haka ba bazata amince ba." Datse kiran yayi ya matsa kusa da Fiddausi yana kallon ta sai yaga tana baya da sauri ta d’auki kwalbar lemo da yake kan table a wajan tana nuna shi da ita shi kuma yana murmushi yana binta. "Kar ka tab'a ni, kar kazo Inda nake, kar ka tab'a ni" daidai lokacin da ya kawo hannun sa gare ta sai kuwa ta buga masa kwalbar gefen kansa nan take ta fashe ya sunkuya dafe da kai ita kuma ta fita a guje.
Caraf taji an yi sama da ita a lokacin da ta fito d’in kafin wani lokaci police sun bayana a wajan aka saka mata handcuffs aka saka Fiddusi a mota aka tafi.
A gidan su a Ibrahim gabadaya y'an uwan sa sun zo an saka shi a gaba ana ta tsokanar sa ana cewa angon Rukayya shi dai sai murmushi kawai amma baya cewa komai. Yaya Hadiza tace, "sai murmushin murna kake ka kasa magana." Hajiya tace, "ke kuwa ba dole ba, yarinyar akwai shiga rai wallahi. Fatana da burina Allah yasa ba irin halin k’awar tane da iya ba."