Sashe 38
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah ya kalle shi yace, “ka tashi kaje gida ka huta.” Yusuf ya mik’e ya fita baice komai ba yana fita Ammah ta kalli Abbah yace, “lamarin a Yusuf Wallahi akwai saka hannu a ciki.” Ya kalle ta yace, “maganar da muka gama yi da Usman abokin sa Kenan, yace min dan Allah a mayar da hankali aman Yusuf dan yana cikin damuwar da zata iya yi masa illa fiye da tunanin mu.”
“Kaji ko, dan Allah mu dage a kansa a fara yi masa addu’a da saukar alkur’ani ko zai dawo daidai.” Abbah ya kalle ta yayi murmushi yace, “Keda kika ce ko mallake ke shi matar zata yi ta mallake babu ruwan ki? Meyasa kike son a samo masa magani yanzu?.”
“Yayi kuskure, kuskuren da ya aikata ne suke bbibiyar sa sakayyar Ameena yake gani tun ba’a je ko ina ba. Amma hakan ba yana nufin zamu watsar dashi bane in bamu taimaka masa ba waye zai taimaka masa?.” Abbah yayi murmushi jin yadda take magana a sanyaye yace, “haka ne, na saka ayi saukar alkur’ani akwai kuma wani maganin sirihi da naji wani malami ya bayar na ganyen magarya na saka a had’a masa sai ki dinga bashi yana sha tunda yanzu kusan kullum yana wajan ki. Na jima da sakawa Ana yi masa addu’a sannan kema ki dinga dagewa a kansa wajan sallah, in kuna tare kice masa ya dinga karanta alkur’ani ko yayi lazumi, ki daina barın sa haka yana zaune yana wannan tunanin na banza.”
Ammah tace, “to Allah yasa a dace.”
“Amin, ki kwantar da hankalin ki haka sakayya take akwai zafi sai ka fita daga hankalin ka wallahi. Yusuf ma ai tayi masa da kyau.” Ammah ya girgiza kai bata ce komai ba Abbah ya shiga ciki ya barta da tunanin mafita, daman yasan dole magantu ita uwa ce bazata so ta cigaba da ganin sa haka ba dole zuciyar ta ta karye.
Yusuf yana komawa gida wajan Asiya ya shiga bai same ya a falo ba ya hau sama zai shiga d’akin sa ya jiyo shewar ta tana cewa, “Shiyas nake yin ki uwata gari, yanzu sabon salon da ya dauko kenan zama a gidan su, ni so nake ya daina ya ma daina zuwa gidsn kamar yadda ya fara a baya ya zama daga ni sai ni, Ameena kuma ta barshi har abada dsn yadda muka raba su bazai sake waiwarta ba in sha Allah.”
Abinda yaji kenan bai tsaya ya sake jin wani abun ba ya bud’e d’akin ya kalle ta maimakon taji tsoro ta kashe wayar sai tayi dariya tace, “gashi nan ma ya dawo daga wajan Ammah din, Sannu d’an Ammah” ta fad’a tana kallon sa cikin rainin hankali. Kashe wayar tayi ya kalle ta kamar zai magana sai kawai ya fasa ya fita ya zauna a falo.
A tsaye ya ganta a kansa tace, “sai ka dinga shigo min gida babu fara’a akwai abinda nayi maka ne?.” Bai magana ba tace, “kana jin ai abinda nace ko?.” Nan ma yayi shiru tace, “kana ji fa.”
“Ameena bana son magana.”
“Kutmar uban can, Ameena kace fa?.” Kallon ta yayi ya kulle ido sunan ne kawai yazo bakin sa yaji ya furta ya bud’e ido zaiyi magana tace, “sai ka fad’a min wajan ta kaje? Dawo da ita kake so kayi kenan ko?. Dan tsabar wulakanci da iskanci ka kalli idona kace min Ameena dan bura’ubanci?. Tambayar ka nake wajan ta kaje?.”
Ihu take masa a kansa shi kuma baya so ko maganar ma baya so amma hakan ya saka ya mata banza kamar ba shi take ba tace, “to wallahi in ma dawo da ita zakayi ya kamata ka San abin yi, dan na rantse da Allah baka isa ka dawo da Ameena gidan nan ba, ta riga ta fita kenan gidan nan nawa ne ni kadai babu shegiyar da ta isa ta sake zama a cikin sa in ba ni ba.”
Tashi yayi ya bar mata falon ya sauka ya fita daga b’angaren ta zuwa b’angaren Ameena, dan baya son magana balle tashin hankali shi kad’ai yasan abinda yake ji a zuciyar sa. yana shiga ya zauna akan kujera sai kuma ya zamo kan tiles dan babu carpet a falon ya kwanta a k’asa din yana juyi zuciyar sa kamar zata buga haka yake ji yace, “Allah ka kawo min mafita, Allah ka yafe min” abinda yace kenan yana sake juya kansa ji yake damuwa zata iya saka zuciyar sa ta buga a wannan lokacin.
Ya jima a haka kafin ya daina juye juyen da yake yi yayi shiru yana kallon hoton Ameena da yake kafe a falon har lokacin ba’a cire ba kawai yaji hawaye suna sakko masa gudun zuciyar sa na sake yin yawa ya kulle idanu sa sai kuma ya bud’e ya sake kullewa yaga fuskar ta dai yake kallo a lokacin da take kuka ranar da suka rabu yace, “Ameenaaa!” Ya fad’i sunan da k’arfi tare da saukewa a hankali ya sake bud’e idanun sa ya rasa abinda yake ji a wannan lokacin shi kansa bai San wanne irin yanayi yake ciki ba. Shin farin ciki yake ko bak’in ciki? Damuwa ce ko kuma tashin hankali ne?.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
Book3
022
Suna zaune a babban falon sabon gidan Rukayya mai kyau suna cin lafiyayar shinkafa da miyar Kaji ga lemo da had'a musu mai sanyi dan 24 hours solar take da ita shiyasa take lemo na siyarwa mai shegen dad'i ga sanyi.
Zakiyya kallon falon take yi tana girgiza kai tana mamaki wai gidan İbrahim ne wannan, ta rame sosai tayi bak’i kamar ba ita Zakiyya ba ya kalli Rukayya tace, "Wato duk Wanda yayi hak’uri a rayuwar sa zai ga alkhairi, mai hak’uri baya tab'a fad'uwa kasa na gani a kanki keda da Ameena. Kalli wannan gidsn yanzu gidan ki ne, da Fiddausi ta zauna da yanzu watakila Keda ita ne a cikin gidan nan.” Rukayya tayi murmushi tace, "nima naga amfanin hak’uri da kuma Karb’ar k’addara Zakiyya, ban tab'a hasashen samun farin ciki kamar wanda nake ciki a yanzu ba, duk inda zai kwatanta kwanciyar hankalin da nake ciki a gidan nan babu wanda zai fahimci hakan."
Ameena tace, "ai ko baki fad'a ba mun gani a zahiri, Gashi nan sai kib’a kike abin ki kin sake yin haske duk da kina da ciki baki bak'i ba saboda hutu kawai kike yi." Rukayya tayi dariya tace, "makaranta nake so na koma a wannan lokacin amma yak'i wai sai na haihu." Zakiyya tace, "ku kam kunji dad’i keda Ameena baku da wata damuwa a yanzu kyau kuke yi kuna k’ina, ni gani ban san a wanne mataki aurena yake ba dan nasan yana dawowa yaga cikin nan saki na zaiyi."
Rukayya tace, "ki daina yiwa kanki fata bazai sake ki ba in sha Allah."
"Hmmm Rukayya ni kad’ai nasan tashin hankalin da nake ciki, gabad’aya bani da kwanciyar hankali a gidan sa kullum cikin fad’uwar gaba nake yi. Yanzu in ya sake ni ina zanje? Ku kun san yadda gidan mu yake karami ne a yanzu bani da wajan zama in akace na koma gida. Nice nake taimaka musu da abinci dana cefane in akace Nima na koma na zauna me gari ya waya kenan?. Tashin hankalin da nake ciki ban san adadin sa ba wallahi.”
Ameena tace, "Taimakon iyayen ki da kike yi Allah bazai barki ki wulak’anta ba. Kuma a yanayin da kike ciki bai kamata ki dinga sakawa zuciyar ki damuwar nan zata cutar da lafiyar ki ba, duk kin rame kamar ba ke ba."
"Rashin kwanciyar hankali shine ya ramar dani, yanzu na gane maganar da kuke cewa kud’i daban kwanciyar hankali daban, gani dai a yanzu a cikin kud’in amma wallahi bani da kwanciyar hankali, Kullum fargaba kar Abbahn fahad ya dawo ya samu cikin nan har ya girma haka."
Rukayya tace, "ki ta addu'a babu abinda zai faru in sha Allah, ki saka Inna ta dinga miki addu’a wallahi in sha Allah babu abinda zai same ki. Har yanzu babu labarin Fidy ko?." Zakiyya tace, "hmmm! Fiddausi ina jin ai d’an yankan kai ta aura ya kai an yanke mata kan, dan indai ba haka ba to watakila ta mutu." Ameena tace, "Haba Zakiyya, meyasa kike cewa haka?."
"To shirun yayi yawa ne Ameena, tun Abban su bai damu ba yanzu shima ya damu ya dame shi sosai ana ta saukar alkur'ani akan Allah ya bayyana ta. Ba’a samun wayar ta an kuma rasa tana ina."
Rukayya tace, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Allah ka bayyana mana wanna baiwa taka cikin aminci. Wallahi Kullum da itanake kwana nake tashi, Kullum sai nayi mata addu'a tun Amir yana tambayata Mama har ma ya daina.” Ameena tace, "Wallahi nima kullum tana raina, addu'a indai zan yiwa kaina zan muku gabadayan ku amma abin yayi yawa shirun nata yayi yawa sosai."
Zakiyya tace, "ba fata nake ba amma wannan shirun na Fiddausi ba alkhairi bane ba, alkhairi bazai b’oye Fiddausi ba sai ma ya sake bayyana ya dan kowa yana tana cikin sa." Ameena ta girgiza kai tace, "wannan haka yake, Allah dai ya bayyana mana ita." Suka amsa da amin suna cigaba da hirar su har suka tafi.
Sai yamma gab da magriba suka tafi bayan tafiyar su Ameena school bus ta kawo Amir tana jin horn ta saka hijjabi ta fita ta bud’e sai da suka ga ya shiga gida sannan suka ja motar suka tafi, wanka ta yi masa tasan suna sallah a makaranta yaci abinci. Suna nan tare da Amir har suka yi i'sha ta koya masa karatu a wajan yayi bacci Ibrahim bai dawo ba.
Waya take masa baya d'auka duk ta damu dan baya kaiwa dare kamar haka, tana tsaye a bakin gate din gidan sai kai kawo take yi hankalin ta ya tashi tana kira baya d’auka gashi kuma bai dawo ba. Horn taji a k'ofar gidan tayi saurin bude k'ofa taga shine tayi Ajiyar zuciya ta zare sakata gate din ta bud'e ya shiga da motar sa mai kyau sabuwa madaidaiciya daidai k’arfin sa ya ajjiye a inda ake ajjiye ta daman parking space din gidan na mota d’aya ne.