← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 93

Sashe 1

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Book 3
001

          Yaya Adam yana zaune a falo shida matar sa Aisha yana cin abinci tana zaune a gefen sa ya kalle ta yace, "Ameena ta fito yau kuwa?." Aisha ta kalli hanyar d'akin da Ameena take ya kalle shi tace, "bata fito ba, abincin ma aika mata dashi nayi." Ya kalle ta yace, "Meyasa baza kice ta fito ba wai? Baki San Zaman dak'in yana k'ara mata damuwa ba?" Ya fad'a zai mik'e tayi saurin rik'e hannun sa tace, "Dan Allah ka zauna."

Ya zauna din kamar yadda tace yana kallon ta yace, "meyasa?."
"Tana buk'atar zama ita kad'ai din wani lokacin, kar ka manta ka sanar dani tana son mijin nan nata sosai, watakila bata kawo rabuwa a yanzu tsakanin su ba dole tana buk'atar keb'e kanta ba ko yaushe zata kasance mai son magana ba. Bata iya yi maka musu shiyasa in kace ta fito take fitowa, ka kyale ta dan Allah kar ya zama an shiga hakkin ta kuma."

Yace, "baki san zama ita kad'ai zai iya k'ara mata ciwo ba? Hawan jini gare ta fa, likita ta tabbatar min da ana bukatar tadinga kasancewa cikin jama'a ana hira da wasa da dariya da ita akan me zan barta ita kad'ai? Fitowa ta cikin mu shine zai saka ta nishadi ko da batayi magana ba hirar mu zata saka ta cikin farin ciki."
"Na sani, amma wani lokacin tana son zama ita kad'ai din ka fahimta, koda ta shigo cikin namu wallahi bata sakewa ka dinga kula da hakan. Kuma Amira na tare da ita suna hira saboda tafi sakawa da Amiran ne ma mahaifiyar ta ta bar mata ita sai ta warware Amiran ta koma, dan Allah ka kyale ta anjima zata fito."

Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abincin sa kafin yace, "mijin nata ma yana neman sake b'ata min rai, hukuncin da na k'iyi masa saboda Iyayen sa shi yake so nayi masa da alama" ya fad'a yana kwafa tare da girgiza kansa. Tayi murmushi tace, "kafa daina zaqewa a lamarin mata da miji, kar kazo kaji kunya nan gaba." D'aure fuska yayi babu alamun wasa ya kalle ta yace, "Kamar ya zanji kunya? Kina nufin zata koma masa ne?, kinga Asiha  bana son b'acin rai kar ki sake fad'amin wannan maganar koda wasa. Wanne irin na daina zaqewa me kike nufi?."

Mik'ewa tsaye tayi ganin ransa ya b'aci  tace, "Allah ya Baka hakuri." Zata wuce kenan aka sallama aka shigo falon duk suka kalli masu shigowa tare da amsa sallamar suka k'araso ciki suna tsuguna suka gaishe da Yaya Adam, yayi murmushi yace, "Zakiyya da Rukayya, Barkan ku da zuwa." Murmushi duka sukayi cikin mamaki Zakiyya tace, "Yaya ban d'auka zaka gane mu ba ai wallahi." Shima murmushi yayi yace, "ashe bazan gane Ameena ba kenen." Rukayya tace, "Gaskiya ne." Murmushi kawai baice komai ba suka gaishe da matar da ta amsa fuska sake yace, "Aminai kenan a wajan Ameena, ki nuna musu d'akin da take."

"Kaga ai ga masu saka ta nishadi sun zo sai hankalin ka ya kwanta" ta fad'a tana yin gaba tana dariya suka bi bayan ta har inda Ameena take. Ta zaune akan katifa ita kadai ta jingina da bango tana kallon bangon yake gaban ta tayi shiru kamar mai d'aukar darasi. Aisha tace, "Ameena kina aikin tunanin ne? Ina Amira da Zaitun suke?."

Sai a sannan ta kalli wajan da taji maganar ganin su Ruky sai tayi murmushi tace, "Aunty sun dame ni da hayaniya ne shine nace su fita, saukar yaushe? Ta fad'a tana kallon su Zakiyya. Aunty Aisha ta kalle su tace, "kuyi mata fad'a dan Allah ku sanar da ita k'addara tana kan kowa, rabuwar aure  kaddara ce tun kafin auren ta Allah ya rubuta haka, ta karb'i kaddarar ta saki jikin ta shi yana can tare da matar sa har yanzu bai zo gidan nan ba koda sunan ganin y'ar sa balle ita, ita kuma tana nan zaune kullum a d'aki tana kuka tana tunani, ku sake nusar da ita ko zata fahimta kune k'awayen ta zata fi amincewa da maganar ku"ta fad'a tana fita ta basu waje.

Zakiyya ta zauna a gefen ta na dama Rukayya ta zauna a haggu suka saka ta a tsakiya duk suka dafa ta Zakiyya tace, "Ameena abinda Auntyn ki ta fad'a gaskiya ne, ki duba yadda kika sake komawa fa dan Allah , wallahi Yaya Adam bazai ji dadi ba kina gidan sa ace kina wannan ramar ba." Rukayya tace, "gata yayi miki dan in ba shi ba babu wanda  zai karb'o ki daga wajan Yusuf."

Ameena ta sauke numfashi tace, "kawai ina tunani ne daman nima zan kasance a cikin layin mata zawarawa?." Rukayya tace, "kaddarar ki kenan ai kuma dole sai ta same ki, shi kuma tunda ya samu wata ya wulakanta ki." Ameena tayi murmushi tace, "Wai a ina kika samu labarin ina nan? Nidai nasan bamu yi maganar ba."

"Daman ai baza ki fad'a mana ba, kiran ki nayi Amira ta d'auka nace mata zan zo gidan sai take fad'a min ai kina nan ga abinda ya faru" Rukayya ta fad'a tana kallon ta. Ameena ta sauke numfashi tace, "Abun kamar a mafarki nake kallon sa".
"Ai nan taba ganin namiji kamar Yusuf din ki ba Ameena, Tunda Rukayya fa fad'a min na dawo daga rakiyar maza, Tunda ya iya yi miki kishiya yazo kuma yana wulak'anta ki a akanta har abin ya kai ga kin dawo gida naji duk duniya babu wanda na tsana kamar Yusuf, wallahi sai Allah ya saka miki dan bai miki halacci."

Ameena bata ce komai ba Zakiyya ta sake cewa, "ki saki jikin ki Hajiya kina gida ne kema ki kawar da komai a ranki yana can tare d a matar sa ke kina nan da damuwa a zuciyar ku ciwo ya same ki ki shiga uku, dan shi bai san kina yi ba ki mik'awa Allah lamarin ki kawai ki fara sabuwar rayuwa kamar ko wacce mace. Wannan damuwar ba abinda zata k'ara miki sai ciwo da wata damuwar, dan Allah ki cire batun Yusuf a zuciyar ki."

Ameena tace, "babu Yusuf a tare dani yanzu Zakiyya, ni burina yanzu ma yazo yace ya sake ni din dan bana mafarkin komawa gidan sa, ni kad'ai nasan me a cikin gidan. Kawai abu kad'an ne yake saka ni damuwa bayan shi babu komai." Rukayya tace, "to shima ya daina saka ki damuwar, damuwa dai ciwo ce a tare dake, yanzu kika samu ciwo kan ki kika cuta ba shi ba." Tayi murmushi tace, "mu bar maganar nan ta wuce in sha Allah na manta da Yusuf kenan, wai ina labarin Fidyn New York?."

Zakiyya tayi dariya tace, "Tana can ana chilling ana buga uwar soyayya." Ameena tayi murmushi tace, "Hajiya Fidy buri ya cika, ga mai kud'i gata kuma a America k'asar da tafi so." Rukayya tace, "buri ya gama cika ai a wajan ta." Ameena ta kalli Rukyy tace, "Ya batun Umar din? Komai yayi daidai?."

Rukayya ta sauke numfashi tace, "yana nan magana tana neman yin k'arfi ma, zancen aure ya shigo tsakani sosai." Zakiyya tace, "Alhamdulillah, amma ya naga bakya farin ciki? Akwai wani abun ne?." Rukayya ta d'aga kai tace, "Akwai." Ameena ta tashi zaune sosai tace, "meye?."

Rukayya ta kalle su tace, "Kun san wanda ya samu Baba da batun aurena kuwa?." Suka kalli juna suka girgiza kai alamun basu sani ba Rukayya tace, "Ibrahim tsohon mijin Fiddausi mahaifin Amir dan ta." A tare suka zaro idanu waje Ameena tace, "Wai tsohon mijin Fiddausi tamu?." Rukayya ta d'aga kai sama tace, "shi fa, yanzu haka maganar da nake muku Baba ya bashi damar yazo mu gaisa. Ban San me zance ba wallahi gabad'aya ji nake kamar na aikata wani kuskure babba. Bana so yazo ma balle ace mun zauna nida shi a matsayin wai wanda yake neman aurena, wani iri nake ji a jikina wallahi sam babu dad'i."

Zakiyya ta girgiza kai tace, "ikon Allah! Ibrahim yazo wajan Baba yana neman auren ki? Bayan Fiddausi ta rabu dashi." Rukayya tace, "ni wallahi zancen ma fad'uwar gaba yake saka min." Zakiyya tace, "Kin san wani abu Rukayya?." Rukayya ta girgiza kai alamun A'a tace, "Sai nake ji a jikina kamar fa daman haka Allah ya shirya shiyasa ya jinkirta miki yin auren har sai da Ibrahim ya rabu da Fiddausi." Rukayya tace, "Kina nufin wai shine mijina? Haba Zakiyya tsohon mijin Fidy ne fa, ai ba easy ace na auri tsohon mijin k'awata Fiddausi, wacce nasan sirrin gidan ta kaf, Haba ai babu dadi."

Ameena tace, "shi abinda Allah ya tsara babu wanda zai canj shi duk abinda mutane zasu ce kuwa a kai, in haka Allah ya k'addara akwai abinda zakiyi ne?. In daman shi Allah ya rubuta shine mijin ki ya zaki yi?."
"Amma dai akwai cin amana a lamarin nan, sai Fidy taga kamar ma tun baya son mijin nata nake yi wallahi. Ni in yazo zan fad'a masa yayi hak'uri kar ya sake zuwa inda nake da sunan yana sona ni bazan aure  shi ba. In na aure shi mutanen unguwa ma ai sai su tsine min, ga Baba yayi na'am dashi sosai, a yadda Umma ta fad'a min sai da yaje gidan su Fiddausi suka gana da Abban su akan batun Ibrahim din tunda  ya dawo yake ce mata shi ya amince da İbrahim. Wallahi gabana fad'uwa yake bana so ace hakan ta kasance."

Zakiyya tace, "in hakan ta kasance din ai me Rukayya? In ma lokacin da Fiddausi take auren sane dan ya aure ki wani abun ne balle bata tare dashi tayi masa nisa a yanzu tunda  tana da aure. Saboda talaka ne Fiddausi taga bazata iya zama dashi ba, kin san komai ai akan abinda ya raba su; ke kuma kina ganin zaki iya zama dashi to meye a ciki?. Ita arzuk'in sa bai mata ba ke kuma yayi miki meye to?."
Chapter 1 · 0% Book details