← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 114

Sashe 97

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Satin mu daya muka yi shirin dawowa gida, da yake Ina son wasu kaya nace a kaini wani shooping mall d'in zanyi siyayya uncle Haysam ya bani driver muka tafi da yaransa kannan amarya su uku sai Hameedah da tace itama zata yi siyayya. Muna zuwa na zabi abubuwan da nake so itama ta dauka suma suka nuna abubuwan da suke so na siya musu akai mana bill na bayar.

Muna fitowa Ina Kokarin saka wayata a cikin jaka na hango wata mata, sosai tayi min kama da malama Mardiyya ta Durbun. Na sake ware ido dan kamar ta baci duk da cewar wannan ta kuma zama babbar mace amman kamannin suna nan. Kasa wucewa nayi sai da na karasa wajan da suke na gaida su, suna ta bina da kallon rashin sani, nayi murmushi tare da cewa.

“Dan Allah kuyi hakuri tambaya zanyi.”

“Toh Allah yasa mun sani yan mata.”

Cewar wace nake da tabbacin itace malamar tawa.

“Wallahi gani nayi kina min kama da wata malamar mu mai suna Malama Mardiyya, ta koyar damu a makarantar Durbun nursery, primary and secondary school.”

Baki bude tana kallona, sai naji jikina ya yi sanyi tare da shaida min bafa ita bace, ina kokarin bata hakuri ashe ita kuma mamaki ne ya kusan kashe ta dan tasan bata koyarwa irin wadannan wayayyun ba a Durbun, muryar ta radau tace dani.

“Kwarai kuwa nice malama Mardiyya ta makarantar Durbun, amman ban gane ki ba gaskiya.”

Ai ban kuma jiran cewar ta ba na rungume ta a jikina cike da murna harda hawaye na, wadanda suke tare da ita suka fara min magana cewar na sake ta na fara yi mata bayani, ga motar mu Hameedah Sai horn take yi min saboda lokacin tafiyar mu airport ya kusa.

“Malama ni ce fa Khadija Basheer.”

Rufe baki tayi, Hawaye suka fara wanke fuskar ta, Gaba d'aya sai farin ciki kuma ya lullube ta..

“Khadija, Dije, Dijen gala yar Baffa ta Gajiyalle mai yar hakiya. Idan ma baki gane ba mune farkon students a Durbun budurwar malam Auwal mai dan gemu.”

Zabura tayi ta mike kasan cewar da tana zaune ne akan kujera, kallona take tana mamaki ganin yadda na canza gabaki daya na, jin horn din ya yi yawa yasa nace cikin sauri.

“Malama akwai labari sosai amman sai mun hudu. Nayi aure idan kunzo kano a masarauta nake, ki tambayi sashen Gimbiya Khadija zamu hadu.”

Ina kaiwa nan na juya da sauri dan karma muje gida Hameedah tayi min sharrin cewa nice na tsaida mu Mami tayi min masifa. Na shiga Mota Ina kallan ta tare da daga mata hannu itama tana daga min, wani irin dadi yana ratsani, gani nake yi kamar naga uwar da ta kawo ni duniya saboda malama tayi min halacci sosai.

*GIM. KHADIJAA*

Mayafi na cire, Dawowar mu kenan inason nayi bacci call din Salman ya sake shigowa wayata, Na wajen ashirin kenan a iya sakkowar mu daga jirgi zuwa yanzu,

“Ranka ya dade...”

“Na gaya miki babu kwanan da zaki sake yi Zawjatii, Ki tattaro kayan ki ki dawo gida yau.”

“Amma yallabai dare ne fa, Ya za’ai nace zan taho yanzu? Fisabilillahi ka bari zuwa da safe mana...”

“Yanzun ne dare yayi? Yanzu fa muka idar da sallar isha’i, Nide na gaya miki ki dawo gida.”

“Ba fa na jindadi... Na kwaso malaria ne maybe saboda weakness din jiki na.”

“Ki dai zo gida yanzu, Akwai doctors.. Zawjatii..! Kinji zucia ta kuwa? Bazan iya kwana batare da naji dumin jikin ki ba, Zucia tah da gangar jiki na sunyi kewar ki... I love and miss you soo much.”

Ajiyar zucia na sauke, Bacci ne dankare a idanu na, Na lumshe idanu kawai ina sosa kunne na da dan karamun yatsa na,

“Shikenan...”

“Na aiko a dauke ki...?”

“No za’a kawo ni..”

“Allah ya kawomin ke Lapia ya tsare mun ke.”

Ahankali nace ‘Aamin..’ Na maida mayafin dana cire jiki na, Jiki ba kwari na sakko kasa ina d’auke da trolley na,

“Ahh.. Ba dai tafiya ba..?”

“Eh wallahi Mami.. Zan tafi, Wai Ammi ce ke tambaya na.”

Na amsa ahankali rashin karyar da zanyi, Mami ta gyada kai tana murmushi,

“Ummale!!! Jeki kira driver ya sauketa a gida.”

Jira nai har Kawu Daddy ya dawo daga masallaci sannan na masa sallama, Da Ya shukrah naci karo a kofar karamin parlor zata shiga, Hannun ta ri’ke da tray dauke da lemo, Ruwa da kuma snacks.

“Ya shukky.. Zan tafi.”

Kallo na tayi jikin ta yai sanyi, Lokaci d’aya naga ta burkice, Ko bataso na ce mata Ya Shukky dinbane?

“Meya faru..?”

“Ahh babu komai.. Na dauka kwana zaki sake yi ai.”

“Eh! Da sai da sss...”

Ban karasa ba sakamakon hango Masoud da nayi, Yana tafe yana gyara hular kansa. Kicib’is yai yana kallo na, Nima na shiga kallon sa, Kallon mamaki, Meya kawo shi gidan Kawu daddy? Kuma da alama wajen Ya shukrah yazo. Da sauri na saisaita kai na ina a’uziyya da sharrin shaidan daya sa ni tsayawa,

“Hajiya Khadijaa.. Ranki ya dade rai kanga rai?”

Kasa k’oda motsi nayi, Jin muryar masoud da nayi cikin kunnuwana, Wanda ko suma nayi na farfad’o zan gane ta,

“Sannu! Ina yini.?”

“Lapia qalau... Ya mai gidan naki.”

Kasa amsa nayi na koma ciki kawai, Kawu daddy na parlor da Mami da Ya hameeda suka ga na dawo ban tafi ba,

“Ah dije kin fasa sai da safe ko...”

Mami ce ta tambaye ni tana bina da kallo, Ni kuwa gaba d’aya zucia ta naga su Ya shukrah da tsohon saurayi na Masoud, Wanda na d’au son duniya na dora masa, Shin wannan cin amana ne ko ci baya? Na tambayi kai na ina nisawa.

“Khadija... Menene?”

Kawu daddy ya tambaye ni cikin kulawa, Na sauke ajiyar zucia hade da girgiza kai,

“Babu komai Kawu daddy.. Ya shukra ce take zance shine na basu waje.”

“Kice tana zance da tsohon saurayin ki dai.. Masoud, Itama shukrah bataji wallahi.”

Mikewa Kawu daddy yayi yana bin ya hameeda datai magana da kallon karin bayani,

“Saurayin Khadija na baya?”

“Eh daddy..”

Ficewa yai wajen Shukrah , Bansan ya akai ba najiyo muryar sa yana wa shukra fada, Can ta shigo kanta a kasa tana kuka. Dawowa yai yana huci,

“Haba wannan wane irin rashin kan gado ne eh? Ko kunya bakya ji? Tsohon saurayin kanwar ki? Kinsan shi sarai ya san ki shine zaku dawo yanzu gotai gotai dake kina kula shi..?”

“Daddy ya girme ni fa...”
Shukra tace cikin kuka.

Kanta yai tamkar zai doketa ta fadi, Ya shiga karkada mata hannu,

“Na hada ki da girman na gwara kan ki. Ni zaki kawowa maganar Shirme? Duk kin kore samarin ki, Dama shine yake hure miki kunne?”

Kuka shaheedah ta fashe dashi tana shessheka, Kawu daddy yaja tsaki,

“Hajia ya akai ake wannan katobarar a gidan nan ba’a sanar dani ba? Ina Shukrah ina tsohon saurayin Khadija?”

“Kayi hak’uri daddyn su. Nima nayi nayi taki yadda, Ni nafi mata sha’awar Sulaiman ma dan gidan Amb Haroun.”

Tsaki yaja yana bubbuga kafafun sa, cikin fada yace,

“To ku saurare ni daga ke har su Hajia, Daga yau idan na sake ganin kafar yaroncan a go....”

“Daddy be dade da accepting feelings dina ba.. Da ya..”

Wani mari ya sauke shukrah dashi seda naji tamkar a fuska ta aka falla shi.

“Idan na sake ganin kun cigaba da mu’amala dashi ban yafe muku ba gaba d’aya. Sannan ku saurare ni dakyau kuji, Ba zamu cigaba da zama rida rida daku ba kai d’aya agidn nan ba zeyiwu ba, Kuna samu kuna korar su akan me? Wallahi ba Za’a sake ba, Abu na biyu mungama magana da su yan uwana, Ke Hameeda kece babba zamu hada ki aure da Na’eem dan Yaya kabiru dake jos. Ke kuma shukrah Abdul (yaron sa) dai na waje na, Da shi Zan hada ku, Domin na yaba da hankalin sa da nutsuwar sa, Tun ba yau ba nake kwadayin ya sake kusanci dani ta hanyar bashi auren jini na, Da Khadija kafin anemi aurenta shi nayi niyyar hadasu saboda hankalin ta. Na gaya masa tun tuni kuma ya amince yana son ki, Ke shukrah ba magana nake miki ba?”

Kuka wiwi shukra take, Ita kuwa Hameeda batace komai ba, Domin dama Ya Na’eem yana burgeta, Shukrah kuwa burgima tashiga yi tana yakushin kanta,

“Daddy Abdul fa kace?Dan girman Allah kayi hak’uri ka sauya mun wani.”

“Alhaji ka duba zancen shukrah, Haka dinne, Ni dama aciki....”

“Yimin shiru, Ai duk kusan hankalin ku d’aya keda su, Duk Ke kike sasu agaba kina hure musu kunne...”

Wayar Kawu daddy ce tai kara ya dauka ya fice yana amsawa cike da girmamawa, Sai a sannan hankali na ya dawo jiki na,

“Kinji dadi kin shiga tsakanin soyayya..”

Cewar ya shukrah tana harara ta. Daria ma taso bani wallahi, Ni da ita kowa ya shiga tsakanin soyayya oho, Na sauke ajiyar zucia kawai. Agogo na kalla tara saura kwata. Da sauri na dakko wayata a jaka, 30 missed calls Salman yayimun. Kiran sa nayi najita busy da alama waya yake yi. Sai ga Kawu daddy ya shigo yana murmushi,

“Kawu zan tafi...”

“Ah ai gashi nanma ya taho nan din.. Yace dama yana da niyyar zuwa mu gaisa.”

“Wa...?”

“Mai gidan naki...”

“Sarki Salman?”
Cewar Mami ta tambaya cikin tsantsar mamaki.

“Eh wallahi, Yace ya kikkira wayarta bata dauka, Hankalin sa ya kasa kwanciya shine ya taho da kansa.”

Kunya duk ta kamani, Nasan Salman zai aikata fiye da haka. Zama nai a hannun kujera ina wasa da yatsun hannu na.....

<>
_Afuwan zafafa fans.. Ba zaku samu kibiyar ajali ba na yan wasu kwanaki. Saboda wani uzuri daya taso🤲🏻Dana kammala zan cigaba da posting IN SHAA ALLAH!_

_Yar uwa kinason karanta zafafa amma documents? To zafafa na harhada kayan su. Da an kammala Za’a yi documents dinsu duka akan Naira dubu d’aya da........_

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.
Chapter 97 · 0% Book details