← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 114

Sashe 60

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake kada mata kai nayi, Domin labbana sunyi nauyin furta kalamai. Ficewa tayi bayan ta ciro min wani gogaggen hijabinta a drawer, Na dan jima a Zaune ina sakawa da warwara kafin na mike na nufi babban parlorn Gwaggo ta fada wanda ya kasance na masaukin baki. Baki na dauke da sallama na shiga ciki, Suna zaune su uku. Gwaggo, Addah, Sai wani dattijo gemun sa ya zama furfura gaba d’aya. Ya rufe kansa da hirami. Gaishe su nayi baki d’aya, Gwaggo ta nuna min kusa da ita na zauna.

“Itace wannan Hajia.?”

Ya tambaya yana mai kallon Gwaggo ta fada. Gwaggo ta jinjina kai. Ya sauke numfashi yana girgiza kai. Na kalli Gwaggo kallon karin bayani. Gwaggo tace,

“Khadija wannan da kike gani babban malami ne na sunnah, Yanada makarantu na tsangaya dama Islamiyya. Kuma ya kasance kamar dan uwa ne agare mu. Domin duk abunda ya sha mana kai ma’ana ya zarce karfin sanin mu.. Toh awajen sa muke neman karin haske. Sunan sa Malam Mujaheed Na Soro, Na gaya masa matsalar da kike ciki tunda dama yasan Salmanu ya kara aure, Tofin nan da kika yiyyi amfani dashi dana wajen Salmanu duk almajiran sa yasa suka yiyyi, To dana gaya masa ba wani canji dai shine yace zai kara bincike akai duk yadda ake ciki zai zo da kansa...”

“Toh Gwaggo.. Allah yasa adace.”

“Aamin Yaa Rabbi... Malam! Bismillah!”Cewar Gwaggo Ta Fada.

Gyaran murya Malam yayi, Ya sosa gefen kunnen sa kafin ya fara cewa,

“Wato azahirin gaskia Hajia wannan babban makaru aka yi musu jifa daga ita har shi sarkin.”

“SubhanAllah..!” Addah Maryama tafad’a tana mai girgiza kai cike da tausayawa.

“Ai Malama Maryama akwai mutane marasa imani a duniya, Wanda digon tausayi wallahi basu dashi a zukatan su. Ahar kullum su dakushe farin cikin mutum yai ta zama a lalace shi suke so. Da zakuga yadda zukatan su suke bakikkirin idan farin ciki yasamu wanda suka tsana zakuyi dimbin mamakin yadda suke shiga mawuyacin hali, Sai sun bi ta kowacce hanya sun kauce sunyi shirka sannan suke jin dadi. Wallahi duk yadda zasuyi sai sunyi wajen ganin sun dakushe mutum, Kai Allah ya mana katangar k’arfe da makiyan mu..”

“Aamin Aamin!” Muka hada baki wajen amsa addu'ar malam...

...
Masu tambayan if yerwas truly a scented product.?...Well yess😅 Yerwa incense and more as the name implies dagaske kamfanin turare ne na turaren wutan kanem empire (bornu) Turaren Kaya, gidah, khumrah’s, kulaccams, turaren ruwa na larabawa dana fesawa, English perfumes, kabbasas, burners, steaming chairs, Kai komai da komai dai na turare Muna dashi.. You can check us on ig @yerwaincense_and_more, Muna tura kayanmu ko’ina a fadin najeriya kai harda nahiyar ketare ta dhl👏🏻Muna bada kayanmu akan farashin sari da saya dai-dai... so please do follow our Instagram page above👏🏻

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
P
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*BOOK 2*
*PG:2 *

________

“Sihiri gaskia ne, Kuma kowa zai iya kama shi dik kuwa da yadda kake tsarkake jikin ka, Sai dai kamuwar na wani yafi na wani, Saboda karfin tashi tsaye da kariya. Ranki ya dade ina fatan kina saurara?... ”

Ya karasa fada yana duba na, Na daga kai ina mai cigaba da jinjina kalaman sa na baya akan ma’kiyi.

“Nayi bincike sosai akan zancen ki da Hajia ta sanar min, Har na sassa yara suka yiyyi addua aka yi miki tofi kuma.. Har yanzu jinin na fita kamar da ko kuwa ya ragu?”

“A’ah! Ya ragu ba kamar da ba.. Nagode Malam!”

“Toh gaskia babban sihiri ne wannan, Kwanaki can baya an kawo min ire iren matsalolin nan. Kuma duk yawanci dai abokiyar zama ce silar ko kuwa wani makiyi na daban.. Shi sihiri gaskia ne domin ya kama annabin Allah ma ballantana mu karan kada miya. Wannan jini da aka sakar miki duk d’aya ne daga sharrin sihiri. Ki cigaba da ibadar ki, Anyi hakane domin wata manufa don kada auratayya ta shiga tsakanin ki da mai martaba. Kuma ta Allah bata suba,

“Sannan duk wannan warin da kikace kina ji na kamar shekararren mushe duk makuru ne wallahi, An miki jifanne don ke kan ki ki kyamaci kan ki, Sannan wani kara da gane gane da kike yi duk razana ce don ki fita ki bar masarautar ne. Sannan an dasa miki tsoro da fargabar cikin ta. Wannan duk sharrace sharracen sihiri ne, Ana kara nisan ta tsakanin ku da juna, Ma’ana ke da mai martaba, Sannan duk wutar kinsa dake sake ruruwa a zuciyar ki duk Sharrin shaidanu ne da akai amfani dasu, Amman In shaa Allahu nan ba da jimawa ba komai zai dai-dai ta da yardar Allah...”

Shiru nayi kawai ina maimata maganganun sa a zuciya tah, Allah na tuba Salman ai ba son hakika yake min ba. Ya aure ni ne dan ya muzguna min. Kawai saboda nayi kokarin ganin ya amsa tambaya a saukar qur’ani da akai. Na sauke nannauyar ajiyar zuciyar da sai da dukkanin su suka dago suka kalle ni,

“Gimbiyah ya dai...?” Cewar Addah Maryama da kulawa.

Na girgiza kai kawai alamun ba komai, Hade da ka’karo murmushin yak’e. Malam ya cigaba da cewa,

“Toh abubuwan sammu dai da yawa akai miki gaskia, Wanda duk wani bakon lamari da jikin ki ko zuciyar ki zata kissima miki duk sharrin shaidanu ne la’anannu, Domin da su ake hada kai acuci bil adama. Allah ya saka muku da gaggawa kuma ya yaye muku dukkanin matsalolin da aka jefa rayuwar ku aciki... Sai kin kara jajircewa da addu’oi sosai, Da yawan salloli, Lazimi da karatun qur’ani, Babu dare, babu rana. Da yawan sadaqah In Shaa Allahu rayuwar ki da tasa zata daidaita da duk wani masoyan ku da ake dakushewa. Muma a namu b’angaren zan sa yara suyita sauke qur’ani, Zan tayaku da adduoi nima, Sannan ga ruwan tofi nan na kawo da akai da zam-zam, Gasu Zaitun nan, Da habbatussaudah da ganyen magarya nan ma, Zan baki ayoyin da zaki karanta.. Kina ji?”

“Inaji Malam.. Nagode!”

“Yauwa shi wannan magani da ake da ganyen magarya ba sai an maka sihiri ba ko an jefe ka, A’ah kowa zai iya yi don tsima jikin sa daga sharrin masharranta, A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai kingan su nan (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan. Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan. Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara). Sai a karanta Suratul A'araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122. Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82. Suratul Kafirun kafa daya Falaki da Nasi kafa uku- uku. Sai a karanta wannan addu'a,

"Allahumma rabban-nas az'hibil ba'as ashfi wa antash-shafi la shifa'a illa shifa'uk shifa'un la yugadiru sakaman" kafa uku. Sannan za'a iya karawa da wannan addu'a "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika" kafa uku. Insha Allahu ta'ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi. Wala nan kusa wala nan da wani dan lokaci. Allah ya shiga lamuran ku gimbiya, Allah ya kara tsare ku da tsarewar sa, Ya kare ku da kariyar sa. Allah ya kara muku ni’ima daga cikin ni’imomin sa, Allah ya karba mana Allahumma Aamin.. Ga kuma wasu addu’oin na rubuta miki, Ki dingayi kullum, Sannan azkhar ma na safiya da maraice dana kwanciya bacci dan Allah ki rike su karkiyi wasa dasu.”

“Sannu Malam, Allah ya amsa. Mungode Allah ya saka da alkhairin sa.” Gwaggo Ta fada ta amsa masa fuskar sa dauke da fara’a. Da alama taji dad’in addu’oin da ya babbani.

“Babu komai Hajia, Yiwa kai ne, Fatan Mu dai addu’oin mu su karbu Allah ya yaye musu..”

“Malam Nagode, Allah ya saka da alkhairi..” Nai masa godia ina karanta addu’oin dake cikin paper daya rubuto min.

Sallama ya mana, Ya mike ya tafi bayan Gwaggo tai masa goma ta arziki, Ya tafi yana mai godia sosai.

Bayan tafiyar Malam muka yi sallah muka sake sabon zama, Gwaggo Ta Fada ta shiga kara kwantar min da hankali, Tana mai sake bani wasu labarun game da masarautar basannabas. Ta kar’kare da,

“Rayuwar sarki Salman abar tausayi ce gaba da baya, Kada ki manta gaba d’aya an juya masa hankali akan mahaifiyar sa, Yana abubuwa tamkar bashi da uwa, Tana raye gida d’aya dashi amman an riga da ancireta cikin zuciar sa, Yan uwan sa da suke uwa d’aya uba d’aya ma an cire su a zuciar sa, Gaba d’aya an cire sanayya, So da shakuwar yan uwan sa na jini da mahaifiyar sa a zuciar sa. Bayaga haka.. Shin ko Kinsan yan uwan nasa da suke uwa d’aya uba d’aya?”

Na girgiza kai, Alamun bansani ba. Gwaggo Ta Fada ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa,
Chapter 60 · 0% Book details