Sashe 59
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuwa Salman sam bai masan inda kansa yake ba. Taita maganganu ita kadai tamkar zaucacciya. Can tabi robobin ruwan tofin da aka shanye da kallo. Tamkar sabuwar tabi haka ta mike jiki na bari ta kunce mad’aurin zanin jikin ta ta ciro wani kullin magani. Ta zuba a roba ta karkada shi sannan ta durawa Salman a baki. Yana kwance ba Uhm bare uhm uhm, Sai kakkarwar ciwo da yake faman yi. Tana gamawa ta sulale ta koma sashen ta hankalin ta a matukar tashe ganin yadda ta samu Khadijaa bayan duk ta aiwatar da abubuwan da malam yace tayi zasu rabu da Salman.
*GIMBIYA SHAHEEDAH*
Zagaye ta shiga yi a dakin ta, kafofinta kunnen ta rike suke da na’urar Bluetooth ta amsa waya. Maganata ake haukace tana daga hannaye. Don dama idan tana cikin tsananin tashin hankali to hakan ne yake faruwa da ita. Tayi ta yin abubuwa tamkar na marasa hankali,
“Hajjaju... Ni de ki kara tambayar sa. Domin Salman fa bashi da lapia sosai. Kuma tinda na binne layar nanne aka sanar min bai san inda kansa yake ba. Anya kuwa malamin nan da kika rakita yasan abunda yake yi?Gaskia bazan lamunta ba Hajjaju. Ko dai bai san kan aikin bane? Ina gaya miki Salman is out of his senses. Ya zama kamar soko.. Ko Kinsan da tsinanniyar nan na ganshi.. Hajjaju ki kara ‘kaimi dan Allah, Zata wargaza min sirri matar nan.”
Tana magana cikin tsananin fushi,
Hannun ta d’aya tana dukan bango dashi. Mahaifiyar tata sai neman kwantar mata da hankali take amma sam tak’i yadda,
“Kawai ki je ki same shi, Idan ba zai iya bane mu nemi wani malamin, Domin wannan yana neman ‘ballo mana da ruwa.. Okay! Seda safe.”
Kit ta katse wayar ta koma ta zauna tana cizan leben ta na ‘kasa, Magana take ita kadai tamkar da wani a kusa da ita,
“Ya zaai ace ni da miji na amma sede ni na nemi shi ba dai shi ya neme ni ba? Ya za’ai ace mu’amalar aure kullum sai baya cikin hayyacin sa yake tunkarata? Dole na nemi mafita.. Tun kafin komai ya bayyana.”
Tayi mita tayi tsaki haka ta kusan raba dare tana abu d’aya...
*SAS*
Kunsan yadda zance yake yaduwa a masarauta.. Kan kace kanzil! Magana ta yanyana har cikin gari da wajen sa.. Cewar Sarki bai da lapia baya fita ko’ina, Zaman fada ma yanzu waziri ne yake zama. Atakaice dai sarautar ta dawo tamkar babu sarki. Babu irin ciwon da mutane basu kwakwulo sun jajiba shi akan sarki Salman ba. Kowa tofa albarkace bakin sa yake.
Sarki Salman na kishingid’e akan wani lallausan carpet dinsa dake malale a makeken parlorn sa. Tufa ce agaban sa. B’angaren sa na dama kuma waziri ne kansa a kasa. Sarki Salman kallo d’aya zakai masa kasan tabbas bayajin dadi. Gaba d’aya ya zabge sai dai ya kara haske. Manyan idanun sa sun sake manyanta tubarkAllah! Kwarjini ya kara lullube shi, Idanun sa saqale da gilashi. iPad ce a gaban sa yana nunawa waziri wasu abubuwa.. Waziri ya kara k’asa da kansa alamun girmamawa da tausasa harshe yace,
“Ran sarki ya dade yayi karko. Ko dai zaka kokarta ka leka fadar ne?”
Sarki Salman yai hanzarin girgiza kansa yana jan leben sa ta kasa.
“Ba zan iya ba waziri, Jiri ne ke kwasa ta idan har na mike. Na kuma gaya maka har yanzu kirjina nauyi yake min, Tamkar an dora duwarwatsu...”
“Assha! Sannu ranka ya dade! Allah ya kara maka lapia.. Da yardar Allah zan kara karb’o maka turaren miyagunnan. Idan kayi kana jin dadi ko?”
Daga kai kawai Sarki Salman yayi ya maida kansa kan wani pillow ya kwanta. Bai kara cira kai ya dubi waziri, Kambun mulkin nasa sun motsa. Haka waziri ya karaci zaman sa ya mike yai masa sallama ya tafi. Ya bar sarki salman kwance yana tunanin da shi kansa bai san na menene ba.
<<<<>>>>>> <<<<<>>>>>>
Kwance yake akan wani katafaran gado, a kalla zai iya daukar mutum bakwai ba tare da sun matse juna ba wajan bacci. Amman shi kadai ne a kai ya yi ruf da ciki kafafuwansa a wale yana ta sakin munshari. Idan ka karewa bedroom d'in kallo zaka tabbatar da cewa jiya ya sha bidirinsa, saboda kayan da ya cire duk gasu nan a kasa ya yi wurgi da su. Dogon wandon yana gefe, T.shirt din ma na wani gurin daman, p.cap din sa ma haka.
A tsakiyar center carpet kuwa, kwalaban barasa ne da ya sha kusan guda hudu. Akan bedside d'in sa ma wasu guda biyu ne an shanye daya an rage wata a cikin kwalbar. Idan ka kare masa kallo tsab kuwa a yadda yake ta shakar bacci, ba zaka taba zato ko tsammanin yana da wata tawaya a cikin rayuwarsa ba, saboda wani irin sihirtaccen kyau da Allah buwayi gagara misali ya yi masa. Wani kyakkyawan abin hannu ne a tsintsiyar hannunsa, tsakiyar an rubuta A.A.S. Wato Abdullah Aliyu Salman.
Cikin tsakanin firgicewa ya tashi yana waige waige tamkar me neman wani abun. Idanunsa ya kai kan agogon dake ajiye akan bedside ya duba lokaci, take ya kuma zabura ya mike yana furta.
“Subahanallah....”
Bathroom ya shiga nan da nan ya sakarwa jikinshi shower, ko cikakken minute biyu beyi ba sai gashi ya fito daure da towel. Da sauri ya bude drower ya ciro suit dark blue, ko mai be tsaya shafawa ba haka ya zura kayan tare da karasawa wajan madubi ya kalli fuskarsa. Duk da cewar be yi wani abu ba, amman ya yi matukar kyau, idan Allah ya baka cikar zati tofa ka godewa Allah koya a wane yanayi kake, kai d'in mai kyau ne. Cikin sauri ya fesa turaruka kusan kala biyar sannan ya dauki jakarsa ya fito yana ta faman buge mutane.
Yau ya yi alkawarin zuwa gidan su shi yasa ko tsayawa yin wasu kakale-kakale beyi ba, kasan cewar ya kusa makara ko da wane lokaci jirgin da zai bi zai iya tashi a lokacin. Yana zuwa kuwa ya tarar passengers duk sun shiga har ana shirin rufe kofa, aka jira shima ya shiga, nan da nan kuwa suka tashi sai jahar shi ta gado, wacce ba zai iya tuna rabon shi da zuwa cikin ta ba. A Abuja suka sauka, amman a ranar ya taho Kano duk da cewa akwai guraran da zai kwana amman sam hankalinsa yana kano yafi son yaje can kai tsaye.
*SASHEN MAI BABBAN DAKI*
(GIMBIYA SA’ADATUH)
Carbi ne a hannunta, Lazumi take yi ganin yadda labbanta ke motsawa ahankali. Hawaye d’aya na bin d’aya a kyakkyawar fuskar ta. Taja ajiyar zuciya ta sauke tana mai goge hawayen da kasan jilbab din jikin ta. Cikin haka Yareemah Abdullahi autan ta ya shigo yana harhada hanya,
“Ammi.......!”
“Na’am Abdul..”
Kasancewar sunata mahaifin yaci. Hakan yasa bata iya karasa furta sunan nasa duka. Da sauri ta karasa goge hawayen fuskar tata gudun karya gani.
Girgiza kansa yayi saboda yadda yake jin kansa a duniyar sama,
“Ya makaranta..?!”
Pcap din kansa ya zare ya wullar a gefe, Zubewa yai akan kujera saboda tangadin da yake yi. Duk da acikin maye yake, Bai gama sakin saba, hakan bai hana shi dafe kansa da hannun sa na dama ba ya runtse idanun sa dakyar yace,
“Ammi...! Barka da rana.”
“Barkan mu Abdul.. An dawo lapia? Maza tashi jekai wanka kaji? Kafin ka fito za’a shirya maka abinci..”
Mik’ewa yai dakyar yana tangadi yayi hanyar fita kenan ta katse shi,
“Ina zaka Abdul?.”
“Waww..Wan.. Wankan zanyi.”
“Au.. Shiga bandakin kasa na cikin dakin nan kayi. B’angaren ka sai dai kayi hak’uri, Yayan ku ya kara aure amaryar can take.”
Wani ashar ya lailayo ya dura yana rike cikin sa,
“Amma bashida mutinci. Bara na fito sai nayi ‘kasa kasa dashi.”
Yana magana yana tafiya har ya shige cikin dakin, Kansa ne ya shiga juyawa ya zube akan gado ya fara jan munshari take baccin maye yai awun gaba dashi.
Gurfane Ammi tayi tana girgiza kai, Matsalar ta duk duniya akan yaranta ne. Dan autan ta da zata kalla taji dadi shima an gurbata tasa rayuwar. Kullum cikin shaye shaye, Ba’a makaranta ba ba’a gidan ba. Makarantar kwana suke suna babbar sakandire. Kullum idan sunyi hutu shi sai ya jima kafin ya dawo hakan ce take kasancewa dashi, Yaita shaye shaye yana debo mata magana.. Gashi dik cikin sauran yaran shi kadai ne meyi..
Sabon shafin kuka sosai Ammi ta bude tana yin sa ba kakkautawa.. Tarasa madafa, Tarasa farin cikin ta, Hannu ta daga sama tana rokon Allah daya kawo karshen wannan kaddarar rayuwa da take gani itada ahalin ta kala kala...
*GIDAN GWAGGO TA FADA*
Band’aki na shiga na canza pad din jiki na, Wannan jini na rasa ranar da zai dena kwarara, Ya ragu sosai ba kamar da ba. Amman har yanzun yana fitowa. Wani lokacin harda guda guda.
Kaya na zura marar nauyi na fesa turare mai sanyin kamshi marar karfi. Haka kawai na tsinci kai na da kallon kai na ta mudubi. Shin ni din menene laifi na da mutane basa so na? Se bina da sharri da mugayen alkaba’i? ‘O ni dije Allah ka jikan iyaye na da rahama, Wasu abubuwan da akeyi min don rashin babu idanun su ne. Tabbas iyaye katanga ce mahallakar makiya. Nayi kewar ku Ummah Da Baffanah. Allah yasa aljannatul frdwas ta zama makoma agare ku da dik musulmai baki d’aya.’
Siraren hawayen da suka zubomin na goge da tafin hannu na, A haka addah maryama ta shigo ta same ni.
“Ah’ah! Gimbiyar gimbiyoyi, Takawar ki lapia sarauniyar zuciyar sarkin garin mu adali me son mu, Dan Allah ki dena zubar da hawayen ki, Inajin ciwon hakan har cikin zuciya tah... Kinji?!”
Murmushi nai kawai hade da kada kai na. Ta tako har gabana tana mai rufe murfin Kullaccam din dana gama shafawa,
“Gwaggo na neman ki..Tana babban parlor ki sako mayafi ko hijabi domin itada bako ne.”