← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 114

Sashe 112

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ku saurara bangama ba, Malam ilya, Malam Sabiu ya isa haka nan, Ku saurara jama’a. Wannan mutanen da sukazo daga birni wakilan gwamna ne dana sarki, Sunce a shaida muku an soke zancen tashin mu, Sai dai abu d’aya ne zasu yi amfani dashi, Gonakin mu na bayan gari dana gefen kan tudu wajen rafi, Dana gangaren bakin kasuwa... Zasuyi amfani dasu wajen ginin makarantar kwana babba wadda yan bautar Kasa zasu dinga kwana, Duk wanda gonar sa ta shafi wajen to sunce Za’a biya kudin gonakin baki d’aya harda karin wasu kudaden, Sannan matar mai martaba wadda ance zatazo nan gaba, Tasa a mana titi kyauta wanda zai kai har cikin birni... Yadda mukayi dasu, Saboda haka cikin satin nan Za’a fara aiki, Nasaka hannu na wakilce mu baki d’aya nida hakimi. Yanzu zamu zaga gonakin dan daukar sunayen duk manomin da gonar sa take wajen, Za’a aika da takardar birni, Zasu zo da kudaden kowa..”

Sai farin ciki, Gaba d’aya dattijawan mazan da mata dake leke ta saman zaure sai suka fara murna, Kowa fuskar sa dauke da farin ciki marar misaltuwa. Mudi ma tsabar farin ciki ko zancen basu gama ba da Abasiyya ya mike zai tafi, Abasiyya taja hannun rigar sa, Fuskar nan tata tasha dige digen jamfarce. Girar data zana ta hade da kunne. Ba sauk’i dai gaba d’aya. Ita nan ta kure karshen gayu.

“Ina zaka bamu gama ba.”

“Sauri nake Bebi Abassy tawa. Zanzo zancen ai anjima.”

“Yasin ba zuwa zakai ba, Kawai dai kai tsoran ladiyo kake har yanzu..”

“Allah ya sawwake, Kede ku bari akawo kudin auren kiga. I lobiyu bebi ta.”

“I lobiyu nima nawan. Mezan samu?”

“Ungo wazobia, Kafin nazo anjiman.”

Sallama sukai ya tafi gida yana tuno yadda Abasiyya Zata zama matar sa. Yana shiga ya fara kwalawa su Gajiyalle kira,

“Gajiyalle, Gajiyalle.”

Fitowa tai daga bandaki tana dafe ciki,

“Mudikalle ina maganin zawon?”

Mudi ya dashare baki yana cizan yatsa, Hamsin din data bashi ya siyo mata maganin kenan ya bawa abasiya kudin tad’i.”

“Tab ki jika kwakin jiya kisha kawai, Gajiyalle an fasa tashin mu daga durbun, gonakin su ale hamza kawai Za’a yi amfani dasu ayi makarantar.”

Gajiyalle ta dankara masa harara tanemi gefen dutsin gurji ta zauna tana nishi,

“Bankadadden banza, Mokadadden wofi, Kana gani wazobiyar adama ce dakyar ta aramin saboda yadda naketa zaryar zawon nan shine zakaje ka kashe? Toh narantse da uban daya haifeni ko zaka siyar da kan rantalelen danka sai ka kawomin wazobiyar nan.”

Mudi zai magana ladiyo tafito tana gud’a da hanci,

“A hayye! TubarkAllah Masha Allah, Ga rantalelen kai nan a jikin ki..”

Mudikalle zai magana ladiyo ta dire tsallen albarka tana karkada masa hannu,

“Ja tsaya karamin munafiki maci amana, Wa yagaya maka bansan Abasiyya kake nema ba zaka aura? Ko kaga anwa uwata kishiya da zakayo mun? Baka isa ba wallahi, Kaje can ku karaci sharholiyar ku da ita, Amman ba zaka auromun ita gidan nan ba. Gida nawa ne nan bana wata ba.”

Gajiyalle dake numfarfashin ciwo jin ana tunkaho da gidan ta saita mike tayo kan ladiyo,

“Wane gida ne naki? Nace uban wa ya baki nan gidan.”

“Badake nake ba tsohuwar kilaki kawai, Tsabar gulma da munafurci kin tako tinkis tinkis kina jan kafa. Maza kafin nasa k’afa na shure ki.”

Nan fa gajiyalle ta cire dankwalin dake kanta, Gashin ta ya zama furfura yayi dagaje dagaje, Ta daure dankwalin a kugu tana lailayo ashariya tana zundumawa ladiyo.

“Ke sanyi nai, Ki tambayi kowa, Wacece Gajiyalle mai yar hakiya, Duk matan garin nan a baya ba wanda ya kai ni yawan kiwo da zabbi da kaji...”

“Ina ruwana dasu, Tunda ban shigo na gansu ba, Abinda nasani shine kin kuntatawa yar mijin ki kin zalunce ta, Kowa da yake ubanta ma ke kika kar shi.”

“Kinci malamar kan uban ki. Da uwannanniya mai yakuwa gyatumar ki zanyi ba dake ba.”

Cewar Gajiyalle cikin fushi, Ko mayafi bata saka ba ta fice fuuu Mudi na tsaye ya rasa yadda zai yi. Halipha ‘dan su sai jan rigar sa yake,

“Abba abinci. Abba abinci.”

“Zo nan halipha muje bakin kasuwa”

Cewar ladiyo. Mudikalle zai hanata fita, ladiyo ta dura masa ashar tana karkada masa hannuwa,

“Kai ka isa ka hanani fita, Babu zanci agidan naka? Bakin kasuwa anan ka auro ni, Don haka dole ka kyaleni tunda tun fil azan acan ka ganni. Idan gyatumar ka tadawo kuma ta tankade mana garin can, Matsa sullutu kawai.”

Tana gama magana ta sabe halipha a hannu tafice, Shi kuma Mudikalle ya rasa yadda zaiyi, Daga karshe ya yanke shawarar bin Gajiyalle, Acan ya tarar dasu da sirikar sa uwannanniya sunata dambatuwa da Gajiyalle, Sai kasa ce ke tashi. Duk yadda akai aso rabiyar fadan nan sai da aka kasa. Sai da suka daku lilis sannan wakilin mai unguwa ya tasa k’eyar su duka biyun zuwa gaban mai unguwa jamilu domin ayi shari’a......

_😂💔Haka dai zaman yake kasancewa a durbun: Ladiyon Mudikalle kenan a gidan Gajiyalle mai yar hakiya... 🧚🏻‍♂️_

Asha hutun weekends Lapia ❤️
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B33_

****Zaune nake a cikin daki duk nabi na gaji sai kace wacce tayi aikin wahala, gaba daya zaman dakin ne ya ishe ni, ina son sauka kasa na dinga ganin gilmawar mutane amman babu hali Salman ya hanani a cewar sa za'a Iya hada baki da masu shigowa sashen nawa su barbad'a wani abin, tsautsayi yasa na bi takai su illatani ko su illata baby.

Sallamar d’aya daga cikin hadimai a kofar daki na yasa nai saurin waigawa Ina amsawa, na bata umarni ta shigo bayan na zura hijabi a jikina. Hannunta dauke da jug garai garai wanda hakan yasa ni hango ko menene a ciki wato damammiyar fura da nono an sanya kankara a ciki gwanin ban sha'awa,

“Ranki ya dade mai babban daki tace a kawo miki ko kina da bukata, Umma Hansatu bata kusa shi yasa ta bayar a kawo miki.”

Tunda na hango furar nan babyn ciki na ya/ta dinga harbi na kamar za'a huda min ciki. Na karba jiki na kyarma tare da yin godiya ta juya ta fita, na karasa wajan table na ajiye tare da dakko kofin da nake shan shayi na zuba, ni kai na yadda furar tayi shar ga kamshin ayaba dake tashi a ciki yasa na kagu na ji ta cikin baki na. Karar da wayata keyi ne ya dinga rabamun hankali saboda ringing d'in Salman ne, na dauki kofin tare da karasawa gurin wayar ina shirin dauka naji ta tsinke dai dai sannan kuma naji an shigo cikin dakin da gudu, kafin na tabbatar da waye naji an buge kofin tallatsin furar ya sauka saman fuskata.

Salman ne yana tsaye sai faman haki yake da alama gudu ya yi da zai taho. Ya dafe kai tare da rintsa idanuwa, ni kuma na yi kicin-kicin da fuska rai na a bace dan na shirya kaiwa baki na ya yi min wannan abin. Kusa dani ya matso tare da rungume ni, kai na dake kirjinsa yasa kunnuwa na jiyo min yadda bugun zuciyarsa ya tsananta. Murya na rawa yana shafar bayana ya fara magana.

“Karki sha furar nan Zawjatii... Kar ki sha. Karya ne ba daga gurin Ammi aka aiko dashi ba, daga gurin Jaleelah ne waziri ya zuba maganin da ya karbo gurin wani tsibbun nasu shi dasu wambai shine suka kawo miki.”

“Innallilahi wa'inna'ilaihir raji'un... Na shiga uku ni Dije, me yasa banyi wannan tunanin ba? Karo na ba adadi kenan, Koda yake sunyi amfani da Ammi kuma daman Umma Hansatu ta tafi gurinta karbo min kilishi, shi yasa nayi tunanin da gaske ne, kai ya akai ka sani?”

Sai da ya dan dago fuskata ya kalleni ya sake maida kai na kirjin nasa yace.

“Ina ciki Ina wani bincike nagani, bayan sun bawa waziri maganin , Shi kuma ya zuba maganin sai suka bawa jakadiya Abu tasa a hijabi ta nufi bangaran Ammi, to daga can ne ta bawa yar aikin Ammi tace ta kawo, ita kuma da tazo ta bawa daya daga cikin ma'aikatanki tare da yi miki bayanin da tayi miki cewar inji Ammi. Na kiraki tun farkon da naga kin karbi kofin amman baki daga ba, ganin kin tashi yasa ni fitowa da gudu karki je kisha kija min asarori.”

“Kai wannan masifa da me tayi kama?”

“Shi yasa nake son mu kuma yin taka tsantsan dan gabaki daya mutanan nan sun shirya lalata min cikin dake jikin ki. Takun da Zaki canza yanzu shine ki dinga zama da hijabi yadda zasu dena ganin girman cikin nan bare su kawo masa hari.”

“Na shiga uku a dakin nawa na sai na saka hijabi?”

“Eh! Dan Allah kiyi min wannan alfarmar dan Allah my love.”

Na rausayar da kai, ni kai na ina jin yanzu na fishi kaunar cikin nan saboda yadda nake jin kaunar abinda yake ciki. Salman ya dago ni tare da karasawa dani wajan gado muka zauna, kafin ya yi magana na riga shi.
Chapter 112 · 0% Book details