← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 114

Sashe 111

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abba ance fa cikin yafi wata hudu, kuma na gangaru da yake min aiki yanzu yace ya kasa gane meye a cikin mace ko namiji, shine na kira na ce ko z....”

Bata karasa ba waziri ya yi hanzarin katse ta.

“Kinga Jaleela ki rabu dani, duk wannan fafutukar da nake yi so nake naga sarautar ta dawo hannun mu, Amman gashi nan abu yana neman hargitsewa. Tun farko nace miki muyi maganin su Abdulqadeer dasu Maheer, ya zamana duk yara mata gareku, amman shegen taurin kai irin naki kika ce, A'a ai kuna hade dasu Huwaila. Toh yanzu..Sai kije ku nemo mafita da kanku, su suna da maza Wanda ko babu jinin Salman a duniya zasu Iya karbar mulki, kuma tsab zasu Iya korarki daga cikin masarautar. Dan haka ki rabu dani naji da abinda yake damu na nima.”

Zata kuma yi masa gardama ya katse kiran tare da jan wani mugun tsaki dan a yanzu Kowa ma waziri haushinsa yake ji musamman a wannan lokacin da yake cikin zafin zuciya da bacin rai. Kaya ya sauya ta yadda ba zaka taba tunanin shi bane, ya fito ba tare da yabi takan iyalinsa ba yaje ya dauki Mota ya fice.

Gurin tsibbun sa ya nufa, yana zuwa ya tarar da shi yana ta dariya ba kakkautawa, tsayin lokaci bokan na dariya waziri be kula shi ba dan hatta shi din ma a wannan yanayin zai Iya yi masa rashin mutunci dan yana ganin kamar ma yana sane da cikin amman be sanar masa.

“Nasan dama zaka zo da kanka ba aike ba, nasan zaka shiga cikin wannan yanayin shi yasa tun farko nace maka Salman baya amfani da duk maganin da kake kai masa.”

“Ni yanzu so nake naji daga Ina matsalar take?”

“Hahahahahah aljanu su taimake ni na taimaki Waziri. Ai babbar matsalar tana tare da Salman, Gimbiya Khadija ita ce matsalar ku gabaki daya waziri. Wannan yarinyar da kuka raina, kuke ganinta kamar karamar alhaki, a yanzu itace zuciya da ruhin sarkin ku Salman.”

“Kana nufin kace min cikin da ake magana na Salman ne? Ta ya ya hakan ya tabbata bayan shi din juya ne bashi da wani tasirin yiwa mace ciki?”

Boka ya kalli waziri tare da cewa.

“Koma dai menene kuje ku tambayi matarsa ta farko, ita tasan menene gaskiyar lafiyar sarki Salman game da samun ciki.”

Waziri ya kuma kallon boka cike da takaici, Sannan ya kawar da kai yana furzar da iska daga cikin bakinsa yace.

“Ina son kayi min dalla-dallah da kanka, bana son naje na samu kuskuran magana, ka gaya min duk abinda yake faruwa.”

Sake bude idanuwa Bokan ya yi tare da daukar wani faifai mai dauke da kasa a ciki ya yi dangwale-dangwalensa, kuma kallon waziri ya yi yana wani irin abu da harshe kamar tsohon maye sannan yace dashi.

“Idan har kuka bari aka haife abin da ke cikin nan da rai, humm-hummm waziri.”

“Yanzu babu abinda zaka Iya taimaka min dashi?”

“Akwai magunguna waziri, kaga Ina da wanda za'a Iya kwantar da cikin ta shekara goma be tashi ba. Akwai Wanda zata Iya haifa amma babu rai. Akwai kuma wanda zamu bayar tayi barinsa Koda yakai watanni tara. Wanne kake so? Saboda ko wanne yana da sharrudan da za'a kiyaye.”

Waziri ya gyara zamansa cikin ransa yana jujuya wanda zai ce ayi, daga kashe dai yace da Boka.

“Ina son ka bani wanda za'a daure cikin ya zamana tamkar babu shi dan bana son ma ace tayi bari ko ta haihu ya mace, wannan duk zai sa Mutane su san cewa zata Iya kuma haihuwa nan gaba. Amman yanzu idan aka daure cikin kaga Sai ayi ta faman jira aji shiru har ma ace tayi karyar ciki dan ta cuci mai martaba.”

“Aljani d'an tsartu ya karbi bukatarka, yanzu haka zai kawo maganin da za'a baka.”

Boka na rufe baki kuwa sai ga wani kullin leda baka ta fado, Bokan ya dauka tare da mikawa waziri yana kuma yi masa karin bayani.

“Karbi wannan maganin, yanzu Aljani d'an tsartu ya karbo maka a can kasar faleru. Za'a zuba shi cikin abu mai ruwa wanda take sha, ko lemo, ko Shayi, ko kuma ruwan sha. Idan har ta sha sau uku yau daya gobe biyu jibi uku, Ina mai tabbatar maka da cewa rana ta hudu zata tashi taji batajin komai a cikin ta.”

Cike da murna waziri ya amsa yana jujjuyawa, muryar Bokan ce ta dawo dashi daga kawa zucin da ya tafi, inda yake cewa.

“Da akwai sharadi.”

“Toh Boka wane irin sharadi ne? Gaya min saboda indai akan wannan lamarin ne zan Iya yin koma menene.”

“Shikenan tunda kace a gaya maka. Sharadin shine idan har bata sha ba tsawon kwanaki uku. Zaka shiga cikin mawuya cin hali, wanda kai kanka Sai ka kyamaci kanka bama wani ba.”

“Toh Wai me yasa ba za'a kashe ta ba ne ita yarinyar?”

“Na Sha gaya maka ba zamu Iya halaka ta ba kai tsaye, kasan munsha gwada tura aljanu dan su kashe ta. Amman sai a kama mana su, wajan aljanu dari uku aka kama mana duk a sanadin yunkurin kashe yarinyar. Kayi hakuri da son kashe ta dan ba abu ne me yiyuwa ba.”

Ajiyar zuciya waziri ya sauke daga nan ya zaro uban kudi ya ajiyewa Boka, a cikin aljihu ya saka maganin daga nan ya mike ya tafi ba tare da ya yi masa sallama ba. Burinsa kawai yaje ya aiwatar da wannan aikin maganin, tare da daukar aniyar hana Dije da Salman kwanciyar hankali...

.....Falaki na daga gefen farfajiyar fada da wayar sa a hannu yana duba tracking din Waziri, Tun daga tafiyar sa har zuwa dawowar sa fada. Saving yai ya turawa Salman. Ranar dai gaba ki d'aya Waziri bai shiga fada ba. Koda ya dawo ma da daddare suka hadu dasu wambai, Waziri ya sanar musu da cikin dije, Kowannen su ya shiga cikin madaukakiyar damuwa da tashin hankali. Gaba d'aya tracking d'insu waje d'aya ya nuna. Salman shi abunma daria yaso bashi , Suna daga zaune shi da dije suna kallon su, Suna kuma cin gugguru sai kace a cinema..

"Kada ki damu da makaman tsibbun su, Lapia zaki haife abinda ke cikin cikin ki.. Sannu ahankali zasu san wannan cikin KIBIYAR AJALI.. Zai zamar musu, Mai dauke da cikin kuma kainuwa ce, Domin ke din sulke baya tare ki sai kin gitta..."

Nayi dariya ina shafa sajen sa dake kyalli..

"Insha Allah honey bunny, Da Allah muka dogara, Yanacan a madakata. Oganniya yar baffana nake, Ko Gajiyalle hakura tayi ta sallama...."

Kafa yasa ya kwantar da kujerar da muke Kai tazama kamar gado. Yasa hannu d'aya yana zagaye labbana.

"Mantar dani damuwar su zumaaa na."

Murmushi nai kawai domin na gano me yake nufi, Na juya masa baya. Hakan ya bashi damar kashe fitila muka tunkari abunda ke gaban mu. Ina kaunar Salman, Domin a fagen soyayya anya yanada na d'aya kuwa?... Duk wata damuwata a daren nan sai dana nemeta na rasa, Sai ma samun kai na nayi da tallafe abuna muka gurji soyayyah..

*DURBUN*

*MAI GARI JAMILU*

“A hayye- A hayye, Ga jirgi ga jirgi! Ga mota ga mota, Yan birni-Yan birni...”

Haka wasu dandazon yara suka shiga zagaye kofar gidan mai gari jamilu suna ife ife, Sun taru rukuni rukuni suna kallon ba’kin da suka zo wajen mai gari jamilu, Jeep motoci guda biyu, Sai luxurious bus guda d’aya, Sai helicopter dake shawagi a saman kauyen, architect ne aciki yana zana yadda za’a yi makarantar, Da yadda za’a shimfidawa kauyen titi wanda zai kai kaika har kan titin birni. Bayan tafiyar yan birnin wanda nambobin jikin motocin su duk na gwamnati ne sai bus dince kawai me dauke da tambarin masarautar Basannabas. Mai gari jamilu ya sake tara dattijawan garin maza yana sheda musu yadda sukayi da mutanen da sukazo daga birni a takaice.

“Ku zazzauna, Ku saurara. Labari ne mai dadi nazo muku dashi.”

Mudi da yaje wucewa jin mai gari na cewa labari mai dadi yazo dashi sai yaja ya tsaya yana cigaba da bantarar raken dake hannun sa.

“Mai gari jamilu muna saurara.”
Cewar na laraba, Mahaifin su uwande.

Mai gari ya sake gyaran murya fuskar sa dauke da farin ciki,

“Kunsan muna cikin jimami na maganar da gwamna ya turo mana, Za’a bamu wajen zama a kauyen Landantsan dake gaban mu, A kuma biyamu kudin gonakin mu, Kusan dukkanin wani mazauni dake durbun kama babba, yaro, tsoho Kai har na goye yasan mu mutan durbun bamuyi marhaba lale da zancen nan ba, Amma ya zamuyi da gwamnati? Duk kuwa da marayar mu ce nan tun ta kaka da kakanni. Wasunmu har sun fara binciken matsugunin da zasu zauna a kauyen landantsan, Saboda makarantar kwana da za’ayi da sauran ma’aikatar aiyuka da za’ayi guda d’aya anan din,

“Toh albishirin ku mutanen durbun, So nake Kowanne daga cikin ku ya fadada murmushin fuskar sa har zuci, Ya kuma sanar da iyalai na gida yadda akai.”

“Kaga mai gari jamilu, Ni wannan dogon bayanin duk mun san shi, Menene alfanun maimaita shi Eh?”
Malam Garzali ya tambayi mai gari cikin kosawa.

“Kai kullum bakacin ribar zance Malam Garzali, Baka taba bari a karasa zance zaka hau ya akai?”

“Yo ai gaskia ne mai gari.. Dole mu tambaya, Nabar buhu na a daji ne kar awakai su cinye dan amfanin ciki.”

Mai gari ya gyada kai, Hade da mikewa tsaye sosai yadda na baya zasu gano shi. Sannan yafara magana da k’arfi yadda kowa zai juyo shi, Ciki harda mudikalle daya tsaida abasiya mai awara suna zance.

“Mutanen Durbun.!!! Mai girma gwamnan birni da mai martaba sarkin mu dake birni, sun ce a sheda muku, Maganan tashi mu koma kauyen landantsan na gaban mu an soke ta..”

Dattijawan wajen suka magana Kowanne cikin farin ciki,
Chapter 111 · 0% Book details