Sashe 5
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba d’aya karkarar ‘Durbun’ ta dauka da shirye shiryen bikin juya bai da zata yi. Kowanne lungu da sak’o na karkarar mutane ne ne keta hidima. Bikin juya bai yana gudana ne Bayan an samu alkhairin abubuwan da aka shuka na noma. Kamar yadda mai karatu yasani hausawa sukan ce :Na duke tsohon ciniki, ‘Kowa yazo duniya kai ya taras.’.
Noma na da ma'anoni da dama kasancewar irin amfanin sa a fannoni daban-daban. To amma dai a fassara mafi sauki, zamu ce, Noma wata hanyar sana'a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin arziki da al'ummai suka raja'a akan ta. A kasar hausa ko kuwa, noma shine babbar hanya ta samun habakar tattalin arziki. Da noma ne hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci dama kayayyakin da ake sarrafawa a masana'anta kamar tufafi da sauran su. A wajen hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen kowanne bahaushe musamman magidanci. Kusan muce ma ko wanne bahaushe ya iya noma yasan yarda ake yin shi. Noma ya kasu kaso biyu akwai: Noman rani da Noman damina. Noman rani: noma ne da ake yin shi a lokacin rani ba da damina ba. Sabanin noman rani, shi noman damina ana yin sa ne a lokacin damina.
Toh *BIKIN JUYA BAI* wasu kwanaki ne da mutanen karkara ke diba suna dandalar cimar kayan dadi, Mafi akasari cimar ta kunshi nama, Na kaji, Zabbi, Talo talo, Wasu kan yanka dabbobin su ayi dabgen miya. Wannan bikin dabdalar rakashen nama dai na faruwa ne a duk shekara bayan manoma na kauyuka sun ebe/kwashe amfanin gonar su.
*A* yau ranar asabar, Saboda haka naji mutan garin mu na yau asabar. Domin ni ba sani nai ba, Ba kuma damuwa nai nasani ba. Illa dai nasan yau zamu ci dadi mu godewa Allah. Domin gaba d’aya karkarar mu miyar ja zasu yi. Tun duhun safiya Gajiyalle ke safa da marwa tana lalleka zabbinta da kajin ta da yan dabbobin ta kar wani yai awun gaba dasu.
Bokiti na dauka nai gangare dan ebo ruwa a rafi. Ina tafe ina wake-wake na. A haka na ebo ruwan na dawo na fada bayi. Ba sabulun wanka ba nida soso rabo na da wanka mekyau inaga sai sallar bara da baba ya bani sabulu kafin Gajiyalle ta k’wace. Don haka yau so nake nayi kyau. Na ebo tokar murhu na duddurje jiki na da ita, Na kwara ruwa. Ina fitowa na sake dakko gawayi Mudi na farfasa na durje baki na dashi. Kai na sai tsami yake. Narasa ya zanyi dashi. Ruwa na kwarara masa na tsane da dankwali na. Kayan kuncen da Adama ta bani na saka. Kamar ranar sallah haka nake ji na. Iska sai kada ni take yi. Yunwa ce kawai ke addabar ciki na. Ina ta jera hamma sai ga baffa ya dawo hannun sa rike da leda,
“Baffa! Sannu da zuwa.”
“Yauwa Ummi na.. Ungo mika mata ledar nan.”
Leka cikin ledar nayi na hango kayan miya ne da mayi na ‘kuli sai tashin kamshi yake. Kai mata nayi ta amsa a dakile tana kallon Baffan mu a dakile,
“Haka za’ai miyar lami?”
“Ki dau zabo na d’aya da ya rage ai miyar dashi.”
Baffan mu ya bata amsa yana mai kwanciya akan tabarmar gefe na. Baki na tsuke da tafin hannu na ina murmushi. Yau zamu sha dabgen dadi. Baffa ya bani wazobiya yace na siyo koko. A dari na fece na siyo na dawo . Ko kadan ban tsaya siyan fada ba yau. Ina kawowa Gajiyalle ta kwace ta barmin dan mitsitsi. Jiki na rawa na karba na kwankwade shi tas. Na hada wanke wanke nayi, Duk aikace-aikacen da zanyi nayi, Daga nan na fece yawo na. Gidan su Zubaida kawata naje mu kaci abincin gidan su, Daga nan muka tafi gidan yan gayu gidan su Nafisan kansila. Sunada wuta, sun kunna talabijin. Gurfane nayi Ina kallon talabijin din, Wallahi yadda mutanen ciki ke magana sunyi shiga cikin birgewa abin ya sake burge ni, Naji inama ni ce. Matar an bata wani abun karfe ta rike tana magana ta cikin sa,
“Lasifika ce ko Nafisa?”
Na tambayi Nafisa ina mai nuna talabijin din da yatsan hannu na. Nafisa ta daga kai tashiga kwararo min bayani. Cikin haka yayan ta Bello ya shigo ya same mu. Ya zabga min harara nima na rama hade da gatsine fuskata. Wata kwalba ya mik’awa Nafisa ta karba tana tsalle,
“Dijangala! Zaki sha?”
Daga kai nayi na shiga motsa baki na, Daga gani zai yi dadi tun kafin ma taba ni. Zubawa tayi a kofi ta mikomin na karba jiki na sai rawa yake yi, Ina ayyana garar dadin da yan hanji na zasu ji, Yaushe rabon duniya da ayyaraye? Karba nayi da sauri na kafa a baki na. Kurba d’aya nayi na dawo dashi, Ji kake ‘phussss..’ a fuskar Bello. A zabure ya mike zai doke ni Nafisa ta shiga tsakanin mu. Ni kuwa gaba d’aya a rude nake. Na zazzago harshe na ina ife-ife,
“Wuta baki na, Wuta.. Wuta baki na. Wuta..”
Gaba d’aya ji nake tamkar harshe na zai zazzago saboda tsabar yadda yake radadi, Kirji na sai suka yake. A guje na tafi wajen rijiya na tinjimo ruwa ina kwararawa baki na, Ji nake tamkar harshe na da ciki na ake bankawa wuta. Sam banbi takan Nafisa ba dake tambaya ta menene? Sai da naji sa’ida sannan na zube awajen ina fiffita baki na, Na zabgawa Nafisa harara, cikeda jin haushin lemon wutar data bani nace,
“Gaskia Nafisa baki da kirki, Dan bakin munafurci shine kika bani abinda zai konamin yan hanji?”
Nafisa ta kece da dariya, Na mike ina gyara damarar kan zani na, Ji nake tamkar na karairaya ta tsabar haushi. Bello ya yo kai na yana karkada min hannu,
“Kede gaba d’aya baki da hankali, kidahumar banza. Dan tsabar reni lemon kazamin bakin ki kika zubamin a fuska. Ni sa’an ki ne?”
“Wannan ne lemo? Walle ba dai lemo ba. Kawai dai mugunta akeson hadamun.”
Bello da Nafisa mai zasuyi ba dariya ba. Suka shiga kyakyatawa. Na murtuke fuska ina gatsine baki.
Nafisa ta ri’ko hannu na tana murmushi,
“Be lemon wuta bane kawata. Lemo ne na sha, Sunan sa coke. Tsaya kiga ma na sha.”
Tana gama fada ta dauki kwalbar ta kafa a bakinta Sai da ta shanye tas sannan ta ajiye. Ganin dagske ta shanye hakan yasa na danji sanyi a rai na. Murmushi na mayar mata nima na dashare hakora na,
“Ayyo! Lemon yan gayu ne dai. To ai kuwa dai zanba su Larai labarin lemon nan. Tab.”
Bello yai tsaki kafin ya sakar min rankwashi a kwanyar kai na,
“Mugu azzalumi..”
Na fada ina sosa wajen. Har ya fara tafiya ya juyo yana kallo na,
“Me kika ce?”
“Ca nai adawo Lapia”
Na karasa fada hade da mai zunde, ya fice ba Tare da yace komai ba. Nafisa taja hannu na muka koma cikin parlorn su. Maman su ta zuba mana abinci fal da naman kaji. Abincin juya ban su na yan gayu. Muka hadu da sauran k’awayen Nafisa muka cinye tas . Suma mukajajje gidajen su muka ci muka koshi, Daga nan naja zugar yara k’awaye na muka tafi gidan mu. Muna tafe muna neman magana. Kafata tayi busu busu ba silipas.
“Oganniya ta Gajiyalle me yar hakiya.”
Cewar lantana yar gidan rumasa’u me kitso. Na kece da dariya kafin na buga tsakiyar zani na na ja guda,
“Sai ni Dijangala ta mai gari yar Baffan ta..”
“Gajiyalle ai ba babar ki bace ko? Ita bak’ace bata da kyau.”
Nafisa ta tambaye ni tana cigaba da irga duwatsun hannun ta. Na tab’e baki kafin na bata amsa,
“Yarinya Dagaske ba ita ta haife ni ba. Ni baba ta ta mutu dan kiji tun ina karama. Kuma ita kyakkyawa ce yarinya.”
Haka dai mu kai ta shirmen mu akan hanya har muka Karasa gidan mu. A tsakar gidan mu zugar k’awaye na suka zauna muka shiga yin yar carafke, Na lek’a gefen murhu inda Gajiyalle ke girki, cikin sa’a ta kammala tana karkasa shi.
“A zuba mana da kawaye na.”
Harara ta dankara min ta cigaba da karkasa abincin. Komawa nai cikin yara muka shiga hirar mu. Can Gajiyalle ta callarawa sunana kira. Na mike a sukwane har ina bal da robar ruwan dan akuyan Gajiyalle. Ina zuwa ta mikamin wani kwano cike da abinci yasha nama. Yawuna yatsinke, kunnuwa na sai rawar dadi suke.
“Ungo.”
Wayyo Allah na dadi! Yanzu duk namu ne wannan? Nama nasha nasha akai. Gudun kar nayi katobara Hakan yasa na sake tambayar ta namu ne da kawaye na.
“Na mu duka ne?”
Gajiyalle ta daga kai tana mai cigaba da kasa abincin gaban ta.A sukwane na karasa wajen kawaye na da kwanon. Muka hau ci sai da muka cinye tatas muka gyatse Sannan kowacce tatafi gidan su. Haba tsabar yadda yau naci na koshi kasa tashi nai nabi lafiyar tabarmar da nake zaune na kwanta sai bacci. Cikin daddadan baccin da yai awun gaba da ni na jiyo wani azababban dundu da aka sakarwa gadon baya na tamkar zai burma saboda yadda aka duma masa dundu. A firgice Na mike Ina sosa bayan. Ina bud’a idanu na na hango Gajiyalle da Mudi, Sai huci take,
“Dan guzumar uban ki ina abincin dana mika miki ki bawa Mudi?”
Idanuna suka kawo ruwa . Wane abinci taban na Mudi? Girgiza kai nayi Saboda hakikanin gaskiya kenan ni bani ta bawa abincin Mudi ba,
“Ba ni .”
“Zaki shiru ko sai na lakada miki na jiki. Yanzu dai dan guzumar uban ki ina abincin yake.?”
“Wallahi Gajiyalle bani kika bawa abincin Mudi ba. Iya abinci na da kawaye na kawai kika bani. Nace miki na mu duka ne? Ki Kai shiru alamun Eh. Amman bayan haka baki bani abincin Mudi ba”
“Dan guzumar uban ki. Ca ki kai na Mudika ne? Na daga miki kai. Uban wa zan zubawa abinci haka Idan ba Mudikalle naba?”
Na sake girgixa kai cikin hakikanin gaskia nace,
“Sai da na tambaya nace na mu duka ne? Kika daga kai alamun Eh”
Kukan kura Gajiyalle Tai ta shak’o wuya na tana huci.