← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 114

Sashe 16

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Baki ji ba ne?”

“Naji, kafa tace take ciwo.”

“Yanzu ta fara yi miki?”

“A'a tunda zamu dawo nida malama Mardiyya.”

Jinjina kai ya yi tare da kallon Siyama da Habi yace.

“Kuje ku riko hannun ta ku kawo min ita nan.”

Haushi ya kuma kamani, wannan malamin jarababbene uban masifa, Hege! Suka riko ni kawai na fara dingishi kamar wata gurguwa har suka kai ni inda nake zama idan shine a ajin. Ya shiga shafar gemo yana kallo na kasa kasa kamar wani marar gaskiya, sai kawai cewa ya yi.

“Kin ganki kuwa? Amman dai ba ke ki kayi wankan ba ko?”

Ban san lokacin da na daga masa kai ba alamar 'eh' sai kuma haushin kai na ya kama ni.

“Haba ni dai naga alama, toh Allah yasa dai a dore da tsabtar. Yanzu dai ga ki kamar mutum yanzu.”

“Kutmelesi! Da ni aljana ce ko me?”

Harar da ya watsa min itace ta tunatar dani a yadda na yi masa maganar, nayi saurin sanya hannu na toshe baki na ina muzurai.

Ci gaba da koyar damu ya yi jefi-jefi yana kallo na tare da yi min tambayoyi amman duk babu wasu kwararan amsoshi, a haka har ya kammala mana aka kada karaurawar tashi.

Ana tashi daga boko mun mimmike zamu tafi gidah Malam Auwal ya dakatar damu ta hanyar biga bencin gaban sa,

“Kowa ya zauna..”

Kowa ya zauna ban dani, Saboda ni yanzu bakin kasuwa nake son zuwa wajen Habibalo mai awara. Yanzu i war haka ta gama suya zata bayar da burbushin awara sadaka,

“Khadija Baffa samu waje Ki zauna, Kin tsaya gandar-dar a tsaye uwa sanda.”

“Malam sauri nake yasin. Me zamu maka ne bayan an tahi?”

“Uban.. Zaki zauna ko sai na lakada miki duka.”

Baki na na cuno gaba, Gwara ya casa ni akan ya hanani zuwa wajen Habi mai awara.

“Ke ba zaki zauna..”

“Jaraba gad’ar maza. Aikin banza.”

Na fada a hankali ina mai sake kafewa a tsaye, Tsumangiya ya d’akko sai dake ni, Sai ga malama Mardiyya ta shigo da littattafai fal a hannun ta.

“Ah’ah Khadija mai kike a tsaye?”

“Ko ba Malam bane zai daka ni? An fa tahi Malama, walle sauri nake akwai inda zani, Amma ya hana mu ko me zamu masa.”

“Zauna kinji? Karatun arabi Za’a fara muku yanzu. Kuma kullum hakan ce zata kasance da yardar Allah. Zan raba muku littattafai da Qur’ani, Malam Auwal zai fara yi muku nasa b’angaren kafin na shigo nayi muku iya matan kina ji?”

Kada kai nayi badan naso ba . Na koma na zauna kawai Saboda ganin mutuncin ta. Tana min magana ne a hankali kullum, Sam bata fada. Shiyasa take birge ni. Ba dan inason na zama kamar irin na gidan radiyo da talabijin ba da nazama Malama nima irin Malama Mardiyya.

Fita tayi bayan ta babbamu komai, Malam Auwal ya tsaya akan mu yana muzurai, Ni walle gemun sa irin na bunsurun Gajiyalle shi yake ban daria. Na sheke da dariya ina tafa hannaye,

“Ke Wai baki da hankali ne?”

“Walle dariya kake ban Malam.”

“Okay ga mahaukaci yana magana ko.?”

“Aa walle ba haka bane..”

Na fada ina gimtse dariya ta. Dogon tsaki yaja,

“Ballagaza kawai..”

Rubutu yayi a allo, Ya juyo yana kallon mu.

“Kafin mu fara komai, Zan dinga kiran sunayen ku a rajista shima, Wanda yazo ya amsa da ‘Labbaika Ya Sayyadi..’ Ba kamar na boko da zaku amsa da present sir ba ko sir. Kunaji? Fahimtun?”

Muka daga kai muna tafa hannuwa, Cikin nutsuwa ya fara koya mana karatun arabi. Walle da dadi, Sai na samu kai na cikin nutsuwa, Haka ya gama koya mana ya fita, Malama Mardiyya ta shigo, Ta fara koya mana nata bangaren. Ta bamu biskin da ruwan ledar fiya wata.

Ta kokkoya mana yadda zamuyi alwala da sallah. Ta k’ark’are mana da,

“Sai bayani na gaba akan”

1-Jinin Haila.
2-Jinin Nifasi.
3-Jinin Istihadha.

“Ku saurare ni da kyau, Domin duk kankantar mace wataran uwa ce. Yauwa Jinin Haila: Sassan da bayani zai gudana akai sune: A-Ma’anar Haila.B-Alamomin Jinin Haila.C-Muddan kwanukan Haila.D-Shekarun Haila.E- (karancin kwanukan tsarki.F-Rabe-raben Haila.G-Abubuwan da suka Haramta ko karhanta ga mai Haila da kuma ababen da suke mustahabbi gareta.H-Yadda ake wankan Haila.I-Hukunce-hukuncen Haila,

“A-Ma’anar Haila:Jinin Haila shine jini wanda yake fita daga mahaifar mace kowane wata na wasu kwanuka. (B-Alamomin jinin Haila:Jinin Haila ja ne wani lokaci yakan sauya zuwa bakii ko ya yi jajur,kuma yana da tunkuza wajen fitowa da kuma zafi,
“C-Muddan kwanukan Haila:Mafi karancin kwanukan Haila kwana ukku/biyu ne saboda haka idan ya kasance kasa da kwanaki ukku/biyu ne to ba Haila bane, Amma ance akwai mai zuwa rana d’aya tal. haka nan wadannan kwanaki ukku dole su kasance biye da juna,mafi yawan kwanukan Haila kwana goma ne.
“D-Shekarun Haila:Jinin Haila yana farawa ne da cikar ‘ya mace shekara tara saboda haka duk jinin da yarinya karama za ta gani ya fito mata kafin ta cika shekaru tara,to ba Haila ba ne,ko da kuwa yana da siffofi hailar.Haka nan jinin da mace ta gani bayan shekarun daina Haila –Shekarun daina Haila shekaru sittin ne ga wadda take Bakuraishiya,in kuma wadda ba ita ba bane daga sauran kabilu shekaru hamsin ne – Wato dai shekarun soma Haila shine shekara tara,abinda ake nufi da shekara tara anan shine lokacin da yarinya ta cika shekara tara cif-cif wato ba mujarradin shigar ta shekara tara ba a’a sai ta cika shekara tara din cif-cif,haka nan ita ma wadda ta kai shekarun daina Hailar sai ta cika shekaru hamsin cif-cif ba mujarradin shigar ta shekaru hamsin ba.
“E-k’arancin kwanukan tsarki:Mafi karancin kwanuka tsarki wato tsakanin wannan Haila da wannan Haila kwanaki goma ne,saboda haka zai iya yiwuwa mace ta iya yin jinin Haila sau biyu a wata amma fa da sharadin a samu tazaran kwana goma tsakanin Haila ta farko da kuma Haila ta biyu.Amma mafi yawan kwanukan tsarki to shi bai da iyaka wato a ce kwana kaza ne.
“F-Rabe-raben Haila:Mai Haila imma ta kasance wadda take ma’abuciyar al’ada ko kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba,wadda take ma’abuciyar al’ada itace wadda ta maimaita Haila sau biyu kuma biye da juna haka nan kuma ya kasance an samu dacewa a lokacin da kuma adadin kwanakin,ko kuma ya kasance a samu dacewa a cikin lokutan ka kai ko kuma a adadin kwanakin ka kai,to da wannan ne mace za ta zama ma’abuciyar al’ada mai lokaci tsayayye ko ma’abuciyar al’ada mai adadi tsayayye ko kuma ma’abuciyar al’adi mai lokaci da kuma adadi tsayayye.Ita kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba ta kasu zuwa kashi ukku wato imma ta kasance yanzu ta fara wato ba ta taba ganin hailar ba ko sauya kaya,ko kuma ta zamo wadda al’adarta ba tsayayya ba wato tana rawa,ko kuma ta zamo ta manta al’adarta,ita ma wannan wato wadda ta manta al’adarta ta kasu gida ukku ko dai ya kasance ta manta lokacin Hailar ta ko kuma ta manta adadin kwanakin Hailar ta ko kuma da adadin kwanakin da kuma lokacin duk ta manta.To duka bayanai sanka-sanka na wadannan rabe-raben Haila ana iya komawa ga littafan Fiqhu misali littafin Zubda ko Tahrirul wasila na Imam Khumaini.
“G-Abubuwan da suka haramta da kuma karhanta ga mai Haila:Daga cikin ababen da suka haramta a gareta akwai yin Sallah,Azumi, [dawafi,Iitikafi da kuma dukkan ababen da suka haramta ga mai janaba kamar taba sunan Allah da na Annabawa da kuma Aimma na Ahlul bayt ko kuma zama cikin masallaci.Haka nan haramun ne ga mijinta saduwa da ita.Wasu kuma daga cikin abubuwan da suke aikata su makruhi ne gareta akwai karatun Alkur’ani mai girma ma’ana daukar Alkur’ani Hizb sittin, Anan zan dakata sai zuwa zama na gaba idan Allah ya kai mu gobe. “

“Wallahi haka kawai na samu kai na da son acigaba da karatun nan, Domin tun ba yau ba. Yalwajin Innarajo na gayamin tafara jini. Billahil lazi na dauka jinin yankewa ne wai ahe sunan sa jinin al’ada. Hi’iyasa Uwande tace Innar ta tace data fara jini ta gaya mata? “Na kada kai ina jijjiga kafata.

“Akwai masu tambaya? Wanda bai gane komai ba ya tambaye ni kunga dai yan maza sun fita.”

Duk mu kai shiru, Malama Mardiyya ta sake cewa,

“Toh Allah ya kai mu acikin satin nan ni zan fara muku tambayoyi. kwa iya tafiya, Shikenan an tashi.”

__
_Asubah ta gari masoyan Dije, Ku shirya tsaf Dijangalar ku fa an kusa wayewa, Kada ku manta har yanzu muna kan shimfidar book dinne ne. Ko kun manta da yadda yazo muku a dandano😉? Na gayshe da yan comment box 1, Gaisuwar ku ga dije na zuwa kunne na, Ana gayamin sosai, Na kusa wantsalowa nima cikin box din a dama dani, Amma kafin sannan Nabila shehu, Maryam Saminu suleiman, (Islaha/Rip maryam) , Daughter billy, Da sauran wanda ban anbata ba. 🤲🏻Dije na godia kwarai😘🥰❤️ Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima tare da fatan alkhairi ga masoyan Dijengala dama zafafa books gaba d’aya.. OneLove😘❤️_

_WITH LOVE; MX🧕🏼_
*K & S*

*MX*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, DOMIN MALLAKAR NAKI, TUNTUBE MU A NAMBOBIN DAKE KASA*

*9*

*WASHE-GARI:*

*Ko da* na tashi daga bacci na fito tsakar gida, Buta na dauka na dibi ruwa na shiga bandaki. Ina fitowa nayi alwala yadda zan iya naje na bubbuga sallah ta wacce ban san iya adadin raka'o'in da nayi ba, na fito na bar gidan, daman tun jiya da uniform dina na yini kuma na kwana dashi, hakan yasa ina karbo sadakar koko na nayi makaranta hankali kwance.

Yau kam ban kwanta ba wajan bishiyoyin dake cikin makarantar na nufa, na kad’o mangwaro na zauna nasha abata babu ko wankewa amman ban damu ba. Har aka fara zuwa sannan na koma cikin yan ajin mu. Malama Mardiyya na zuwa ni ta fara nema, aikuwa ta ganni kamar yar jakuna, ba zaka taba cewa sabbabin uniform bane a jiki na duba da yadda suka ci uwar dauda. Ta kalle ni bayan ta rike habar ta tana cewa.

“Yanzu Khadija kayan makarantar ne kika mai da su haka? Amman dai baki cire su ba tunda kika saka su ko?”

“Wallahi malama ban cire ba, yo ji nayi anata yabo ana fadin nayi kyau hi yasa naki cewa sai nan da sati biyu.”
Chapter 16 · 0% Book details