Sashe 4
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
••
Kukan akuyoyi da tunkiyoyi shine ya farkar dani, saboda ji nayi tamkar a tsakiyar kai na suke yin kukan. Ina bude ido naga cincirindon mutane tsaye a kai na suna kallo na kamar sunga mai hauka sabon kamu. Na tashi ina ‘kifkifta idanuwa ina kuma turo baki, kafin nayi magana sai na fara jera atishawa kusan guda shida a lokaci guda.
”Oganniya Dije yau kuma me ya hado ki da Gajiyalle har ta kore ki daga gidan?”
Malam Muttaka ya yi min maganar yana ri’ke da gemun sa. Haushi ya kamani na sake daure mayafi na dake kugu na tare da cewa.
”Waya sanin mata.”
”Kina nufin ba ki yi mata komai ba ta hanaki kwanan gidan ku?”
”A gida na kwana, kawai fitowa nayi nan ko zan samu na Allah ya bani abin da zan yi karin kumallo dashi.”
“Allahu Akubar Dijangala kina ganin rayuwa, toh Allah yasa ki samu.”
Ganin yana shirin tafiya ba tare da ya bani ko sisi ba, yasa nayi tsalle na dire a gabansa ina mai kallon cikin ido nace.
“Cewa nayi fa na Allah ya bani kuma naga ka tafi ko kai bana Allah bane?” Malam Muttaka ya yi sauran kallon mutanan dake wajan, aikuwa naga shi suke kallo, naji dadi dan nasan da kunya yace min shi ba na Allah bane yanzu a kafirta shi.
“Toh ai ni Dijengala yanzu haka bani da kudi, sai dai ki bari wata rana idan Allah ya sake hada mu sai na baki.”
Aljihunsa na kalla zuciya ta sam taki yadda da cewa ba kudi a ciki, na kalli mutanan wajan tare da cewa.
“Allah dai ya hana babu, kuma duk wanda yace a gurin nan yana da kudi ya boye yace babu Allah yasa idan ya fara tafiya su fadi, dan Allah kuce amin.”
Yara ne kawai suka amsa da amin sabanin manya da kuma matasan da suka san suna da kudin, kafin kace mene tuni sun gudu kamar wadanda suka ji karar bomb. Na kama kugu na rike ganin banyi nasara ba, gashi gari ya yi haske dan na dai Allah ya taimake ni naci dambun nan jiya da sai nafi haka wahala wlh. Hanyar gidan mu na bi da kallo, zuciya ta nason zuwa saboda ina son shiga bandaki, tsoron abinda Gajiyalle zata yi min duk da nasan ba zata kashe ni ba iya kaci ta buge ni kilama harda ciwuka. Ban samu kwarin gwiwa daga jarumar zuciya ta ba dake son na koma gida, sai dai na samu damar daga kafa nayi tafiya har zuwa gidan mai gari, inda na taki sa'a ina shiga ana gama damun koko. Na karasa wajan Ramma wato uwar gida da yake ita ke damawa, na durkusa kusa da ita ina washe baki.
“Inna Ramma sannu da aiki, dame zan taya ki?”
Sai naga tayi kicin-kicin da fuska da alama ta gano cewa wani abun nake son a bani, dan itama tasan hali na bana yin abu dan Allah sai dan a taimaka min. Ta sake matsar da bokitin kokon zuwa gabanta, na yi murmushi a raina nasan bazan bar gidan ba sai na samu abinda zan sakawa ciki na. Haka aka yi kuwa duk rowar Ramma a ranar sai da nasha koka da wainar rogo, ina gamawa kuma na kara gaba abu na, duk wanda ya ga yadda nake rayuwa yasan cewar ba'a gaban mahaifiyata nake ba, saboda rayuwa nake yi kai na tsaye, kuma alhamdulillahi duk iya rawar kai na da rashin nutsuwa ta babu wani fasiki da ya taba nuna zai yi lalata dani.
Muna cikin wannan rayuwa aka zo aka fara gina mana makarantar boko, ana ginin nan ne na fara samun goma ashirin a wajan wani bawan Allah da yake leburanci a gurin. Allah ne ya sanya masa jin tausayi na hakan yasa yake kyautata min, dan ko abinci aka kawo musu daga gidan mai gari sai ya ajiye min idan nazo ya bani. Ranar da aka buɗe makarantar harda manyan mutane suka zazzo daga birni, da hakimi mataimakin gwamna shine yazo ya wakilci gwamnan sakamakon shi baya kasar. Munyi murna tamkar anyi mana wahayi da gidan aljanna saboda ganin manyan motoci da ganin yan gayu, gaskiya kauyanci beyi ba, komai muka yi sai an gane cewa akwai karancin wayewa a tattare da mu.
Bayan an kammala komai baki suka tafi ragowar ruwa, lemuka da abincin da suka bari yara da manyan kauyen muka durfafar musu, ni da yake na iya rigima sai da na samo lemon kwalba uku da ruwa jarka biyu na kulle a gyale na sannan na kuma daurewa a jikina. Na nufi wajan kololin abinci na sunguma nayi gida da gudu harda masu biyo ni. Kai tsaye na shige bandaki ina ta faman nishi, ko Gajiyalle bata san da shigowa ta ba sai hanayi da ta jiyo ta fito tana tambayar.
“Danladi lafiya?”
“Dije ce ta dauke mana abinci, kuma mai gari cewa ya yi duk a rarraba.”
“Almura kace sata tayo?”
“A'a kwacewa tayi daga hannun Ayuba gashi nan.”
Danladi ya fada harda nuna Ayuba wanda yake ta faman huci kai kace da gaske kwato musu nayi.
“Toh ina take almurar yarinyar?” Gajiyalle ta tambaye su.
“Ai ta shigo nan gidan da gudu.” Ayuba ya fada yana sosa cikin hancinsa.
Gajiyalle ta shiga nemo ni longu-longu amman Allah besa zata duba bandaki ba, ta fito daga dakin Mudi tana cewa.
“Wallahi kuka bibiya ta haura ta katanga, kunsan ta iya tsallake ta tunda ba tsaho katangar gare ta ba, kubi bayan gari kila can ta buya.”
Ina jin lokacin da suka fita, na saki wata nannauyar ajiyar zuciya dan ba ƙaramin wahala nake sha ba a tsaye. Sum-sum-sum Gajiyalle ta ganni ina fitowa daga cikin ban daki, ta kasa magana sai kallo na da tayi tana rike habar ta alamar mamaki tsantsa.
“Iyeeeee! Kaga almurar yarinyar nan, dama kina cikin gidan nan?”
Ta fada tana sake kare min kallo irin na zaki yi bayani d'in nan, banji komai ba dab nasan ta akwai son banza, dan haka na ajiye kular dannan na kwance lemokan da ruwan ina cewa.
“Yo dan Allah Gajiyalle kowa yana diba ni bazan debo na kawowa iyaye na ba?”
Gajiyalle tace,
“Eh mana yar albarka, ai daman nasan kina cikin bandakin, shi yasa ma banje nemanki can ba. Ah! Lallai baki sun samu dadi irin wannan hinkafa harda hanta.”
Tana maganar tana luma katon hannunta cikin abincin, ta debi gurin naman ta kai bakinta tana lumshe ido. Na dinga buga mata harara ina miƙa mata jarkar lemo guda daya da ta ruwa. Amman matar nan ta sake dauke wasu ta barni da guda daya-daya tana cewa.
“Haba Oganniya Dije! Nima dai yau na ‘dan dana wannan kirararin da ake yi miki. Baffanki da yayanki fa duk baza ki bayar a ajiye musu ba? Haba ai ban sanki da haɗama ba autar Baffa.”
Haushi da mamakin ta suka tokare min a wuya na, matar da taki jinin taji mutane suna ce min yar fari yar autar Baffa, tana jin an fada zata fara masifa da jaraba race bani bace itama tana nan zata haifawa Baffa yara jira take yi ya maro daga talaucin da yake fama dashi. Amman yanzu dubi yadda take ta faɗa tamkar gaske, gaskiya mata makirai ne wallahi, kuma nasan da sun kare zata maida ni gidan jiya wato duka da zagi. Haka na hakura ba dan rai na yaso ba sai dan tafi karfi na, kuma a ranar bacci nayi harda minshari sai kusan karfe biyar da rabi na yamma sannan na farka, fitsari kawai naje nayi daga nan na dauki kular gidan mai gari zan mayar, na haɗu da su Ayuba dasu danladi sun dakko sanduna, gaba na ya buga na fara waige-waigen inda zan samu makami nima, can na hango gatarin malam Iro na faskare a jikin bishiyar kofar gidan sa, na ruga na dauka tare da nannaɗe siket d'in jikina nayi shirin yin dambe.
“Yanzu sai ki gaya mana wa muka kama?” Cewar Danladi yana nuna ni da sandar hannunsa.
“Cabdijan! Lallai ma yaron nan, kana nufin zan tsaya ku jibge ni ne sai kace wata shegiya? Wallahi tallahi duk yaron da bai fasa duka na ba nima bazan fasa buga masa wannan gatarin ba. Me nayi muku da zaku doke ni iyeee?”
Ganin yadda nake buga gatarin a kasa ina kuma yin tsalle ina direwa yasa duk suka tsaya daga nesa, sun san tsab zan iya dukan su dashi dan wani lokacin ba hankali gare ni ba.
“Yarinya idan ba tsoro ba ki ajiye gatarin hannunki kiga idan bamu yi miki tsinannan duka ba.” Laminu ya fad’a.
“Hahahaha ahaiyeeee nanaye! Bazan ajiye ba d'in kun dauka bani da wayo ni ma, kuma ku fara gaya min abin da nayi muku dan ni nasan banyi muku uban komai ba.”
Duk sai suka zagaye ni, kusan su bakwai ni kadai kamar wacce tayo musu wani abu. Na sake gyara gatari na ina nuna su idanuna a waje kamar wata zakanya. Da yake Danladi yafi cewa a doke ni hakan yasa na nufeshi da gudu da nufin kwala masa sai kuma yace kafa me naci ban baki ba, ganin haka da nayi ne yasa duk na bisu zan kwala musu suka gudu, ina huci na ce.
“Da ku tsaya mana ku gani yan iska kawai, kun dauka zanji tsoran ku ne?”
“Ke Dije kin fiye masifa wallahi, babu wanda baki taba fada dashi na a cikin kauyan nan, wallahi ki dena idan ba haka ba wata rana zaki sha wahala dan kowa haushinki yake ji.” Cewar malam Iro yana karbe gatarinsa da na dauka.
Ko kula shi banyi ba saboda daman haushi yake bani, mokotan mu ne amman suna ji Gajiyalle zata zane ni basa zuwa su taimaka min. Na dauki kular na tafi ina ƴan wake-wake na har naje gidan mai gari na basu sannan na fito na tafi yar kasuwa dan yin hira da kuma wasa da ƴan talla. Ban koma gida ba sai kusan karfe goma har da wani abun.
*BIKIN JUYA BAI*