Sashe 68
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Addah Maryama ce da masu aikin su guda biyu suka nufi sabon shafin nawa don ganin yadda za’a kwaso tsofaffin kayana azuba acan. Suna zuwa suka tarar sama da kasan an zuba furnitures, Komai Italian royal ne, Saboda haka kayan sawa na kawai suka dauka suka jeramin acan, Aka yayyafa ruwan magani da turaren habbatussaudah da tazargade. Da sauran magunguna da malam ya harhada ciki harda na tsari aka rataye a kofar shigowa.
Ta WhatsApp addah maryama taita turomin hotunan koina ina nunawa Ammi, Zuciata sai hasaso shaheedah take, Shin ko awani yanayi take yanzu? Oho. Kai bama ita kadai ba harda su gimbiya Jaleelah. Duk na gano bakin su d’aya, Amma kowannen su yanada wani boyayyen quduri a zuciar sa game da Salman da karagar mulkin basannabas.
Ranar gaba d’aya Addah maryama da masu aikin su a masarauta suka kwana, A sashe na, Ammi taimin adduar tarewa lapia hade da fatan alkhairi. Amma bata rakani sabon sashe na ba, Saboda gudun abinda zaije ya dawo dongane da Salman dinma anan yake.
Tabbas nera tayi kuka agidan nan, Kaya wanda suka amsa sunan kayan gida su ne acikin sa. Kai harya dustbin k’irar Royal ne, Murmushi nai tunowa da nid’in ba tabbata zanyi aciki ba, Nan da lokaci kalilan da komai ya tabbata zan karb’i takardar saki na na kara gaba..
Munsha hira sosai da Addah maryama tana kara dorani akan network, Sai da muka raba dare muna hira tukun sannan bacci mai nauyi ya dauke mu..
*GIMBIYA SHAHEEDAH!*
Sashenta ta shiga tana kuka, Dama akwai lapiar zagi, Haka taita lailayowa tana durawa hadimanta, Kayan babban parlorn ta kuwa haka taita farfasasu tana kuka, Tamkar idan tayi hakan magani zasuyi mata.
Ranar dai mutum uku ta targada daga cikin hadimanta. Dak’yar ta iya janyo waya ta kira mahaifiyar ta ta sheda mata komai, Ta bata hak’uri da doriyar ta kwantar da hankalin ta, Khadija yasar ta za’ai a fitar da ita daga masarautar nan ko da rai ko babu. Sai a sannan Shaheeda ta danji sanyi sanyi a ranta,
“Shikenan Hajjaju... Na hakura, Amman kamar yadda kikace wallahi ba zan bari su samu sukuni ba, Tunda ta shiga gonata sai na nuna mata ita kaskantacciya ce.... Ki sanarwa wannan banzan bokan aikin sa baici ba dan haka kaza ta ubansa...”
Tana gamawa ta katse kiran ta kuma jefar da wayar ji kake tartsssss.. Ta fashe. Tashi tai ta shige da’ki wani kullum magani ta dakko ta zuba a ruwan wankanta ta shjga wanka, Tanayi tana tsinewa Khadija albarka...
<><>••. <><>••. <><>••.
Komawata sabon sashe na yau sati d’aya kenan cif, Tunda na koma ban kara shiga sashen Salman ba, Saboda daga kofata idan na saka maganin yana ruskar sashen sa, Gashi karatun AlQur’an nake so nake na sauke hizb sittin. Shiysa kullum ina daki ban cika fita ba, Ko gayda Ammi sai bayan kwana bi biyu nake zuwa yanzu na dukufa sosai ina addu’oin neman kariya.. Ta window na ina kallon shige da ficen da shaheeda keyi kullum, Sai zarya take safe rana dare. Ta d’auka ina wajen sa. Ni abunma dariya yake bani. Ba ita kadai ba, Su wambai ma kusan kullum sai na jiyo hargagiyar su, Suzo saitin kofata suyita yada magana.. Na kanyi murmushi a duk sanda suka yi haka, Ni wallahi gaba d’aya yanzu basa damuna. Kuma lokaci kawai muke jira da zai bayyana gaskiyar komai. Yanzu kam Alhamdulillah muna samun cigaba sosai a bangaren Abdullah domin har ya zana SSCE successfully.
____Turare masu sanyin kamshi na shafa, Na nufi sashen Ammi. Har a raina nake jin ta. Shi yasa bana iya kara kwana biyu ban lek’a mata ba, Musanman da magungunan temakon su yake hannu na. Wadaraccen mayafi na na yafa akan doguwar rigar jikina ta lace. A hanyar da zata fitar dani daga sabon sashe na na had’u dasu gimbiya jaleelah, Gaishe su nayi suka amsa babu yabo ba fallasa,
“Sai ina kuma amarya..?”
Gimbiya Najwa ta tambaye ni tana karewa kayan jiki na kallo..
Takaici ya isheni, Su din ina zasu je da daddaren nan? Na yatsina fuska ina bin farcen hannu na da yasha lalle da kallo. Can cikeda k’asaita nace,
“Zan kai gaisuwa ne... Daga unguwa kuke ne?”
Suma yatsina fuskar suka yi, A dakile gimbiya Jaleela taban amsa,
“Uhm... Munje zagaye ne.”
“Okayy! Sai da safen ku. Allah ya tashe mu lapia.”
Gaba sukai basu amsa ni ba, Nima na wuce ban sake bi ta kansu ba. Ta baya na zagaya na shiga sashen Ammi, Suna zaune da Abdullah kunnen sa saqale da earpiece,
“Ammi..! Barka da dare.”
“Barkan mu dai Khadijaa.”
Ammi ta ansani ni cikin fara’a
“Abdullah ya gari..? Me ake jine?”
Turo baki yai gaba yana yatsina fuska,
“Wani abune..”
“Okay! Kaci abinci? Ko a soya maka favorite dinka a hada da tea dinnan me dadi?”
Saurin kada kai yayi yana murmushi, Nima murmushin nayi, Shi dai yanasan wainar fulawa da ruwan shayi marar madara. Shiysa na dage nake masa saboda shayin nake zuba maganin da Malam ya bayar, Kuma Alhamdulillah anata samun ci gaba. Domin Abdullah sosai ya rage yawan daren da yakeyi, Kuma baya shaye shayen abubuwa kamar sanda na dawo masarautar. Sai dai kawai yayi shiru yana jin waka baya shiga harkar kowa. Wakar ma so nake ahankali na koya masa ‘kinta, Ta yadda komai zai dai-daita.
“Kede bakya gajia Khadija? Ki bari su Na’imah suyi mana?”
“A’ah! Bakomi Ammi, Bara nayi sauri na kammala.”
Kitchen na shige, cikin k’ank’anin lokaci na gama hada kayan wainar fulawa na fara soyawa ina zuba masa acikin food flask. Ban d’au lokaci ba na kammala soyawa, Na hada masa tea din na zuba duk abunda malam yace kamar koyaushe na kai masa na ajiye,
“Sakko kaci Abdullah...!”
Lumshe idanu yai ya bude yana murmushi,
“Na...Nagode Kh..”
“Uhm uhm dai bana hana sunan na ba..” Cewar Ammi tana gyara masa.
“Thanks Aunt Kay.”
Murmushi nai, Kaina har girma yake Idan naji yana cemin Aunty Kay dinnan, Sufa yan gayu komai nasu na dabanne. Gashi mun fara sabawa dashi, Ammi ba kadan ba takejin dadin hakan. Sai dana tabbatar ya cinye komai sannan na musu sallama na koma bangare na..
Ina cikin tafiya tamkar ance juya kawai na hango shaheeda sai zuba sauri take yi, Ko kallo na batayi ba ta shige ciki wajen Salman, Murmushi nai kawai na shige sashe na, Turaruka nima na bulbula na *yerwaincense&more* Sannan na cokala dauri na ya koma ture kaga tsiya, Wadataccen gashin kai na ya bayyana..
Lemon iced drink na dauka, Ina tafe ina taunar strawberry chewing gum a baki na, A haka na shiga wajen Salman baki na dauke da sallama. Suna zaune shi da ita, Ya tallafe habarsa yana kallon cup din gaban sa data zuba masa tea. Ina shiga ta dago ta zabgamin harara, Nayi murmushi ina danne dariyar data tahomin,
“My Whole world... Barka da dare.”
Da sauri ya dago ya kalle ni na kashe masa ido d’aya ganin tana kallo na, Batasan da biyu nayi hakan ba.
“Yaya... Yaya barka da dare.”
Daga shi har ita tsayawa sukai suna kallo na, Na sake maimatawa ina dashare mata hak’ora, Mik’ewa tai tana fiffita da kasan mayafinta duk kuwa da na’urar sanyaya parlor dake sanyaya mu,
“Yaya.... ?Ke banason munafurci, a gidan uwar uban ki na zama yayar ki? Salman ka shiga tsakani na da yarinyar nan wallahi, Dan yanzu sai mu debi yan kallo.”
Nayi murmushi kawai ina sosa tulin packing din gashi na, Can na cire dankwalin na ajiye a gefe, Ina kallon irin mayen kallon da Salman kebin gashi na dashi.
“Yaya Allah ya huci zuciar ki.... Ni na kai matsayin mu debi yan kallo dake? Haba wane mutum.”
Komawa tayi ta zauna tana huci, Na matsa daf da kafafuwan Salman na zauna, A hankali nasa hannu na zaro kafafun sa dake cikin takalmi half covered. Na shiga matsa masa k’afafuwan ina murmushi,
“Sannu da hutawa.. Kasha zaman fada, Kaga yadda suka kumbura kuwa.? My Whole world Allah dai ya baka ladan mulki.. Ya biya bukatu na alkhairi.”
Lumshe idanu yai ya bude su a kai na, Shaheeda tacika tayi fam,
“Salman magana muke, Ka tashi mu karasa maganar sai mu dawo..”
Ahankali yasa hannun sa ya dafe goshin sa dashi,
“Shaheeda.. pls let me be...”
“Toh ai kuwa zan dawo nan sashen naka da zama wallahi. Gwara ka zabi d’aya.”
Shiru yai bai tanka taba, Na guntse dariar data tahomin, Can na tuna da lemon iced drink din dake gaba na, Dauka nayi na dora masa akan hannun sa,
“Sha kasamu coolness your majesty.. Kamata yai a barka ka huta wallahi..”
Ai bansan na janyo ruwa ba, Shaheeda ta shjga surfa min zagi tana neman janye ni daga kusa dashi,
“Allah ya huci zuciyar Yaya... Nifa ba dake nake ba, Idan dake nake ai da kai na nake kenan, Ni dake ne awajen fa Ko kin manta...? Ina maganar jama’a na waje.”
Na karasa fada ina turo bakin shagwaba, Gaba d’aya ina magana ne ina kallon Salman, Yayin da ita kuma tana tsaye kamar muciya tana surfa kwakwazo. Nan kuwa da ita nake.. “
“Washh Allah na... Kai na kwana biyu yaita kaikayi, My whole world tun ranar daka wankemin shi dinnan a bandakin kasa? Bai sake yi ba sai dazu ya dawo. Dan sosamin tsakiyar gashin plss.. Kaji nawan.”
Tamkar soko haka ya zama, Na samu kai na da kwantar da kai na akan cinyar sa duk kuwa da tulin fargabar dake zucia ta. Hannu yasa ahankali ya shiga sosamin kan, Na tsiri lumshe idanu ina mai magana ahankali cike da jan hankali...
“Wasssh Allah na dadi .. Gaskia My whole world zaka zama personal hair stylist dina, Ni da zaka iya dakamin kalabar nan guda biyu irin ta last week..”
Wani dogon saki shaheeda ta saki tana tafa hannuwa, “Lalle Salman shekaru nawa da auren mu kitson kai nama baka kalla amma ace dagayin auren ka har mace kake wankewa kai, kitso da wani susa kamar dan daudu..”
Zaiyi magana nai saurin cewa,
“Nan haka baka sosawa, Kawo hannun kaga cikin nan..”
Ai ban karasa ba, Shaheeda ta janyo hannun sa ya tashi,