← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 114

Sashe 30

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mas'oud ya juya ya kalli Dije wacce itama shi take kallo, hakan kuma ya tayarwa da Shukrah hankali tayi saurin katse su ta hanyar cewa.

“Kaga wasu jakunkuna da nayi order jiya.”

Sai ya waiga ta miko masa wayarta yana kallon jakunkuna, ba karya sunyi kyau, kuma zasu yiwa Oum Waleedah kyau.

“Sunyi kyau sosai kamar na siyawa madam, tana warkewa sai ta rataya a barta ko.?” Ya fada yana kallanta da murmushi.

Turo baki tayi tare da mai da idanuwa ta rufe ba tare da ta ce komai ba, abin da yake sake jan ra'ayinsa akan ta kenan wato yanga.

“Kana nufin Dije zaka siyawa?” Shukrah ta tambayesa cikin mamaki.

“Eh mana na murnar ta tashi lafiya ba.”

“Cab, ai duk an riga an siye su. Jira kawai masu su suke su dauki abubuwan su, sai dai next time.”

Shi ma daman ba wai da gaske yake zai sai mata ba, koda zai siya mata abu baya jin zai sai mata a gurin wanda ta sani bare kuma yar uwarta. Duk iya surutun da Shukrah take yi masa besa shi ya fuskance ta ba, sai rubuce-rubuce da yake ta faman yi tamkar besan abin da take cewa ba. Haka suka yini har Mas'oud d'in ya fito zai tafi tayi saurin biyo bayan shi. Dije na kallon ta fita gabanta ya dinga bugawa, gani take tamkar wani makircin zata ta yi masa, gaba daya bata yadda da Shukrah ba sam. Cikin ranta ta dinga addu'a dan tasan babu mai tsare mata Mas'oud sai Allah, shine ya had'a zukatan su a lokacin da basu sani ba, haka suna fatan ganin Waleed da Waleeda a tsakanin su.

°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°°
*MASARAUTAR BASANNABAS*

Tun a ranar da wannan tsautsayin ya affku ya ke cikin jimami, ko da suka shiga mota yaso ya daure ya tsaya dan yaga abinda zai faru da yarinyar da bafadansa ya rafkawa sanda. Amman ya kasa saboda shi baya san hayaniya, wannan dalilin ne yasa ko kallon gurin be sake yi ba bare asaka ran zai yi wani abu akai. Har suka je gida bai dena ganin jarumta irin ta wannan zakwakurar yar jaridar ba, da take son taji wani abu daga gare shi. Sashensa na musamman ya nufa kowa ya tsaya daga bakin kofa dan wannan ka'ida ne da indai ya shiga cikin wannan dakin to babu wanda yake shiga sai matarsa ko mahaifiyarsa.

Cikin isa da kasaita ta nufo sashen nashi, Bayan jakadiya ta mata iso. dan a kan kunnanta motocinsa suka shigo masarautar, bayin ta suna biye da ita sun sha kaya iri d'aya. Tana zuwa wajan kofar bayin nata suma suka tsaya yayin da ita kuma ta karasa ciki kamar yadda ta taho cikin tinkaho mai nuni da cewar ita d'in matar sarki ce. A zaune ta tarar dashi kansa a kasa ko glasses d'in dake manne a fuskar shi be cire ba. Daman idan da sabo ta saba da duk wasu dabi'unsa, musamman na shariya da kin kallon mutane tamkar wani makaho. Banda wani fitinannan kamshe babu abinda take yi, ta zauna can nesa da shi idanunta a kanshi tace masa.

“Sannu da dawowa, shin me yake faruwa ne naji ko'ina ya dauki zance nama kasa gane abinda yake faruwa. Shin me ya faru da kai?”

Ya yi shiru tamkar tana magana da gunki da aka sassaka da dutse. Taja tsaki a can kasan ranta dan tasan ko mahaifiyarshi ce a nan gurin take tambayarsa ba amsa mata zai yi ba bare ita da taga wajan baccin shi.

“Anyway! Nasan daman ba magana zaka yi. Amman ko da kane ina son ka yi min alama yadda zan fita daga cikin shakkun da nake ciki. Shin kun bige wani ko wata ne a wannan fitar da kuka yi?”

Ashe yaji duk abinda take ta fada, sai gashi ya daga mata kai ba tare da bata lokaci ba. Ta jujjuya idanuwa tare da tabe baki.

“Ance ai ta mutu ma, Allah ya taimaka ba kai zaka sha azumi sittin ba driver ne da ya yi sanadiyyar mutuwar ta. Sai dai kuma kai ne zaka ba da diyya, tunda kasan dai kai za'a sanyawa ido kaji ko?”

Kamar wata uwarsa haka ya kuma daga mata kai alamar 'eh' yaji. Tayi shiru dan tasan ta gama magana dashi ba kuma daga kan zai yi ba. Kusa dashi ta d'an matsa tasa hannu zata zare masa dark shade d'in da ya yi mata shamaki da ganin fuskarshi, ya yi saurin sanya hannu ya rike nata da take shirin cirowa alamar ba ya so. Sai ta kai bakin ta kan hannun nasa tare da sumbatar shi tana cewa.

“Yau ma ba zanga fuskar ka ba ko? Shikenan.”

Mikewa tayi tabar parlorn dan dama zuwa tayi taji tabbas daga bakin shi kuma taji. Abin da kawai za ta yi shine tasan yadda kudin diyyar da za'a kai sun biyo ta hannunta. Shi kuma abin ne ya yi matukar bashi mamaki jin cewar yar jaridar ta mutu. Ya dinga yin hasbunallahu a cikin zuciyar shi, a ranshi yana jin ashe daman mutuwa za ta yi shi yasa Allah ya ba shi iko da damar daga ido ya kalleta? Rabon da ya yi irin kallon nan ya manta, dan ko mahaifiyar sa ba zai iya tuna rabon da ya kalli kwayar idanunta bare ya gane a wane hali take ciki. Abinda ya sani kawai shine muryar ta da kuma yadda take tafiya. Ranar da kyar ya rintsa saboda abin da yaji na cewar badanshi ya kashe wata yar jarida daga yin tambaya. Duk kafafan watsa labarin da ya kunna da daddare labarin ake yi, sai dai su sunyi sabanin abinda yake jiyo wa a bakunan mutane wato.

Yarinyar tana karkashin kulawar likitoci, mutane kuma suna cewa ta mutu rufe maganar ake yi dan kar ace mutanan sarki ne. Sai da safe bayan ya fito fada su waziri suke sanar dashi cewar yarinyar ta farfado kar a damu nan ba da jimawa ba zata koma bakin aikin ta. Be ce komai ba sai da yaji duk wannan firgicin da yake ji duk ya ware baya ji yanzu.

••••
A ranar da Dije ta cika kwanaki biyar a asibiti ne yasa sarki Salman ya kirawo wani amintaccen bafadanshi yace yaje ya binciko asibitin da aka kwantar da wacce aka buga, baya son kowa ya san cewar zai yi wannan binciken saboda idan suka ji hanawa zasu yi, sunfi son su ji ana zagin shi a duniya ana cewa bashi da mutunci. Haka aka yi yaje da daddare har asibitin, wanda ya gano shi ne dalilin binciken da yayi na gidan rediyon da take aiki, yaje can suka sanar dashi, shi yasa besha wahala ba wajan ganowa. Lokacin da yaje ya tarar Mas'oud ya fito Shukrah na biye dashi, bafade ya tambayi nurses d'in dake reciption dakin da aka kwantar da ita.

Daga nurse din da take kula da ita sai Hameedah dake zaune tana danna waya. Dije kwance idanunta akan kofar tana jiran taga shigowar Shukrah sai kawai taga kayan fadawa irin na jikin wanda ya yi sanadiyyar kwanciyar ta a asibitin yanzu haka. Cike da tashin hankali tayi saurin rufe idanuwa da alama yanzu mugun tsoran shi take ji. Sallamar da ya yi ne tasa Hameedah dagowa nurse din kuma amsa masa tana mai tasowa dan jin abinda yake tafe dashi.

“Wani abun ya faru ranka ya dade?” Nurse d'in ta tambaya dan sanin karin bayani.

“Daga masarautar Basannabas ne aka umarce ni da nazo naga halin da yarinyar take ciki.”

Cikin sauri Hameedah ta taso, tsayawa tayi tana kallon bafaden tare da cewa.

“Okay sannu da zuwa, ni Yayar tace.”

“Masha Allah, ko zan samu ganin mahaifin ku dan na kara bashi hakuri akan abinda ya faru, da kuma jinkirin rashin zuwan wani daga cikin masarautar Basannabas ?”

Wayar ta dago ta shiga kiran daddyn su amman sam taki shiga not reachable. Ta sanar masa ta kasa samun wayar shi amman idan yazo zata gaya masa. Ya kuma kallon Dije wace har lokacin bata bude ido ba saboda haushin su da take ji, ya juya ya tafi. Yana tafiya babu jimawa Alhaji Isma'il ya dawo, suka bashi labari ya jinjina kai, kuma sannan haushin su shima da yake je na rashin nuna kulawarsu akan lamarin ya ragu. Gwamna ne kawai da shugaban yan makarantar da suka yi saukar sune kawai suka yi wani abu akan lamarin sai kuma yanzu da sarkin ya yo aiken dubiya, hannu na dukan cinya ba wani ihsani, a matsayin su na wadanda sune silaaa..

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
........🧕🏼

*BINT M H*

*Epi: 16*

________Satin Dije biyu a gadon asibiti tayi shar tamkar ba ta yi wani ciwo ba. Hakika mafi yawancin mutane musamman talakawa suna mutuwa ne ta hanyar rashin kulawa ta musamman. Munsan cewa duk wanda ya mutu lokacin shi ne ya yi. Amman mafi yawa wahala da kuma rashin abinda zaka kula da lafiyar taka yana taka muhimmiyar rayuwa wajan rasa rayuwa kan mu masu tsada. Alhaji Isma'il ya tsaya tsayin daka wajen ganin ta samu sauki kuma alhamdulillahi gashi har an sallame su sun koma gida.
Chapter 30 · 0% Book details