← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 114

Sashe 110

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tak’arasa tana cigaba da rusgar kuka, Hankalin gimbiya asmau yai matukar tashi,

“Fulani! Menene? Eh! Waya saki kuka? Menene kiyi magana mana.”

“Hajjaju! Ta tabbata cikin nan gaskiya ne, Wallahi tsabar tashin hankali ban kare masa kallo ba hajjaju, Baki gansa ba ya girma..”

“Kina nufin kice har ya nuna sosai kenan? Katarar ubancan.”

“Har Salman na matsa mata kafafu, kingan su atare kuwa hajjaju? Wallahi bansan sanda nai gajeriyar suma ba hajjaju. Ina cikin damuwa Hajjaju, Da alama zamana yazo kar..”

“Karki karasa, Uban uban su daga ita har shi Salman din, Banda mahaifin ku ya tsaya akan su, Ai da Aliyu Salman mahaifin sa ma bazai sarautar basannabas ba wallahi. Ciki tamkar yabi iska ne, Dan dole musan abinyi akansa yanzu yanzu kuwa.”

Shaheeda tasake barke wa da kuka tana jujjuya kanta kawai, Idanunta Salman da dije kawai suke tariyo mata, a yadda tagan su dazun nan Salman din na marairaicewa dije.

“Fulani! Ko bakya jina ne?”

“Inaji hajjaju.. Yanzu hajjaju idan zancen ya fito fa? Kinfasan yadda mukai rufa rufar sa shekaru da yawa,.”

“Kassh! Banace ki dena damuwa ba? Yanzun kikasan abubuwa nawa zansa amiki!? Ciki harda binne maganar bazata taba fitowa ba. Ciki kuwa idan kwantar wa ne sai musa a kwantar yabi fatar cikinta.”

“Toh Hajjaju..”

“Yauwa fulani. Kwanta ki bacci da munshari kinji? Karma maganar can tasaki a mawuyacin hali.”

Sallama sukai takashe itama ta katse. SHAHEEDA kuwa Sabon shafin kuka ta bude taitayi tana bori. Can Salman ya kirata a waya, Dakyar ta iya dagawa tana share hawayenta.

“Hello shaheedah..”

“Na’am”
Ta amsa shi tana mai kokarin daidaita muryar ta.

“Ya jikin naki.? Na dawo na tarar bakya dakin, why?”

Shaheeda ta kunduma masa zagi azuciarta tana share hawaye a fili,

“Na wartsake shi yasa..”

“Okay.. Zan zo anjima.”

Kit shaheeda ta katse kiran tana mai wulli da wayar. Tunanin yadda hajjajun su zata bullowa lamarin kawai take, Domin shaheeda irin mutanen nanne masu oya oya. Komai na ta so take ya zama babu matsala. Tana ta zaune, Dake period take, Sai dai ta tashi ta canza pad tadawo ta zauna. Har Salman ya shigo tana can tana tunani.

“Inata sallama kinyi shiru.”

“Banjiba. Barka da dare.”

“Barkan mu.. Ya jikin naki?”

Ya fada yana taba goshinta, Ta goce tana yamutsa fuska, Kunsan tabarmar kunya da hauka ake nadeta, Fashewa tai da kuka tana zubewa a jikin sa.

“Menene.. Jikin ne?”

“A’ahh..! Salman meyasa zaka ci amanata har haka?”

“Amana kuma? Wata amanar taki naci?”

“Yanzu fisabilillahi shekara da shekaru nayi hak’uri na zauna da kai duk tsawon lokacin nan, Nayi nayi muje Habeeb medical center dake Oman a samun cikin nan ka ki... Amman shine a asirce ka ka kai amaryar ka aka dasa mata.. No wonder kuke bobboyewa, Kwana biyu bata gidan ashe da walakin.”

Har tayi ta gama Salman kawai binta yake da kallo, courage dinta na matukar bashi mamaki. Murmushi kawai yayi, Ya kamo hannunta yana murzawa a hankali,

“Shaheedah.. Idan hankali ya ‘bata hankali ne ke nemo shi, Duk wani mumuni baya cire rai ga rahamar ubangiji, Babu wanda abu dake bamai yiwu wa ba fyace Allah ne ya kadarta haka kingane? Dan doctors sunce bazaiyiwu ba shikenan kuma kika dauka bazaiyiwun ba? Uhm? Ina karatun ki”

“Meka dauke ni Salman, Jahila?”

“No ni bance ba, Kawai naga a matsayin ki na mai zurfin ilimi sosai bai kamata kice haka ba.”

Fincike jikin ta tayi daga nasa ta mi’ke tsaye.

“Idan mutanen duniyar nan zaka tara bazan yadda ba, Saboda tsagwaran makirci ne. Ko dai zuwa kukai aka sa mata, Ko kuma zuwa tai ta sa meshi ta wata hanyar, Kai bazaka sani ba domin naga alama an wanke an baka ka kasha. Amman dai tabbas ka kwana da sanin wannan ciki ba naka bane..”

Mikewa yai shima yana kallon cikin idanunta, Ta janye da sauri saboda kwarjinin daya mata.

“Haka kikace ko?”

“Eh haka nace.”

“Shikenan! Mu kwana lapia..”

Ficewa yai batare daya kara bi takanta ba. Ita kuma ta zube awajen tana hawaye. Jakadiya Abu dake labe tana jinsu ta dora hannunta a kirji tana zare idanuwa.

*SAS*

Yana koma sashen sa, Wanka ya shiga yayi a bandaki hade da alwala, Ya zura kayan bacci ya nufi sashen Khadija. Tana baje akan carpet tana cin gyada.

“Zawjatii..”

“Honey bunny.. Ka dawo?”

“Eh na dawo..”

“Ya jikin nata?”

“Taji sauki.”

Gyada kai nayi kawai na cigaba da cin gyadata, Na daga kafafuna na dora akan cinyarsa daya zauna a kusa da ni, Ni kuma kai na yana daga can gefen gado na dora kai na akan tum-tum.

“Dan mammatsamun kafafuna.”

“Okay... Your highness.”

“Yauwa takawa na.. A matsa dakyau.”

Matsamin ya fara yi cikin kwarewa. Yana shafamun heat balm awajen,

“Meye labari..?”

“Hm babyn ka taita kicking dina, Naita cin abinci. Saura kadan fa dazu na rama naushin data mun.”

Zare idanu yai yana daria, Ya saki k’afar ya dawo santar kai na yana d’aga rigata sama, Hannun sa yasa yana shafa cikin, Hade da dora kansa akai

“Little one! Ayi hak’uri a dena dukan Mami, Tace Zata fara ramawa.”

“Mami?”
Na tuntsire da daria, Na mike zaune , Na barshi yanataiwa cikin magana kamar da wani yake.

“Uhm.. Mami da dadi fa. Ko akwai wanda kikeso, Mama, Maama, Ammi, Oumma, Maa, Mommy, Ayii, Ummi.”

“Ai Kowanne yayi dadi har Mamin. Zamu zaba sai babyn tazo.”

“Mace zaki haifa mana love?”

Ya fada yana shafa gashin kai na. Na lura abubuwa mafi soyuwa a jiki na dayake muradin so akwai gashi a gaba gaba. Na dora kai na akan kafadar sa ina shafa kwantaccen sajen sa,

“Inason mace.. Saboda saka mata kaya pink, Da yi mata kitso.”

“Nima inason mace... Mai kama dake sosai. “

“Me kama da kai dai. Sai tafi kyau”

“Wa yagaya miki.. ?Tab! Me kama dake dai Insha Allah. I can’t wait. Allah dai ya saukeki lapia.”

“Aamin! Aamin.”

Dauka ta yai gaba d’aya ya dire akan gado, Yasa hannu ya kashe fitila. Yana mai janyo bargo ya rufe mu, Daga nan wasan ya canza aka shiga fagen daga sosai....

<><>>>>>>>>>>>>>>>. <><><><><>>>>>>>>>

*SASHEN JALEELAH*

Jakadiya Abu dakyar tayi bacci saboda maganganun Salman da shaheeda data jiyo akan cikin da dije ke dauke dashi, Gari na haske tatafi sashen Mama Jaleelah don sanar da ita labarin cikin. Tunda itace d’iyar waziri.

Mama Jaleelah na hakimce akan kujera gama cin abincin ta kenan tana hutawa, Da alamun bacci ne yakeson d’aukar ta duba da yadda take lumshe idanu ahankali tana bud’e su. Jakadiya Abu tashiga bayan anmata Iso, Tana zama tafara haki saboda da tazara tsakanin sashen hadimai dana matan gidan.

“Hakkin me kike Abu? Gudu kikayi ko kuwa wani ne ya biyo ki nan din.? Laifi ki kai ko menene? Kinzo sai numfarfashi kike, Tashi ki bani waje in babu abinda ya kawo ki.”

“Tuba nake ranki ya dade, Allah yakara miki lapia da nisan kwana. Wallahi daren jia ban runtsa ba shi yasa ka.”

“Bakida lapia ne?”

“Kalau nake ranki shi dad’e... Furgici ne kawai da tsantsar tashin hankali dana shiga.”

“Ina ji..”

“Tun kwanakin baya nake wani bincike, Toh Allah da ikon sa sai daren jia sakamakon binciken ya fito..”

Mama Jaleelah ta mike daga kishingid’en da take ta zauna tana duban jakadiya.

“Ke na fara sanarwa, Domin abunda ya shafe kine ya kum...”

“Jeki ga ainihin zancen.”

Jakadiya ta saki nannauyar ajiyar zucia kafin cikin tabbatarwa tace,

“Gimbiya Khadija.. Na dauke da juna biyu.. Har ya girma.”

Mama Jaleelah ta mike saboda jinta da ganinta daya dauke na yan Wasu dakikai.

“Maimata abinda kika ce...”

“Gimbiya Khadija na dauke da juna biyu.”

Ai Jaleelah bata jira karashen zancen jakadiya ba tashige cikin dakin ta, Jikin ta sai kakkarwa yake. Waziri (mahaifinta) ta kira ta fada masa komai. Alokacin Waziri kuma ya gama shiryawa zashi fada. Da sauri ya koma ya shige cikin dakinsa ya rufe tare da tuge rawanin kansa ya yi cilli dashi, banda cije baki da bubbuga hannu a kanshi babu abinda yake yi. Uban gumin da yake tsatsowa daga jikinsa sai ka rantse da Allah daga wanka ya fito tsabar digar da gumin keyi. Zagaye kawai yake a cikin dakin zuciyar shi cike da matukar mamaki jin cewar amaryar sarki Salman tana dauke da juna biyu.

Ta ya ya mace zata samu ciki bayan an tabbatar da cewar mijin ba zai taba haihuwa ba? Karya ne wallahi dole akwai wata kullalliya da Salman ya shirya yi a cikin masarautar nan, shi yasa yaje ya auro wacce ba jinin sarauta ba. Yar talakawa da bata da arzikin komai sai bin gidajen yan uwa.

Karar wayarsa ce ta katse masa tunanin da yake yi, ya lalubi cikin aljihunsa ya ciro yana dubawa. 'Mai martaba' ya gani baro-baro ransa ya yi mugun baci ya mai da wayar cikin aljihunsa. Ba zai dauka ba domin yanzu jin tsanar Salman yake yi a fili ba wai a zuciyarsa kadai ba. Ya tsane shi tsana mafi muni da babu wani dan Adam da ya taba tsana kwatankwacin wannan.

“Sai na illataka Salmanu, sai na nuna maka baka da wayo bare kuma dabara. Bana sonka bana kaunarka, ko mahaifinka na zauna dashi ne kawai ba dan ina kaunarsa ba bare kuma kai da aka haifeka a gabana. Ni zaka munafinta ka nuna min cewa ni ne abokin sirrinka? Ni zaka mayar sauna wanda besan abinda yake yi ba Salmanu? Kayi kadan wallahi, ba a haifeka ba ballantana kace zaka fini dabaru. Muje zuwa zan nuna maka koni waye Salmanu, wannan cikin ba a isa a raina mana hankali akan shi ba, Sai kun fadi yadda akai kuka samo shi munafukan banza munafukan wofi.”

Cewar waziri da yama rasa abinda zai yi saboda tsabar damuwa da shiga tashin hankali. Domin rashin haihuwar sa da shi zasuyi amfani wajen tsige rawanin sa, Wani kiran ne ya kuma shigowa, cikin masifa da zage-zage ya ciro wayar da niyar kashewa ya yi zaton Salman d'in ne sai kuma ya kara ganin sunan Jaleela, ya dauka a fusace yana cewa.

“Menene kuma, Zaki bi ki dameni?” Cikin damuwa Jaleela tace.
Chapter 110 · 0% Book details