← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 114

Sashe 53

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta kama hannu na sannan muka tafi, bayan ta nuna min bandakin tace na shiga. A bakin kofar an rubuta addu'ar shiga, hakan yasa na yi nima dan a can gidan da na baro ko niyar yi nazo yi sai naji an goge min na kasa yi sai dai na shiga a haka. Wanka nayi sosai, daga nan nayo alwala nayi addu'ar fitowa wacce itama ga ta an sakale a saman kofar. Bayan na fito ne naga ta ajiye min komai sabo sai dai banda bra, na dan kalleta nace ta bani pad idan akwai, ta tashi ta dakko min leda guda na dauka tare da komawa bathroom d'in nasa na kuma fitowa. Mayuka masu kyau ta bani na shafa nasa wandon baccin na tsaya ina faman raba ido, bana iya kwanciya sai da half vest koma bra d'in, kamar ta gane ta juyo ta kalle ni tana murmushi tace.

“Haba ranki ya dade, ko a baya kina bacci da bra yanzu kam ya kamata ki aje su a gefe. Kisa rigar kawai an fi son a dinga kwana a haka inji likitoci.”

Ban iya musa mata ba, haka nasa rigar da hula ta nuna min gado tace na kwanta. Nan fa ta fara bani labarai, gaskiya wayayyiya ce adda Maryama, dan a daran sai da tasa na saki jiki da ita muka shiga hira kamar daman mun dade da sanin juna. Gwaggo ta Fada ta aiko aka kawo min wani ruwa, tace nasha sannan kuma na shafe a jiki na. Nayi kamar yadda tace daga nan kuwa muka ci gaba, sai da dare da yi sosai sannan muka yi bacci. Ba karamin dadi naji ba ranar, kuma ban tsorata ba lafiya lau nayi bacci na tashi.

____Washe gari da safe bayan nayi wanka na shirya cikin doguwar riga, Adda Maryama da yaran ta suka gaishe ni na amsa fuska ta cike da walwala. Daga nan aka kawo breakfast kala-kala, muka ci da yake tana business hakan yasa aka dinga kiranta a waya, tace min bari taje ta dawo. Gwaggo ta kira ni naje na zauna kusa da ita, itama tun ina jin nauyin ta har dai daga baya na saki jiki muna ta hira tace.

“Kamar yadda na gaya miki dole sai kin tashi tsaye kin nemi kariya sannan zaki ji dad'in yin rayuwa. Na yi matukar mamaki lokacin da naji zancen auran ku saboda duk mun san shi ba mutum bane ma'abocin kalle-kalle, babu yadda ba'a yi dashi ba wajan kawo wacce yake so amman yaki, dole sai da aka hada auran shi da Shaheedah. Abin da ya kuma bani mamaki be wuce yadda ya auro ki ba, bayan yasan tsarin mulkin masarautar nan ba a auro bare dole sai jinin sarauta. Tun da naji ya yi aure kuma a boye har sai a ranar daurin aure sannan ya fada, na san lallai ba karamin so yake yi miki ba.”

Na tabe baki yadda ba zata gani ba, bata san auran manufa ya yi dani ba shi yasa har take zaton soyayya ce. Ni nasan mutumin nan auro ni ya yi dan ya kuma wulakantani tunda gashi nan an kai ni gidan be kula ni ba har na baro gidan saboda shi bashi da mutunci. Gwaggo ta ci gaba da cewa.

“Kin ganni nan? Da a cikin masarautar nake, amman dalilai suka sa dole na baro ta saboda bana son fitina. Bari na baki tarihin masarautar Basannabas, ki gyara zama ki kuma karkade kunnanki.”

Gyara zama nayi dan dama ina son abinda zai kuma dauke min tunani. Gwaggo ta fara da cewa.....

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
*ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). *

*KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASA*

*29....*

_*KIBIYAR AJALI.....!_*
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🏹🥰😍

_*WAIWAYE:-*_

_*MASARAUTAR BASANNABAS*_

Tarihi irin na kunne ya girmi kaka d'in nan, ya yi nuni da cewa, Masarautar Basannabas wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru da suka gabata, Wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci. Sunan Basannabas din ya samo asali ne tun a shekarun baya. Tarihi ya nuna cewa wasu tsatson fulani biyu ne da akewa laqabi da *Bassan da Nabas* suka zo daga gabas maso yamma inda suka yada zango a nan suda matayen su da ‘ya'yan su da shanun su. Anan suka kafa dandalin kasuwancin su, Ma tafiya dake wucewa ta nan suka kwadaitu da yanayin kasuwancin su, Allah ya sanya musu albarka kwarai da gaske. Duk fatake na nesa da na kusa su na zuwa su sari kaya a wajen su. Sosai yankin ya shahara, har ya zamto mutane na yiwa yankin laqabi da garin *Basan da Nabas*. Shekaru aru-aru haka ake kiran sa, Kafin yankin ya zamo sananne, har zuwa lokacin da turawan mulkin mallaka suka bawa nijeriya 'yancin ta. Bayan nijeriya ta cire garuruwa ta sanya musu suna. A lokacin ne aka yiwa yankin *Basan da Nabas* kwaskwarima ya dawo *Basannabas....*

*MASARAUTAR BASANNABAS*
👑

Tana d’aya daga cikin k’asaitattun masarautu da ta keji da kambun mulki, masarauta ce wadda ta kafu tun misalin 998 mailadiyya, Ma’ana dai fiye da shekaru dubu. Sarauta da hakimci a masarautar Basannabas ta kasance wani babban al’amari wanda yake da muhimmanci. Sarautar Basannabas ta kasance a hannayen ahalin rukunin sarakuna tsatso (jini) d’aya. Tun daga kan Marigayi mai martaba na da wato sarki Durbin jingau. Masarautar Basannabas nada sarki d’aya tak na yanka/Gado, Ba taka haye bace, Sannan akwai hakimai masu lakabin sarautun gargagiya a matsayin mataimakan sarki awajen gudanar da kambun mulki.

Gaba d’aya rukunun sarakunun garin Basannabas a tsatson jini d’aya yake, Wato dai tsatson yan uwa guda uku, Marigayi Sarki Durbin Jingau, Da tsatson marigayi Sarki Masekiri (Tajiri) Jirgau, Da Marigayi Sarki Ilyasu Jirgau. Gaba d’aya ahalin su ne ke mulkar birnin Basannabas.. Tun daga kan sarki Masekari Tajiri 1559 zuwa 1669. Har zuwa sarki Ismaili Rabo 1701 zuwa 1804.

Daga nan sarauta ta koma hannun iyalan Dallatu na lokacin wato tsatson marigayi Ilyasu Durbi a shekarun baya. Bayan rasuwar Sarki Ilyasu, Sarautar Basannabas ta fada hannayen tsatson marigayi Durbin Jirgau, Dana Marigayi Masekiri Jirgau, Kafin daga bisani ta sake dawowa hannun jikokin Sarki Ilyasu, Dake Allah yayi sarautar a hannun su zata zama. B’angare da dama sun ‘ki hakan, Daman duk inda gidan sarauta yake dama dole a samu haka. Akwai suka, Tsagwaron makirci da sihiri babu wanda ba’ai ma sa ba, Da k’yar da karfin addu’a dai, Sarauta ta dawo hannun mai Martaba Sarki Aliyu salmanu Aliyu, Wato jikan-jikan Sarki Ilyasu.

_*MAI MARTABA SARKI ALIYU SALMANU ALIYU*_
(Mahaifin SAS)

Sarkin Basannabas mai martaba Aliyu salmanu Aliyu ya gaji mulki ne daga hannun mahaifin sa marigayi sarki salmanu ibrahim ibrahim. Sarki Aliyu salmanu ya kasance kasaitaccen sarki wanda ya gina sarautar Basannabas ta hanyoyi daban daban. Babu na biyun sa a bangaren tsarin sarauta. A tsari da kuma tarihin sarautar Basannabas a wancen lokacin, Bayan an dora sabon sarki a karagar mulki, Ko kuma ana shirye shiryen dora shi akan mulki, Wajibi ne ko ince al’ada ce, Dole sai sabon sarki ya auri mataye har biyu daga tsatson sarauta. Kuma su zamto na farko acikin matayen nasa, Kafin daga bisani ya auro biyu wa’enda yake so daga baya, Kana ya iya ‘karawa da ‘kwarkwarori (concubines). Wanda suma ake samo masa daga jerin ‘yayan dagatai ko kuma ‘yayan fadawan zaman fada wato ‘yan majalisar sarki. Idan kuma ya kasance yana da mata wanda daga cikin tsatson sarautar Basannabas ne, to shikenan ba sai ya kara ba, Idan kuwa ba jinin sarauta bane, To fa lallai dayan biyu ne, Ko dai ya sake su ya musanya da jinin sarauta, Ko kuma yayi murabus daga karagar mulki, Kana a cire shi daga duk wasu al’amura na masarauta.

Bayan nadin Sarki Aliyu salmanu a lokacin, Abubuwa da dama sun faru a masarautar domin sosai aka samu ruguntsumi na rabuwar kawuna, Babban dalilin dayasa hakan kefaruwa da Sarki Aliyu, saboda matar da zai aura, Domin ya kafe akan shifa a lalle dole ya zamto ya auri wadda yakeso tun tasowar sa, Wato y’ar daya daga cikin bayin masarautar, Wato yar sarkin ‘kofar kudu, An kad’a an raya amma sam sarki Aliyu ya kafe akan kudurin sa na auren, A lokacin babu wanda ya tsaya masa sai dan aminin baban sa. Wato mai martaba sarkin *Masarautar Bullo*, Sarki Ibrahim Hashimu. Wanda ya gaji sarautar ta bangaren kakan baban sa.

Gashi Bullo itace masarauta ta biyu dake bin bayan Masarautar Basannabas. A duk fadin nijeriya itace masarauta ta biyu da ake ji da ita a kasar nan. A lokacin sarkin Bullo ya tsayawa sarki Aliyu domin cinma wani burin sa na daban, Bai dai bayyana ba alokacin. yabar wa zuciar sa ajiya. Ya tsaya tsayin daka wajen ganin Sarki Aliyu ya karb’i karagar mulki. Duk wani shige da fice yayi, Yayi amfani da karfin mulkin sa, Da kuma ta fada aji na mulkin farar hula (democracy). Dan a lokacin y’ar wajen sa tana auren shugaban kasa na lokacin.
Chapter 53 · 0% Book details