Sashe 23
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itama Mami sai ta saki bakin tana rike habarta idanunta a kai na take cewa.
“Dije ai wannan ba daki bane, cikin nan inda muke shine daki. Nan da suka nuna miki toilet ne da ake bayan gida ko wanka, ki dena damuwa a hankali zaki fahimci komai, yanzu dai ki taimaka ki shiga kiyi wankan duk yadda kika ga dama.”
Na sake komawa ciki na tsaya ina kallon yadda aka kawata shi, ni da naga na malama Mardiyya ina ganin shi aljannar duniya, ashe ga aljanna na ban sani ba. Na duba naga sam babu bokiti a bandakin kuma bana son kuma yin abinda zasu min dariya sai kawai na cire kaya na dauki wani kofi da na gani sai na dinga dibar ruwan da Hameedah ta tara cikin kwami ina tsaye ina wanka na. Abin da ya sake daure min kai a ciki shine, da na waiga sai naga kai na a cikin madubi na hango kumfa a inda hannu na baya kai wa sai nasa ruwa na watsa a gurin, na kuma matsawa wajan madubi ina duddubawa ko akwai inda bai fita ba. Ashe amfanin shi kenan a ciki, ikon Allah gaskiya yan gayu komai nasu daban yake. Ina gamawa na saka skirt dina tare da jansa sama wato har kirjina sannan na fito sai faman muzurai nake kamar bani da gaskiya.
“OH my God Dije, maimakon ki dauro towel kawai sai ki sako skirt ɗin da kika cire.”
Shukra ta yi maganar tana yatsina fuska da murmushi a fuskarta.
“Ai ban ganhi Au ban ganshi ba.”
“Kai! Ohh Dijeh, daman har yanzu ana hi da hah a duniyar nan?”
“An dena walle.” Ta kuma sakin wata dariyar.
“Kin kuma ai Dije, mu bar wannan maganar kawai zo ki shafa mai kisa kaya muci abinci.”
Na amsa mata sannan duk suka fita ni kuma na janyo jakar kayana da Jummai da shigo min dasu, na ciro basilin dina na shafa sannan na ciro riga da zani nasa tare da zauniya a kasa na zabga tagumi ina tunanin yadda rayuwa ta zata kasance a cikin wannan gidan.
“Dije ki fito muci abinci ma, kin zauna anan kina ta tunani?” Hameedah ta leko tana min maganar.
Na tashi nabi bayan ta muka nufi dining da gurin kansa abin kallo ne bare kuma yadda aka kawata kan table d'in da abincika kala-kala. Kamar yadda naga sun zauna haka nima naje na zauna ina ta raba ido.
“Dije maimakon ki sako kaya mararsa nauyi shine kika jibgo wata atamfa?”
Nayi murmushi kawai ban ce komai ba saboda ko tace naje na saka mararsa nauyin to bani dasu dan haka shiru kawai shine a wajan. Shukarah ta fara zubawa kowa wanda yace yana so, ni kuwa daman bama sanin abubuwan nayi ba bare nima fadi nawa ra'ayin, koda aka tambaye ni ma cewa nayi a bani koma menene zance dan ni babu abinda bazan iya ci ba indai naci din ne. Ai kuwa ta zuba min farfesu na naman kaji da ya sha kayan kamshi na lashi lebe na sama da kasa yo yaushe rabon da a hadu? Ta miko min harda sako min wani cokali mai yatsu na kuwa cire na ajiye shi a gefe na zura hannu ina dakko tsokar kazar nama ina dannawa cikin bakina.
Ana ta hira amman ni sam bana sauraron su nama na kawai nake ci ina korawa da lemon kwakwa mai dan karan sanyi da yasha madara har wani gardi-gardi yake yi alkuran. Haka muka gama ci kowa ya yi harkar gabansa, ni kuma tunda na samu tv na zauna ina ta kallo shirye-shiryen su yana dada bani sha'awa da kara karfafin gwiwa wajan son yin aikin jarida.
Sallah ce kawai take iya tayar dani daga gaban talabijin d'in nan. Koda nayi sallah isha'i dawowa nayi naci gaba da yin kallon, su kuma mutanan gidan kowa ya tafi yin harkar gabansa, a nan bacci ya dauke ni, koda uncle Isma'eel ya dawo anan ya ganni ina ta bacci kan kafet nayi rashe-rashe tamkar wacce tasha abin maye. Kawu yace a mai dani daki kan gado, Jummai tazo ta dinga tashi na amman ina naki tashi saboda wani irin nauyin bacci da Allah ya sakko min a ranar. Haka Mami da kanta tayi ta tashi na nan ma shiru sai kyale ni suka yi sai da uncle ya gama cin abinci ya tashi da kanshi ya dauke ni ya kai har kan gadon Shukarah yace mu kwanta kafin nima a siyo min nawa.
Muna bacci na dinga yarbawa Shukrah kafafuwa na a jikinta, tun tana min kawaici har ya zamana ta dawo tana duka na wanda ban san tana yi bama saboda tsabar bacci dana’urar sanyi abinka da basabin ba, Da asuba take bamu labari, kuma ni dama ba gwanar iya ba da hakuri bace tun ina karama ballanta kuma da na fara girma.
“Wai Dije ba zaki ban hakuri ba.?”
Na kalleta da mamakin jin abinda take fada, sai kuma na shiga yatsina fuska alamar bafa zan bada ba.
“Dije tazo inji Mami a kasa.”
Cewar mai yiwa su Hameedah gyaran daki da wasu aiyukan da suka shafe su wato Lamtana. Na tashi da sauri nabi bayanta dan ba hakurin nan zan bayar ba komai zata yi min. A zazzaune na tarar dasu, na duka har kasa duk na gaishe da su sannan cikin murna da murmushi kawun nawa yace dani.
“Dije ki saki jikin ki a cikin gidan nan saboda kema ya ta ce kamar yadda suke ya ya na babu banbanci. Duk abin da kike so ki gaya min ko Mami ga ta nan a zaune, uwa ce a gareki ina son ki bi umarninta kamar yadda su Hameedah suke yi mata. Sannan insha Allahu zan samar miki makaranta ki ci kaba tunda kin kammala secondary, me kike son ki karanta ne Dijeh? Dan kar naje na yi miki shisshigi cikin rayuwarki.”
Na dinga soshe soshe saboda wata kunya da nauyin sa da suka kama ni a lokacin, ina murza idanuwa nace.
“Kawu ni dai ina son naga nayi aikin jarida.”
Yace.
“A'ah a'ah a'ah! Kice zamu samu mai jiyo kwakwafa a duniya kenan? Masha Allah Dije, toh Allah ya tabbatar da alkairi insha Allahu zan yi kokarin ganin kin cika burinki na rayuwa. Tashi kije Allah ya taimaka.”
“Amin kawu na gode.”
“Yauwa bana son wannan kawun da kike kirana dashi, ki kirani da sunan da kikaji mutanan gidan nan suna kira na wato daddy..”
Nayi dariya ina rufe fuska da tafukan hannayena tare da tashi na tafi, na tsani hawa bene saboda tsoronsa nake ji, duk sanda zan hau ji nake kamar za'a turo ni na gangaro ko nayi baya idan ina hawa.
Har na kusa gama hayewa sai kuma na dawo na sakko, na koma parlor sai na tarar basa nan. Fitowa nayi dan har ga Allah bana son zama guri d'aya dan bahaushe yace zama guri d'aya tsautsayi ne. Lamtana na gani zata shiga mota, da sauri naje na tambaye ina zata je, tace cefane zata yo, na hade hannuwa ina rokonka akan dan Allah ta tafi dani na raka ta, aikuwa tace to na shiga muka tafi ina ta sake ganin birni da suke abubuwan su cike da burgewa. Ina biye da ita har ta kammala siyayyar muka dawo mota driver ya dawo damu.
A farfajiyar gidan muna shiga da mota na hango matar Kawu Isma'il wato Hajia Abeedah (Mami) da kawarta suna zaune akan fararen kujerun dake zagaye da yar balcony’ din farfajiyar.
“‘Mami mun wuni k’alau, Ina yini Hajia?”
Na gaishe da Mami da kawarta cikin ladabi, Mami ta amsa da fara’a, Kawar kuma ta debe ni ta watsar, Mik’ewa nayi na shige ciki abuna. Ina shigewa nabi kofar dana rufe da kallo ina harararta tamkar ita taki amsa min gaisuwar.
“Abeedah! Wacece wannan? Karki cemin sabuwar mai aiki kika dauka haka? Bakya tsoron abunda zaije ya dawo?”
“Hmm! Hajia ba yar aiki bace. D’iyar mai gidan nan ce, Yar kanwar suce data rasu shekarun baya.”
“Ayyo to! Ai kuwa tamkar ita tayi kanta. Tab ni fa bana son rikon ya'yan yan uwa n miji, Akwai su da kisisina ga shiga tsakanin ka da mijin ka.”
“Anya kuwa? Wannan fa yar kauyen kayau ce fitik. Kawai dai dan tana da zubin manyan mata ne, Ga kyau tamkar ita ta kera kanta. Ai babanta ance bafulata ni ne, Shima bai jima da rasuwa ba.”
“Allah sarki! To amman dai kiyi takatsan tsan.”
“Insha Allahu!”
Dakin mu na shige ina mai yage hijabin jiki na, Ya Shukrah ce kawai a ciki Ya Hameedah bata nan.
“Assalamu Alaikum!..”
“Wa’alykm Salam Oganniya Dije!”
Na murtuke fuska ina gatsine baki,
“Ya Hameeda an tsine wannan sunan fa...”
“Inji wa? Karya kike bayan ke kika bamu labarin? Aina aka tsine? Jia ko shekarn jia?”
Na sheke da dariya ina kallon kai na a mudubin su mai tsaho, Zaka iya ganin kanka gaba ki dayan ka a tsaye.
“Sunana Nana Khadija.. Ko Ummi na yadda Baffa na ke gayamin sanda yana raye.”
Ya Hameeda tayi murmushi kawai tana gyad’a kai, Bandaki na shige nayo wanka sosai, Kafin na sauya kayan jiki na zuwa doguwar riga marar nauyi, irin tsarabar makkan nan. Jefi jefi mukan taba hira da Ya Hameeda har Kawu ya dawo yace akirawo mu duka,
“Kawu Sannu da zuwa..”
“Yauwa yar kawu duk da dai nace bana son ana ce min haka! Ba dai matsala ko?”
“Babu Kawu!”
“Yauwa munyi magana da wani Professor anan jamiar da zaki fara, Yace suna shirye shiryen ranar da zasu sanya ku fara lectures, Saboda haka kafin sannan nidai na yanko miki form a center din da su Hameeda suka koyo British English, Saboda ki sake wayewa da ilimin sa. Ai h..”
“Alhaji Wai British eng learning centre dai?”
“Ita! Meya faru?”
“Uhm! Alhaji gani nai tayi tsada, Haj Luba ma kasa sa yarta tayi.”