← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 114

Sashe 108

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigewa tai cikin gida aguje ta shiga kiran wayar mahaifiyar ta, Ta gaya mata komai ,

“Kwantar da hankalin ki shaheeda ki dena kuka dan ALLAH.. Ba dai ciki kike tsammani ba? To bazashi ko Ina ba, Yana sa akaiwa Gimbiya Rahama matar baban ku ehe?”

Cikin kuka shaheedah tace,

“Iska kika sa aka turawa cikin.”

“Ta haife me? Fadi da k’arfi..”

“Ta haifi katangare.”

“Toh Karki wani damu, Yadda zancen cikin rahama yazama sai tarihi haka na waccen shegiyar ma zai zama, Ba zama zamuyi ba, Ki tabbatar da tudin sa, Watan sa, Nauyin sa idan zai yiwu, Ta hakane zansa a cinna wa shegiya katangare dai dai girman cikin ta.”

Jin haka shaheedah ta fa’da’da murmushin ta,

“Sai Hajjaju..”

“Toro babba nake, Gimbiyar sarki Ibrahim Hashimu, Fadawa duniya kice kwarai mahaifiyar ki ce.”

“Allah yabar mun ke hajjaju..”

“Kedai bar kuka kawai Kinji? Sai komai ya lafa zamu koma K’asar nan a dasa miki cikin kuma dole ki haife dan uban uban Salman din, Bai isa ya kawo gaddama ba. Amma kafin sannan ki shiru da bakin ki, Kada ki bari kowa yaji kinji.. Kinsan babu wanda yasan hakikanin gaskiyar komai.. Kije sashen Salman din ko natan kan ki tsaye.. Ki gano mun dagaske cikin ne ko kuwa? Kinsan fa yan kauye Idan suka samu birni ta murjesu wallahi baka gane su.”

“Gaskia kam hajjaju.. Toh zan duba da kai na kuwa zanje har sashen nasa.”

“Yauwa, Kiyi suman karya, Kiyi bori ki nuna yaci amanar ki, Sai dai idan dasa mata kai. Kita bori a sashen nasa kinji?”

“Toh hajjaju.. Zan gaya miki yadda akai..”

“Yauwa.. Sai da safe, mai martaba na mun iso.”

Sallama sukayi, Shaheedah ta malale akan gado tana kyalkyala dariyar farin ciki.. Ranta fes. Gani take tunda hajian su ta tsaya mata batada wani sauran shakku.....

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B31_

*GIM. KHADEEJAH*

Hidimar bikin su Ya shukrah muka shiga, Duk da dai ba zuwa nake yawon kasuwa da suke ba, Ina gidah abuna. Biki saura kwanaki biyu na koma gidan Kawu daddy, Na shiga cikin dangi akaita warkajamin biki da ni, Biki yayi kyau kwarai matuka, Kwanaki 3 akai anayi, Addah maryama sunzo dasu Umma Hansatu suma. Salman ma yabawa Kawu daddy tasa gudunmuwar duk kuwa da dakyar Kawu daddyn ya k’arba don shima dai dai gwargwado yanada nasa rufin asirin, Ni kuma tawa gudunmuwar Mami na bawa.

Anci biki an darje, Amare kowacce an kaita gidan ta, Kai Ya hameeda ne banje ba can jos, Kawu daddy yace naje mata ziyara amman bayanzu ba, Ya shukrah kuma gidan ta ma ba nisa dana Kawu daddy domin unguwa d’aya ne, Sai dai layi ne ya banbambata. Wayyo yan uwa da dadi suke, Gaba da baya dik inda na juya sune, Anyi zumunci, Munsha hotuna sosai, Biki ya kare Kowanne ya koma inda ya fito, Anaiwa amare da angwaye fatan zama lapia da zuriya ta gari.

Shaheeda kuwa sau wajen biyar tana zuwa sashen Salman amman bata haduwa da Khadija, Dik iya zurfin bincikenta bata gano hakikanin inda dijen take ba. Salman kuwa wani lokacin har guduwa yake ya barta saboda yadda take manne masa domin shi tsoro take bashi musanman ranar daya gama kallon cctv recording din bangarenta baki d’aya.

***** A hankali ta karasa ta murda kofar parloun cikin shiga wacce take fatan wanda ta yiwa ya karba ya yaba da hannu dubu ba biyu ba. Ko babu komai tasan ita d'in mai aji ce, ban da zuwan Dije cikin rayuwar su shi kansa salman yasan Shaheedah akwai isa da takama har a kan kin kansa. Kicibus suka yi da Dr Fiddau zata fito, ganinta yasa Shaheedah zaro ido dan tasan ba lafiya ba indai aga ganta ansan wani ne babu lafiya tazo dubawa.

Baya tayi tana umartar Dr. da ta fito, bayan ta fito ne tace ta rufe kofar ta rufe duk bata kawo komai ba cikin zuciyarta sai da taji Shaheedah na tambayar.

“Ya akai Dr. na ganki anan?”

Cikin dakiya Dr Fiddau tace.

“Lafiya lau Gimbiyar mu, mai martaba ne ya kira ni.”

“Jikin nashi ne ya motsa ko me?”

“Allah ya taimaki Gimbiyar mu ya kara mata hakuri da juriya, daman yace idan na fito nace a sanar dake yana son ganinki.”

Dr ta samu kanta da kwakuso karya, Saboda babu irin gargadin da Salman be yi mata ba akan karta sake ta gayawa kowa cewa Dije na da juna biyu, idan har yaji maganar ta fito kuma daga bakin ta ne to ya yi alkawarin sai ya koreta a jihar shi gaba daya. Yanzu Babban tashin hankalinta shine, Salman ta baro shi tare da Dije a daki, kuma tasan dole ne Shaheedah ta gansu, gashi yar kamar t-shirt ce a jikin Dijen ana ganin bullowar cikin jikin ta.

“Alright! Daman ina son nazo na duba shi bari na shiga thank you Dr.”

Gabaki daya rasa yadda Dr za tayi akan ta tsayar da Shaheedah daga shiga cikin dakin tayi. Tasan bata isa ba kuma Shaheedah mutum ce wacce bawanta be isa ya sata tayi abu ba indai na kashin kanta ne. Tayi saurin dakko waya tana kiran Salman amman be dauka ba saboda Dije na can na yi masa raki, daga tace bayanta sai tace hannu ko kafa haka yake bin duk inda ta fada yana matsa mata, yana jin kiran wayar a kan bedside amman ya kasa zuwa ya dauka saboda da ya dan tsaya zata ce 'wash Allah'.

Babu ko sallama a haka Shaheedah ta murda kofar bedroom d'in tana lumshe ido jiyo kamshin turaransa da tayi. Sai dai kuma me, hango Salman tayi durkushe a gaban gado yana yiwa Dije tausa. Da yake baya ya bawa kofar sai ya zamana be san waye ba duk a tunaninsa ma Dr ce ta dawo, amman yadda yaga Dije tayi wata irin zabura ta juyo shine yasa shi saurin mikewa yana kallon kofar. Shi kansa Salman din da yaga Shaheedah a wannan lokacin sai da kirjinsa ya buga, saboda itace mutum ta farko a duniyar nan da baya son tasan Dije na da ciki saboda yadda yagani a na’urar dake dakko masa sirri dan yasan ba zata taba yadda ba duk kuwa da duk wata qullaliyar rashin haihuwar sa daga gare ta ne.

Baki bude take kallon su, Dije na kokarin janyo blanket ta rufe jikinta, sai dai abinda suke gudu shine ya kasan ce wato ganin cikin. Shaheedah ta dago kafa a hankali tare da rufe kofar ta jingina bayanta a jiki saboda yadda kirjinta yake bugawa da karfin gaske. Fatan ta da burin ta yasa ba abinda take zargi bane a idanunta. Salman ya kirkiro murmushi wanda iyakarsa saman lebansa yana tahowa gurin Shaheedar.

“Gimbiya irin wannan shigowa babu excuse?”

Ya yi maganar yana kokarin dafo kafadar ta, Ya ma manta when last ya kirata da gimbiya. tayi saurin dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, bugun zuciyarta yana daduwa tasa hannu ta dafe goshi tare da cewa.

“Salman amanata kake ci? Salman kai ne tare da wannan banzar matar akan gadon mu na mulki? Wait! Wannan toliyar ta cikin ta na meye?”

Komawa ya yi ya zama Salman d'in shi jin ta ambato cikin Dijen wacce ta rufe jiki da blanket ta tsaya tana kallon su. Shi kuma Salman ya tsuke fuska yana cewa.

“Ke baki da toliyar a cikin ki Shaheedah?”

“Kai kanka kasan cewa bani da tunbi, kuma itama ba shine da ita ba ballantana kace min shine.”

Haushi ya fara ciki Salman dan yaga alamar so take ta kaishi makura, gashi yama rasa abinda zai ce mata sai faman cizon lips da yake yi. Ni kuwa sakkowa nayi daga kan gadon har blanket d'in ban kallesu ba na nufi hanyar fita ta kuma danne kofar da bayanta, gashi bana son nace zan bi ta dayar kofar saboda babu wanda yasan da ita sai ni da Salman kadai.

Cikin Bazata kawai muka ga ta finciko blanket d'in ta tsaya tana kare min kallo cikin rawar jiki. Ta tabbata cikin ne da Khadija? Shin k’oshi ne ko kuwa? Idanunta ne? Kallonta ta mayar kan Salman baki na kyarma ta ce.

“Salman!!! CIKI?”

Haushi da takaicin ta suka taso min, dama ni ba hakuri ba bare nace in an min zan kyale, na ja tsaki tare da cewa.

“Eh ciki ne haramun ne dan nayi shi a yanzu? Ko kuwa kin dauka cewa dan kin kasa dauka uban Kowa ma ba zai dauka ba? Kinyi kuskure da kike tunanin cewa ni gunki ce ba zan Iya bukatar namiji a kusa dani ba. Namijin ma kuma tsadadden mijinki wanda yasan takan soyayya irin Salman...”

Jiri ne ya shiga kwasar shaheedah, Daman anata kawo mata tabbacin cikin ne, Bata taba yarda ba sai yau data ganewa idanun ta. Ta runtse idanunta dakyar ta budesu cikin tsantsar bakin ciki, Domin tuni wani abu ya taso ya tokare mata a wuya. Duk da son tayi borin karya hakan yaci tura, Domin wani ‘daci ne taji yana taso mata tundaga cikin ta zuwa wuyan ta, Sulalewa tayi ta fadi...
Chapter 108 · 0% Book details