← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 114

Sashe 73

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu abin da na dauka dan ko magungunin su duk sun kare, na kuma sanar da Gwaggo ta fada, tace malam zai kawo wasu idan ya gama hadawa. Ta baya nabi ko ina haske tamkar ba dare ba, na karasa ciki kai na a kasa kamar wata marar gaskiya. Tamkar a tare muka zo da Shaheedah, dan ko sallama ban gama furtawa ba naji shigowarta cikin isa da takama, na kai duba na wajan da Salman yake a zaune shima yana kallon mu, duk a zato na yana sane ya kiramu mu duka.

Sanye yake cikin wasu fitinannun kayan bacci masu mugun santsi milk color, ba karamin kyau suka yi mai ba abin ka da farar fata wacce ta hadu da jin dadi. Zaune yake akan sofa ya dora kafa daya kan daya yana girgizawa, hannunsa dauke da glass cup mai dauke da fura da nono da yaji ayaba da kwakwa yana sha. Daga ni har Shaheedah tsayawa mukai muna kallonsa dan kamar be san da tsayuwar mu ba a gurin, ina ta tunanin abin yi kawai naga ta nufe shi tare da hayewa kan cinyarsa tana lankwasa kai.

“Honey ban gane wannan lamarin ba, yaushe rabon da na kasance tare da kai, kullum kuna tare da waccen yarinyar mai kashin tsiya. Na gaji to gaskiya dan haka yau sai dai ta hakura da duk wata jarabarta dan ba zata samu ba.”

Shi kanshi Salman dagowa yai yana kallona, Shi kansa yaji abin da be taba kawowa ba. Ni kuma na sakar masa wani shu'umin kallo da ya sanya shi hadiye furar da ya kurba cikin bakin sa. Na karasa wajan center table tare da cire hijabi na ina faman jujjuya kugu na. Ban yi gigin zuwa gurin su ba tunda ta rigani hayewa kan cinyar da nake samu na zaune dan kawai na guma mata.

Ina tsaye kam sai faman gyara gashin kai na nake yi, ina kuma karya wuya cikin salon shagwaba nace.

“Whole world kasan yadda naji dadi dazu da ka matsa min mara ta? Ina komawa part dina period din yazo cikin sauki. But naji yanzu ma tana dan tsira min, shine nazo ka kuma yi min irin yadda kai min please.”

“Ba Zai yi ba din, ko baki ji ba? Na ce ba zai yi ba ko kin dauka bawanki ne Shi. Kuma yanzu ba ke kike da Shi ba, ni ce nan, kwana biyu ina sane da yadda kike yi masa zarya ko kin dauka Shi irin jarababnun mazan nan ne?”

“Dan Allah Yaya ki yi hakuri ya dan matsa min, ai ba wani abin zamu yi ba tunda dazu mun hadu, mun dade kuma tare. Ki barshi a matsayinsa na miji na ya yi min ba sai naje asibiti wani ya yi min ba.”

Nai maganar cike da nuna mata Cewa a kage nake, na kuma tabbatar mata da cewa mun yi wani abu da Salman din Wanda take ta kurin yau da ita Za a yi. Tartsatsatsatsasss muka ji jikin kunnuwan mu, da sauri nai tsalle biyu na rungume bayan Salman din ina kudindine fuska, Jiki na kuma yana bari alamar ina cikin tsoro, Sai faman wayyo Allah nake kai kace wani abu ya biyo ni tsabar iya acting. Shaheedah kuwa baki ta saki tana kallon yadda na cukwikuiye Salman kamar bana san ya gudu ya bar ni.

“Ke! Menene haka kamar wata yar karamar yarinya? Baki ga glass cup din hannunsa ne ya fadi ya fashe ba zaki mana Wannan dramar. Ke ko dai kin tab'a d'ana wasan hausa ne, dan naga kin iya acting din sosai?”

Nai kamar zan yi kuka ina cewa,

“Yaya ni banga lokacin da cup din ya fadi ba, kawai kara naji na dauka ma bomb ne. Kuma ni fa ko hausa drama bana kallo bare nasan me suke koyarwa.”

Shaheedah taja tsaki tare da kallon Salman tana shafar habar sa mai dauke da kwantaccen gashi, nima kuma naki sakin shi sai dad'a ma kwanciya da nai a bayan nasa ina faman sauke numfashi. Ta kuma jan tsaki, abin da yake batawa Salman rai kenan wato mutum ya yi ta tsaki a gabansa, ko ba dashi kake ba baya so sam.

“Yaya Shaheedah dan Allah ki bamu koda one minute ne ya gama yi min please.”

Shi kanshi Salman yana mamakin ganin yadda Shaheedah tak'i daga masa cinya tunda ba saba yin haka tai ba, ya gane cewa ta yi haka ne tunda Dije ma yi take a gabanta, sai dai sam ba ta burgeshi ba tunda abin na ta kwaikwayo ne.

"Idan zaki zo ki wuce kizo ga hanya nan, idan har sai ya danna miki zaki ji sauki toh wallahi sai dai marar taki ta zazzago makira kawai."

Na zare hannuwa da jikina daga na Salman na mike tsaya cikin nuna bacin rai a fuskata, zuciya ta kuwa shar dan nasan yanzu ma na guma mata bacin rai a zuciyar ta. Nazo zan wuce shi yasa tattausan hannunsa ya riko ni, muka had'a ido dashi, sai ya lashi saman lips din shi tare da furta.

"Why...?!"

Duk da ban gane dalilin ce min haka ba, sai nai amfani da wannan damar wajan sunkuyar da kai na ce.

"Ka barshi kawai na hakura tunda ba ta yarda ba, ni bana son rigima kuma itace babba."

Ji nai ya sakar min hannun haushi ya kamani duk a zato na zai ki saki na ko kuma ma ya janyo ni jikinsa dan mu kunsawa Shaheedah bacin rai. da sauri na dauki hijab dina na saka, ko ta kansu ban kuma bi ba haka na fice ina kunku ni. wallahi duk da bana jin ina son Salman, amman tabbas naji na tsani Shaheedah, haushin ta nake ji fiye da tunanin mai hasashe. Ina shiga daki nayi cilli da hijabin tare da fadawa kan gado, tunanin Mas'oud yana son fado min nai saurin mikewa zaune dan bana son akwai auran wani a kai na kuma a ce ina tunanin wani daban.

A can wajan su kuwa, Dije fitowa Shaheedah ta fara kissing din shi tana kokarin cire masa riga, Salman yai saurin rikewa tare da daga ta daga cinyarsa ya mike tsaya. kallan ta ya yi cikin dafe kai yana rintsa ido shi a dole ga wanda kanshi ya fara ciwo. Ya riko hannunta suka nufi kan gado yana ta dafe goshi yace.

"Kai na ke ciwo, ga sanyi ina ji lullube ni please."

Shaheedah ta saki baki da hanci tana kallon sa, ganin yadda yake rawar jiki ne yasa itama ta hakura ta rufa masa tattausan bargo tana mai hadiye maitarta a fili. Gashi maganin da ta sha so ake suyi mu'amula a daren, kuma ta kasa samu tunda gashi kwance yana rawar sanyi. Da kyar ta iya fitowa daga dakin ta koma sashen ta tana jan tsaki. Salman kuwa tana fita ya yaye bargon tare da bin kofar da kallo, sam ba wani ciwon kai da yake ji, kawai tunda ya ga wata yar k'aramar laya a wuyanta, ta sanya zaran sarka a jiki ta yadda idan ba kula kayi sosai ba bai zama lallai ka gane cewa laya bace.

Shi kuma tun da ya gani yaji sam hankalinsa be kwanta da sarkar ba, hakan yasan ya shi yin pretending na ciwon kai da jin alamar zazzabi. can kuma salon khadija ya fado masa, wato yarinyar ta san ta kan makirci, idan ban da haka me yasa idan su biyu ne bata tab'a ko rike masa hannu idan ba da dalili ba. Amman a gaban Shaheedah sai tai ta nuna ai har sun riga sun zama abu daya? yana son sanin me yasa take masa wannan salon, yau tsabar kwarewa ma cewa tai ya matsa mata mara bayan beji ba kuma be gani ba.

Tunani ya fara tabbas akwai wani abu da khadija ba ta son Shaheedah ta sani game da rayuwar su. kamar yadda yanzu ya fara tunanin akwai babbar matsala tattare da wadanda suke zagaye dashi. Lallai ya zame masa tilas akan ya kara wani salon kusanci tsakanin shi da khadija, yana ji a jikinsa cewar ba zata cuce shi ba duk da cewar yasan ba son shi a ranta, amman yasan ba tasan komai ba a cikin makircin sarautar Bassannabas bare tace zata yi masa. Dole ya kusantota gurin shi tun kafin wani ko wata a cikin masarautar su fara kulla mata mummunar dabi'a.

Da wannan tunanin ya shiga toilet yai alwala ya fito, gurin da furar sa ta kife yana nan ba a gyara ba, kuma a ka'ida Shaheedah ce ya kamata ta tsaya ta gyara masa, amman saboda bata saba ba kuma ta fita da b'acin rai shi yasa ko a jikin ta. Da kanshi ya tsabtace gurin dan ba zai iya barinsa har gari ya waye ba.

Sallah yai sannan ya yi ta addu'a tsawon lokaci kafin ya tashi ya hau kan gado, kwanciya yai tare da lumshe idanunsa. Khadija yake tunawa da yanayin yadda ya ganta cikin kayan bacci, be san dalilin da yasa yake yawan tunaninta ba. Amman ya fara jin cewa ya yarda da ita a cikin rayuwar sa, yana jin ta cikin zuciyar shi musamman yadda yaga tana nuna masa muhimman abubuwan da yai wasarere da su. Da kyar ya samu bacci ya dauke shi bayan ya duba sakkon da aka turo masa ta waya.

*WASHE GARI*
(SASHEN GIMBIYA KHADIJA)

Da kyar na iya tashi daga bacci sakamakon wani mummunan mafarki da nai akan Salman, bathroom na shiga ba jimawa na fito daure da alwala, sallaya na shimfid'a nai nafila ina idarwa nayi sallar asuba daga nan azkhar nayi ban tashi daga kan sallaya ba sai wajan karfe bakwai na safe. Wanka nai nazo na shirya kai na cikin wata atamfa d'inkin riga da zani, na dakko alkyabba na d'ora daga nan na fito zuwa parlour na inda na tarar da hadimai na suna ta aikin tsabtace gidan. Bayan sun gaishe dani ne na ce mutum daya tazo ta yi min rakiya sashen da bayi mata suke a cikin masarutar.
Chapter 73 · 0% Book details