← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 114

Sashe 96

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“A banza a wofi ma Hajjaju, ni kam na shiga uku na lalace idan har Salman ya kusanci yarinyar nan. Mari na ya yi a gabanta Hajjaju, wallahi wannan yarinyar ban san da uban da take takama ba har yasa aikin da muke yi akanta baya tasiri.”

“KI bari zan yi magana da mahaifinki.”

“Yaushe zaku yi har ku samo min mafita hajjaju?”

“Idan muka kebe zan sanar masa tunda yanzu yana fada.”

“No Hajjaju yau nake son mafitar nan, Ina son a kashe yarinyar can tun kafin asirin mu ya fara tonuwa.”

“Shikenan to bari naje nasa ai min iso da shi, duk yadda mukai Zaki ji.”

Katsewa Shaheedah tayi ta mike tsaye tare da kallon madubi tana faman goge hawayen da suke zubo mata tace.

“Wallahi sai na yi maganinki gobe Dije kike ko wa, na tsakeni na tsani duk wani naki. Yau kin sake Sanya min tsanarki tunda har sanadinki Salman ya mareni, Sai na kashe ki Kowa ma ya huta, Koda kuwa Salman zai hauka ce na rantse da Allah Sai na ga bayan ki muje zuwa zaki San kin shiga gona ta.” Kafa tasa tayi wurgi da kwalbar turaren kusa da kafarta tamkar shine ya yi mata laifin.

*WASHE GARI.*

Daman tun daren Salman yaga abinda Shaheedah tai da irin kudirinta, dan haka gari na wayewa ya kira ni a waya muka gaisa yace na shirya a lokacin Alhassan zai zo ya kai ni gida, kamar nace masa yayi wuri Sai dai nayi shiru na amsa masa da to. Wanka na shiga na fito Ina cikin shafa mai ya kira yace na fito ba Sai na tsaya yin kwalliya ba, abin ya dinga bani mamaki irin wannan gaggawa haka?

Pink shadda ce da akai min doguwar riga dinkin ya zauna a jiki na das. Yar jakar da na zuba kaya na janyo bayan na yafa mayafi wadatacce a jikina, na fito na sanar da hadimaina cewar zan yi tafiya kakata ce bata da lafiya suka dinga yi mata sannu, ban san me yasa na kife su da hakan ba ko dan naji Salman yace baya son kowa yasan da tafiyar?.

Kirana ya sake yi saboda duk yana kallo na ta cikin cctv, yace na tsaya Alhassan zai zo ya karbi jakar tawa, kafin ma ya gama gaya min..Sai gashi ya zo ya karba yace nabi ta kofar kudu nace masa to. Shi kuma Salman yace kafin na fita nayi addu'a, nayi sannan na fita still Ina rike da wayar a jikin kunne na muna magana.

“Zan kira kawu daddy zamu yi magana dashi, abin da nake so dake shine ki kula min da kanki baby na.”

Murmushi kawai nayi bance komai ba saboda rashin abin fad'a. Sai da na shiga mota sannan yace zai gayawa Ammie kome ne ne dan yasan za tayi cigiya idan taji shiru. Da kyar ya ajiye wayar ni dai Ina jin kamar da akwai dalilin da yasa shi cewa na tafi tunda da munyi magana cewar dashi zamu amman yanzu yace na taho. A raina dai nace tafi nono fari naje na sake ma babu nacinsa na kwanaki biyu.

A tsaye a parking lot muka ga kawu daddy da alama yasan da zuwan mu, ya karaso cike da fara'a nai saurin bude murfin na fito, cikin murnar ganinsa naje na rungume shi. Har ga Allah bana raba shi da mahaifina hakan yasa nake manta cewa uncle dina ne ba wai shine Baffa ba.

“Sannunku da isowa Gimbaya.”

Na dago cike da kunya tare da sunkuyar da kai Ina cewa.

“Daddy harda kai a sunan nan?”

“Eh mana ai Gimbiyar ce. Shiga ciki muyi sallama da malam Alhassan.”

Nace to tare da shiga cikin gida cike da murna. Yaushe rabona da gidan tun randa aka fitar dani zuwa masarauta. Babu Kowa a parloun kasa hakan yasa kai tsaye na nufi dakin su Ya Shukrah, na gansu duk sunyi dai-day akan gado suna ta bacci, na saki murmushi tare da juyowa na nufi dakin Mami, itama tana kwance tana bacci a raina nace 'kaga yan hutu basu da wata matsala' a zahiri kuma fitowa nayi na nufi parloun kasa Ina jiran daddy dan ba zan Iya tashin su ba.

Da fara’a ya shigo ya zauna, na gaida shi cike da ladabi ga kunya da nake ji dan gani nake tamkar sun gane duk abinda yake tsakanina da Salman. Kawu daddy ya gyara zama tare da cewa.

“Nasan baki yi breakfast ba dan mijin ki ya sanar min, ki shiga kitchen kisa masu aiki su yi miki abinda kike so kici, gashi wadannan sarakan baccin basu tashi ba tunda suka yi sallah suka koma.”

“Na leka ai naga suna ta bacci shi yasa ban tashe su ba.”

Yace.

“Eh tashi kije kice suyi miki abin kari dan maimartaba sai nanata min yake baki yi breakfast ba kika taho.”

A rai na nace 'lallai Salman babu kunya, kawu daddy yake ta shaidawa banci abincin na sai kace ya fishi sona' A fili kuwa mikewa nayi naje na sanar da masu aiki wadanda ni banma sansu ba da alama sababbi ne, nasan kuma kila ajiye aikin suka yi saboda halin su Shukrah na wulakanci da gadara. Parloun na dawo inda na samu kawu daddy zaune yana duba wata takarda wacce da alama tana da muhimmanci. Kallo na ya yi bayan ya ajiye takardar yace min.

“Kinga kinyi sa'a daman jibi zamu tafi Lagos bikin Fatima. Nan suka aiko da cards dinki, Sunce kunyi magana ko? God so kind kuma mai martaba yace daman kuna da shirin zuwa amman ba zai samu dama ba shi saboda wasu matsaloli da yake son ya yi settling d'in su.”

Baki na yana rawa nace.

“E! Nasan da bikin, To! Kawu to me yace? Yace dai na biku ko?”

Shiru yayi yana nazari na kafin ya yi dariya yace.

“Yace aje dake kiga gurin idan kun tashi zuwa ba sai kunzo kun nemi address ba.”

Murna ta cika ni na dinga yi daga nan muka ci gaba da hira har zuwa lokacin da aka kammala dafa min indomie da kwai, abinda ya bani mamaki guda biyu ce amman na cinye ta tas harda sude plate abin da nake cin daya da kyar amman yau har biyu da dafaffan kwai uku. Lokacin ne Mami ta fito, tana gani na ta saki baki tama kasa karasowa kasan.

“Hajiya sakko mana.”

“Su Dije na gani yau a gidan, anya ba b'atan hanya tayi ba kuwa.”

“A'a zuwa tayi ta gaishe mu.”

Cewar daddy dan yasan tsab zata Iya gasa min magana.

“Alhaji kenan, baka san Dije yar dadi miji bace? Ace tunda yarinyar nan tai aure bata sake zuwa gidan nan ba saboda bamu muka haifeta ba.”

“Wallahi Mami ba haka bane ba, Salman d'in ne bashi da lafiya.”

Nayi maganar cike da son ta yarda dani. Karasa sakkowa tayi ta zauna a kusa da kawu daddy tana jan furfurar kansa da ta dan fara yawa, nayi kasa da kai na cike da kunya Ina tuna yadda muke da Salman. Gaida ita nayi ta amsa min tare da tambayar yadda nake da lafiya ta, naji dadi sosai na kuma gaya mata lafiya lau. A nan ne kawu daddy yake ce mata zasu tafi dani Lagos din tunda dama zuwa nayi da niyar yin kwanaki luckily kuma yazo da bikin Ya Fatima.

Fitowar su Ya Hameedah ne yasa ni saurin tashi Ina murmushi, suma dai kamar Mami tsayawa sukai suna kallo na, Sai dai kawu daddy ya taka musu birki tare da ce musu su san yadda zasu dinga yi min magana, wannan dalilin ne yasa duk suka hadiye abinda ya taso musu suka shiga gaida ni. Bayan mun gama gaisawa ne daddy yace mu koma daki muka tashi duk muka koma Ina ta jin dadin ganina cikin Yan uwa.

Jefi Jefi idan Salman ya samu time yana kirana yaji lafiya ta, har zuwa dare.

Shaheedah kuma sai aikin neman ganin bayan dije take, inda aka tabbatar mata da cewa bata cikin masarautar, Koda ta tambayi Salman cewa yayi shima tashi ya yi yaga bata nan ta Iya yiwuwa guduwa tayi saboda abinda Shaheedahn tayi. Muka cigaba da shirin tafiya Lagos inda Salman ya turo min da kudi masu yawa Wai nayi amfani dasu, gashi kawu daddy ma ya bamu mu da su Shukrah kuma duk kai daya.

*LAGOS*

Tunda muka sauka aka turo driver ya dauke mu nake jin wani irin farin ciki, kasan cewar Ina kusa da window yasa Ina hangen komai akan hanya, wani ya burgeka wani ya baka haushi a haka har muka isa gidan uncle Haysam. Gida ne katon gaske mai kyau da tsari, Sun canza gida, Ba wanda na sani bane zuwa na nafarko, Yara da manya suka fito yi mana maraba suma cikin murna da nishadi.

“Gimbiya Khadija....”

Suka dinga fada kunya kamar ta kashe ni, na samu ni dai da kyar na zauna bayan nasa an kawo min ruwa nasha. Kiran Salmanu
ne ya shigo, a raina nace shidai baya gajiya da kira kamar wani marar aikin yi sai na kira na. Gajiyar hanya ya yi min tare da sake jaddada min cewar ban da zama da yinwu na amsa masa, hayaniyar da ya dinga jiyowa itace tasa be dade akan wayar ba ya katse. Aka dinga zuwa gani na ai matar sarkin bassannabas ce, wacce tazo kwanakin baya kafin auran cacacaca aka dinga yi.

Munsha biki sosai an kai amarya gidan mijinta ina kallon ta a rai na nace 'itama fa haka zasu yi da nata angon oh ni Dije' wallahi abin ne yake bani mamaki idan Ina tunawa da irin yanayin da muke kasancewa da Salman, wani ince Anya ba shi kawai yake irin wannan abun ba? Wani kuma ince Wai ko wace mace haka ake mata ne? Babu amsa saboda ni nake tambayar zuciya ta.
Chapter 96 · 0% Book details