Sashe 7
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Allah sitiri buƙi, inci tsohowar....”
Ban kai ga karasawa ba naji wani irin abu ya sauka a tsakiyar kai na, babu arziki na yi kasa ina kuka ina ihun a kawo min dauki. Kafafuwa da na gani sanye cikin wani cover sheo shine ya tabbatar min da cewar wani ne ya yi min abu. A hankali na dinga dago ido ina karewa jikin kallo, kafin daga bisani na sauke idanuwa na biyu na dora su kan fuskar shi, gabana ya buga ras! Saboda tsananin tsoro da naji. Sam fuskarshi babu annuri bare kayi tsammanin fara'a a kai, ya kalle ni fuska a murtuke tare da cewa.
“Bar nan gurin ko na babbalaki.”
Sam ban san daga ina furucin ya fito ba, dan ban maji kalmar a baki na ba bare nace ni nayi, kawai saukar furucin nayi a cikin kunnuwa ne ina cewa.
“Saboda me?!”
“Ohh tambaya ta kike yi?”
Cike da gasgata tambayar da ya yi min nace,
“Eh walle talle ban gane mekake nuhi da cewa na bar gurin ba.”
Bacin rai ya kuma ziyartar zuciyar shi, ya dan matsa kusa da bishiyar darbejiyar dake bayan shi, ganin yana niyar tsinko bulala yasa nayi saurin rugawa da gudu tare da yi masa gwalo. Shi kuwa gabaki d'aya haushin yan kauyan namu yake yi, tunda yazo yake faman korar masu zuwa gulma wato iri na kenan, bamu shiga anyi da muba, gashi mun hana wadanda ake koyawa suyi cikin nutsuwa. Malamar ta leko ta taga tana yiwa malamin magana cikin dariya.
“Malam Auwal kana ta fama kaima.”
Yaja dan karamin tsaki,
“Ni anya zamu shirya da yan kauyan nan kuwa? Wallahi malama Mardiyya baki ji yadda rai na yake baci ba, gashi sam basu da tarbiya mazan su da matan su.” Dariya malama Mardiyya tayi.
“Wallahi kuwa malam Auwal sai dai kawai muyi hakuri tunda Allah ya kaddara cewa nan zamu dawo, ni dama mai gida na da kyar ya yarda wallahi dan cewa ya yi sai dai na ajiye aikin saboda nisan dake tsakanin mu da wannan Kauyan.”
“Mtwww! Ni abin da yake bani haushi malama shine, yadda kina ganin yara a kauyan nan maza da mata sunfi dari biyar duk wadanda basa zuwa, dubi ko class d'aya mun kasa samu saboda wulakanci, babu abinda suka sani sai tallah shegun.”
Malama Mardiyya ta kwashe da dariya tana gyara zaman mayafinta tace,
“Lallai malam Auwal kafi mai gida na jin haushin wannan kauyan, kasan shima ya taba zuwa nan yin aikin ƙidaya, nake gaya maka suka ki amincewa a yi musu haka suka tattara suka koma gida ransa a mugun bace. Shi yasa da nake gaya masa anyi min transfer zuwa nan ya fara masifa, da kyar na samu ya amince, tunda gaskiya ni dai albashin da nake karba yana rufa min asiri sosai.”
Malam Auwal ya tabe baki kai kace shi ba da albashin ya dogara ba, mugun dan kwalisa ne dan irin samarin nan ne da suci a cikin su gwara su sanya a jiki ace sunyi abu iri kaza a rayuwar su. Matashi ne dan a shekaru ba zai wuce ashirin da bakwai ba, dogo ne baki irin mai kyau din nan mai dauke da yar siririyar fuska, idanunsa mici-mici kamar wanda aka sauwa, habarsa dauke da d'an guntun gemu wato tabani kasha hadisi da samari ke yi. Ya kuma taɓe baki tare da cewa.
“Ai kuwa ni zanyi maganin su wallahi tallahi, dan babu shege ko shegiyar da zata sanya ministry su zo suyi mana dibar albarka.”
“Da kyau malam Auwal ina bayan ka wallahi dari bisa dari.”
Cewar malama Mardiyya tana ta dariya.
Wucewa ya yi ya tafi ita kuma taci gaba da koyar dasu kamar yadda ta soma yi.
Ina ta gudu ban tsaya ba, duk a zato na yana biye dani ashe bai ma biyo ni ba, sai da naje kofar gidan mu na turo kofa tare da lekawa sannan na tabbatar da cewa gudun banza nayi. Gajiyalle ta damko min wuya na tare da tun kudani cikin gida tana masifa.
“Gantalalliyar yarinya kawai, babu abinda kika sani sai yawo da bin lunguna yin dambe. To zaman banzarki ya kare daga yau, maza dauki gashi nan na soya nayi miki kullin biyar, goma da ashirin. Tun dazu na hangi su Lami sun tafi tallar wainar roga da wainar gero nasan zuwa wannan lokacin ko basu siyar ba toh sun kusa. Amman ke da yake ba ƴar mutunci bace, baki taba yin tunanin abin arziki ba, tashi maza ki tafi yar kasuwa ki sai sa min.”
Wani sassanyan dadi ya mamaye rai na, yau na samu abin da nake so wato damar yin tallah, saboda tan matukar bani sha'awa, musamman idan naga yadda kawaye na suke sha'anin su da kudi. Carab na dauki farantin gyada ina murmushin farin ciki nace da Gajiyalle.
“Daman fa Gaji kece baki sani ba, ina ta so na gaya miki ki dinga yin wani abu ina fita yar kasuwa dashi. Toh sai na yi shiru dan karki doke ni, yanzu kuwa kinga kema zaki zama mai kudi kamar Innarajo, dama har ta fara tarawa Balki kayan aure, nima kinga sai ki fara yi min tanadin nawa.”
Ta sakar min wani banzan kallo wanda ya tabbatar min da cewa taji haushin kalamai na, sai dai bata ce komai ba har na tashi na fice daga gidan. Wayyo ranar jina nake tamkar a gidan aljanna saboda farin ciki, gashi tun kafin na karasa yar kasuwan na fara ciniki a majalisar Sallau mai tsire.
Cas! Suka bani kudin gyadar naira saba'in na dauki farantin na dora a kai na ina digirgine ga kuma kudi a hannu ina kuma lissafawa. Ta kusa da makarantar da aka bude na bi, har zan wuce sai kuma na sake shiga ina mai kulle kudin a gefen mayafi na da nayi damara a kuguna. Wasu malamai suka kira ni suma suka siya, naga na dazu da ya biyo ni amman wannan karon ko kallo na beyi ba, har zan tambaye shi ko zai siya, sai nayi shiru dan na lura kamar bashi da mutunci.
Na tafi yar kasuwa kasan cewar ni sabuwa ce kuma gyadar sabuwar suya ce sai ya zamana ta kare da wuri. Ina kudin Gajiyalle? Na same su ci banza ci wofi tamkar nawa ne, ni har mantawa ma nayi cinikin ba nawa bane saboda rufewar idanuwa. Ban lura cewar kudin sun kusa karewa ba sai da naje siyan kankana kwallo daya aka ce min naira saba'in, jiki na yana bari na zaro ina kirgawa naga arba'in da biyar ne kawai. A lokacin gabana yayi mugun faduwa na dafe kirji na tare da furta.
“Na shiga uku da Gajiyalle.”
Babu shiri na dauki farantin gyadar na tafi gida, sai da na kusa zuwa sannan na fashe da kuka ina tafiya ina yi kamar wacce aka yiwa dukan tsiya. Na shiga zaure na samu kasa duk na zuba a jikina da gurin baki na idan ka gani ba zaka taba kin cewa ba na jaki na sha ba a gurin manyan maza, na shiga ina dora hannu aka. Gajiyalle na zaune tana dinkin hula gani a wujejjige yasa ta saurin mikewa tana tambaya ta.
“Lafiya Dije?”
“Na shiga uku Gaji zasu kashe ne.”
“Suwa ye?”
“Yan sholisho... Wayyo Allah na Gaji sun kwace cinikin na shiga uku.”
“La'ilaha illa lahu ni jikar mutum hudu me kike son sanar dani Dije? Kina nufin kice an siyar da gyadar yan iskan gari sun turmusheki sun kwace cinikin?”
Na gyada kai na ina share maina da bayan hannu, tace.
“Na shiga uku Dije kin cuce ni, dan kaniyarki ina karfinki da har kika bari aka kwace kudin? Shikenan daman gyadar rantowa nayi nace zan yi gwaji gashi nan kin gwadani Dije, wallahi Kedai banza ce sakarai shashasha. Allah ya isa ban yafe ba, gashi dole na biya.”
Tana magana rana duka na ni dai ban da bata hakuri babu abinda nake yi, cikin dashasshiyar murya nace bayan na zaro ragowar kudin.
“Wannan kawai suka bani, suma din sai da suka mare ni da suka ji nace ba tawa bace ta babar mu ce.”
“Uban babar ku, nice babar taki dan malafar gyatuminki? Da ace kin dauke ni uwa ai da ba zaki bari su karbe miki ba bakar munafuka kawai, tashi ki bani waje ko na karya ki, bana son ganin ki Dije na tsane ki.”
Na tashi kamar munafuka na fita, zama nayi a zaure ina tikar dariya ta ganin yau na rainawa Gajiyalle hankali. Tun daga lokacin kuwa bata sake gigin dora min komai ba, duk nacin da nayi mata kin yarda tayi haka na hakura, na koma gidan jiya wato yawace-yawace kwararo-kwararo ina gurin.
*SASHEN MAI GARI JAMILU*
Gaba d’aya kusan duk maza dattawan dake karkarar Durbun suna zazzaune a karkashin bishiyar darbejiyar da mai gari jamilu yake zaune. Yana hakimce akan kujerar sa yasha rawani na masu gari, Sauran mutane na daga kasan taburmi sun yi gurfane suna sauraron mai gari. Malam Bashari (baban Dije) shi ma yana gefe kansa a kasa. Mai gari ya sake jan majina kafin ya cigaba da cewa,
“Toh nagode da abunda wasun ku suka yi min, Wato ina matsayin mai garin nan ban isa na zartar da hukunci ba kenan sai an gayawa magabata na? Saboda an rena ni shine Za’a kai ‘karata wajen hakimi? Kai bara na fito muku a Mutum. Kauyen nan tsatso na ne suka kafa shi, Babu wasu wa’enda suka isa su zartar da hukunci bayan namu. Ku ba farin cikin ku bane ace ‘ya’yayen ku suna boko? Yanzu ‘yayan kansila su biyu ina har alfindi yake kai su kullun suyi bokon? Gata ya samu yanzu za’a zo amana makarantu shine kuke bakin ciki? Wannan wane irin kidahumanci ne? Toh dai,