← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 114

Sashe 28

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsab nayi shiri na cikin wani arnan lace Coffee mai dauke da ratsin milk d'in zare, an yi min din kin doguwar riga wacce ta amsa sunan ta. Nasa mayafi milk da takalmi sai agogo da shima ya kasance ruwan madarar. Na tsaya a gaban madubi ina karewa kai na kallo, wanda nasan idan har Mas'oud ya ganni to tabbas ba zai taba kin bina ba, dan zai ce za a kalle masa ni, yana da matukar kishi dan ko a gurin aiki ya dinga min magana akan yadda mutane suke yabo na da kuma wadanda suke biyowa ta gurinsa suna sake gaya masa yadda Allah ya bani halitta mai kyau.

Jakata na dauka na fito ina bin step d'in nan a yangance, yanzu fa babu batun tsoro dan gudun da nake yi a kai ko yan gidan albarka. Na saba da shi yabi jiki na sai kuma nan gaba ban san me zai bani wahala ba bayan shi. Naje dakin Mami na yi mata sallama a lokacin Kawu ya fito shima, muka yi sallama na tafi shima Mami ta raka shi motar sa ya wuce. Da naje gurin aikin banga Mas'oud ba, a gurin Aminu Gumel nake jin wai sun tafi asibiti Abban sa ne bashi da lafiya. Na karbi kayan aiki muka tafi a motar gidan radio d'in. Sanda muka je an taru matuka, na samu naje can kan highe table na kara abinda zan dinga daukar maganar manyan baki sannan na koma gefe inda aka tanadarwa yan jaridu gurin da zasu zauna.

Gurin saukar karatun Alqurani mai girman ya kawatu sannan kuma ya yi cikar da alkalami ba zai iya rubutawa ba. Manyan mutane kuwa ba'a magana wadanda suka halarta. Sarkin musulmi, gwamna, Sarkin Basannabas da manya masu mukaman gwamnati da ma yan kasuwa dake jihar.

Tunda tashigo wajen yake jin yanayin sa na canzawa, Yana hakimce akan doguwar kujerar girma da aka lullube da farin yadi. Me dauke da tambarin ‘’Sarkin Basannabas” . Lokaci zuwa lokaci ya kan duba designer agogon dake daure a wutsiyar hannun sa, Ba shi da ikon ya nuna gajiyar sa. Shin meyasa ma yazo? Yai taiwa kansa tulin tarin tambayoyin da shi kansa bai da amsa. Bakin sa ya masa nauyi. Sanye yake cikin hadaddun kayan sarakuna. Kallo d’aya zakai masa kasan shidin matashin sarki ne, Mai ji da ado da zatin halitta. Taune kasan leben sa yai ta cikin rawani. Idanun sa na saqale da bakin gilashin sa tamkar na gado. Tun yana makaranta ance kullum cikin saka shi yake. Bai taba bari aga kwayar idanun sa. Sannan baya kallon mutane na tsawon wani lokaci kowaye kuwa kai.

“Ya RABB! I’m exhausted....”

Ya furta a labban sa yana jera ajiyar zuciya. Tunda aka fara hidimar saukar ba kallo yake ba. Kansa a kasa yana jujjuya zobunan azurfar hannun sa.

Sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS) kyakkyawa ne na ajin karshe, Ma’abocin ado (sutura da zuciya) Dauke zuciar sa take da son taimakawa jama’a da kuma alkhairi agare su. A Zahiri ka ganshi zaka dauka ya gama da cewa duniya da lahira saboda yadda yataso cikin gata da ingatacciyar rayuwa, Tun kafin ya gaji sarauta awajen mahaifin sa (Marigayi sarki Aliyu Salmanu Ibrahim) ya kasance mai hankali, Samun kamammen ‘da irin sa sai an tona, Da kamar wuya. Bai dauki rayuwa da zafi ba, Yana bin komai ahankali, Duk da cewa ya tashi cikin gata, Bai taba daukar gatan nasa tabbatacce ba. He’s kind, attentive and most caring..

Yana kishingid’e ya jiyo zazzakar muryar ta na masa yawo a cikin kunne,

“Sunana Nana Khadijaa Basheer Inuwa. Ni ce yar jaridar dake wakiltar gidan rediyo da talabijin na DokinKarfe24. A tare da ni akwai matemaki na Ashafa Ghali Dikko.. Shin mai girma sarki ya kaji lokacin da aka ce wannan babbar makaranta zata yi taron saukar karatun Alqurani mai girma a cikin jahar ka mai albarka?..”

Kwata kwata sarki Salman bai bi ta kan zancen da take fada ba. Samun kansa kawai yai karo na farko a rayuwar sa da yayi wa bil adama kallon k’urilla har haka. Tun daga tafin kafarta ya fara kallon ta, ya tafi ga tsarin shigarta ta jiki har zuwa kan fuskar ta wacce tasa shi lumshe idanuwa ba tare da ya ankara ba. Ya sake bude ido ta cikin dark shades d'in fuskarsa yana kallon yadda ta d'an rankwafo alamun tana jiran bayanin sa duk da tazarar dake tsakanin su. Bata ankara ba taji an sanya wata zungureriyar sanda tare da buge abin daukar sautin na ta. Kasan cewar idanun shi suna kanta ne yasa yaga yadda tabi wanda ya yi mata wannan wulakanci da kallo tana tsuke fuska.

“Karya ki ke yar jarida, sai dai kiyi mana tambaya ba dai da sarki mai daraja ba.”

Sarki Salman ya sake kallon ta dan yaga wani irin mataki zata dauka gurin bafaden shi da ya yi mata wannan abun. Sai yaga ta dauki abin daukar maganar tana kallon shi tare da sanya tafin hannunta da yasha jan lalle a yan yatsun suka yi matukar kyau. Sai kuma yaga ta juyo ta kalle shi, ya dauke kai duk kuwa da cewar yasan ba tasan ita yake kallo ba sanadiyar glasses d'in shi.

“Amman ya kamata muji ra'ayinsa dan yana da matukar amfani ga al'ummar mu.”

“Karya kike yar talakawa.”

Bafaden ya sake fada yana bula babbar rigarsa dake nuna cewar shi din bafaden sarkin ne. Wani irin takaici ya rufe Dije, ta sunkuyar da kai kasa. Duk a tunanin sarki Salman kuka zata yi, besan zaka da warwara ta shiga yi da zuciyar ta ba. Sai yaji tamkar ya yi mata magana, amman mulki da izzar dake tattare da sarauta ta hanashi koda yin motsi. Dije ta kuma kallon sarki Salman duk kuwa da banda tulin rawanin sa bata ganin fuskar sa ta sake cewa,

“Ranka ya dade gashi an gudanar da karatun saukar Alqurani, ya kaji a ranka game da yaran da suk.....”

Bata kai ga karasa tambayar ta ta ba kawai taji saukar sandar nan a gefen kanta, wanda ya yi sanadiyar da yasa ta saki wata gigitacciyar kara mai gigita kwakwalwa, ta kuma sulale ta fadi kasa sumammiya. Dai dai lokacin sarki Salman ya mike aka dora masa malafarshi ya tsaya cak yana kallon yadda yan sanda suke korar mutane dan a samu yadda za a ceci yar jaridar da bafadanshi ya rafke. A hankali ya sakko daga wajan ya nufi motarsa ba tare da ya tsaya ya yi sallama da mai girma gwamna dake gurin ba.....
...

______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
*K..........*

*NH*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA*

*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *
*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*

*15*

Gabaki d'aya sai hankalin mutane ya dawo kan Dije dake yashe a kasa. Shi kuwa sarki Salman tuni motarshi ta bar gurin taron tamkar ba sune suka jaza wannan ta'asar ba. Basu tsaya sunji me yake faruwa ba bare su san halin da yarinyar mutane take ciki. Kafin kace menene tuni aka dauke ta aka sa a mota sai asibiti domin bata san inda kanta yake ba. Kasan cewar akwai manyan jami'ai hakan ya sanya suna zuwa asibiti babu wani bata lokaci aka shiga bata taimakon gaggawa.

Mas'oud dake kan hanyar shi ta zuwa gidan radio saboda yaje gida ya maida mahaifinsa kenan, kawai yaji labarin cewar Dije na can asibiti bata san inda kanta yake ba. Ya juyo da motar ya nufi asibitin cikin tashin hankali da tunanin abinda ya sa har hakan ya afku a kanta. Koda yaje kasa shiga cikin asibitin ya yi, yan sanda sun hana kowa shiga. Ya ciro id card d'in sa ya nuna musu amman duk da haka suka hana shi shiga, dama duk sauran yan jaridar da suka biyo su suna tsaye a bakin gate an hanasu shiga, saboda so ake a boye maganar cewa bafaden sarki ne ya yi sanadiyyar hakan. Aka fara cewa ai cikowar mutanan gurin ne yasa numfashin ta ya dauke ta zo faduwa shine ta buge.
Chapter 28 · 0% Book details