← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 114

Sashe 13

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi tafiyarsa hankali kwance, babu abinda ya damesa da yadda yaji Gajiyalle tana kuka tana ihu kamar wata tababbiya. Ni kuma na karasa kusa da ita wai zan lallashe ta tunda naga babu mai bata hakuri, makota ma basu shigo ba bare asa ran zasu bata hakuri su taushi zuciyarta. Nasa hannu zan kamo nata tayi saurin sanya kafa tare da ture ni na buge da bango, dai dai lokacin Baffa ya shigo kuma yaga yadda ta ture ni. Ya kalle ni ya kalli Gajiyalle daga karshe yace dani.

“Ummina me ya faru?”

Na tashi tsaye ina karkade jiki na tare da turo baki.

“Ba Mudikalle ne ya daukar mata a....” Ban karasa ba tayo kai na tana cewa,

“Munafuka yiwa mutane shiru, daman kallon mu kike kina sauraro dan ki dinga zuwa kina gayawa mutane? Ina ruwanki yar jakar uba? Mudikalle dai nawa ne dan haka ba komai ɗan ya dauki kayan uwarsa. Ke yanzu ba hanyar lalacewa kika dauka ba? Yanzu daga bokoko kike shegiya, shi sana'a zaije ya fara ya zauna da mutuncinsa.”

Na kalli Baffa naga ko zai ce wani abu amman ya yi shiru sai hula ma da ya gyara tare da wucewa dakinsa yana cewa.

“Toh shikenan Allah ya kyauta.”

Haushi ya kamani, Ban taba ganin miji irin Baffa na ba. Duk gidan da nake shiga matan suna tsoran mazajen su amman banda Gajiyalle da Baffa na, gabaki d'aya rayuwarsu ta banbanta da ta sauran ma'aurata. Gaji ta kuma kai min doka na goce hannunta ya sauka jikin bango ta kuma sakin wani ihun tana zagi na.

Waje nayi dan nasan ranar ko kanzo bazan samu ba dan haka gwara naje na nemo abincin da zanci. Karatu kuwa gabaki d'aya na manta dashi bare na tuna da kyautar da malam Auwalu ya bawa Siyama, ko kuma dan be karfafa min gwiwar cewa zai bani ba shi yasa na manta oho. Haka dai na yini a waje sai dare na sake komawa gida, da nayi sallama ma bata amsa ba ko haushi take ji har lokacin oho mata. Na samu waje na kwanta ina ta uban nishi saboda naci tuwo a gidan su Nafisa ci na hauka saboda sai da kowa ya tashi ya barni a wajan kwanon.

Gajiyar wasan jiya da kuma haushi na da Gajiyalle kiyi yasa na makara da tashi, sai kusan karfe takwas da kwata na farka. Ina ta hamma na shiga bandaki na fito ina kallon kofar dakin ta naganshi a kulle tasa tsumma ta kulle kofar alamar ta fita unguwa. Na shiga dakin Baffa yana kishingid'e yana sauraron radio ya kalle ni cike da mamaki yace.

“Ummina baki tafi makaranta ba daman?”

“Makaranta kuma Baffa! Wacce?” Ina turo baki ina maganar dan sam na manta da ita.

“Boko da kika fara zuwa mana jiya, ina nan ina murna kina can kina ta zuba karatu ashe kina cikin gidan nan Ummi na.”

Nayi saurin bubbuga kai na jin yana motsi wanda bana raba d'aya biyu kwarkwata ce ko amosanin ka, nace.

“Aradu na manta da ita, yo nifa yanzu na tahi Gajiyalle ko tahi na bata yi ba kuma yunwa nake ji Baffa.”

Gefansa ya duba ya dakko wani kofin sulba ya miko min, nasa hannu na karba. Koko ne ya sake miko min kaushi mai dauke da danwake yace naci. Ina ci muna hira yana cewa nayi sauri na tafi makarantar.

“Baffa har kyauta ake ba yarwa a ajin mu.”

“Masha Allah, kema ki samu ki ciwo babba kinji Ummina?”

“Yanzun nan ma kuwa Baffa, dan ma dai malamin ba hi da mutunci walle. Baya sona he ya yi ta zagi na yana kira na da yar tallah.”

Baffa ya girgiza kai dan shima yaji babu dadi yadda naga fuskarsa ta bayyana. Ina gamawa ya bani naira biya na dauki hijabi na da yaci uban dauda na tafi ina wake-wake na. Kai tsaye ajin mu na jiya na shiga, ganin ba malam Auwal bane yasa nayi saurin fitowa na kuma lekawa d'aya ajin nan kuma malama Mardiyya ce, na kuma fitowa da gudu, tana ta kira na amman nayi mata banza saboda yau ajin da malam Auwal yake nan nake son zama.

Can na hangoshi a ajin yara wato ecc yana ta raba musu alawa suna ta murna, ba zato kawai yaga ana miƙa masa hanu, girman hannun yasa shi saurin kallon mai shi muka hada ido na sakar masa dariya shi kuma yana hararata yace.

“Ke kuma daga ina kamar wata aljanna?”

“A bani nima.”

“Me?”

“Alawar da kake rabawa.”

“Ke wai me yasa baki da hankali ne? Kinga sa'anninki a nan wajan?” Kamar ban san abin da yake yi ba, idanuwana suna kan alayoyin yaran ina ta hadiyar yawu.

Ni gaba d’aya ba damuwa nayi da gasamin maganganun da yake yi nayi ba. Fatana dai ya dankamin alewar da yake rarrabawa yan yara. Na sake matsawa kamar zan shiga jikin sa, Ya tsula min tsumangiya ko zafi ma babu. Na kwashe da dariya ina karkade inda ya dake nin, Ma’ana dai na mayar masa da kayan sa domin ba zafi tai min ba. Cike da mamaki yake duba na,

“Zaki matsa ko sai na kara zuba miki wata?”

“A hayye nanaye! Malam Lauwali kenan. Yo dan wannan dukan naka shine me zafi? Yo ko gajiyalle takan dau lokaci tana kirbata kafin nayi kuka. Nide yanzu dan bani guda d’aya ko rabi ce Malam Lauwali.”

Zubamin wata shaudar yayi yana huci,

“Ke waye Malam Lauwalin? Ni sa’an wasan ki ne. Naga alamun tsantsar reni a tattare dake. Kneel down!”

“Lid-dawun? Me kenan! Ayyo. Tab! Yasin na mance sunan kane Malam.”

“Kneel down! Bush girl!”

“Lid-dawun! Bushgyas. Nifa kayi da yaran hausawa bana arna ba. Dan bansan me kake nufi ba.”

“Zaki sani yanzu kuwa. Jeki tsakiyar ranar can ki tsugunna awajen akan gwiwoyin ki, Duk malamin daya ce ki tashi kice nace a’a.”

“Tafi nono fari.. a hayye sha madarar lilo..”

“Ke me kika cewa.?”

Ko kallon sa banyi ba, Na kwaye rigata na zuba gwiwoyina a kasa, Inata sauke masa kwandon tsinan taka.

“Matsiyaci, akan ya bani alewar yana bakin cikin zan da zanyi. Allah ka saka min.”

Ina daga nesa ina zabga masa harara, Da sauri ya taho ko duka na zai yi sai kuwa ya bige da kyauren kofar ajin, Me zanyi inba dariya ba? Na shjga kyakyatawa kuwa ina nuna shi. Cikin haka Malama Mardiyya tazo ta same ni,

“Khadija me kike anan!”

“Malam Lauwali ne nasan, Ya hanani alewa, Ya shasshauda min tsumangiya, Shine nan kuma yace nazo na zuba gwiwoyina a kasa. Ai kuwa gahi can ya doke gohin sa a kyaure.”

Na karasa ina babbaka daria, Malama Mardiyya ta girgiza kai kawai,

“Malam Auwal sunan sa ba Lauwali ba. Kuma ki dena yin abunda Za’a dake ki. Sannan malamai tamkar iyayen ka suke kinji? Domin daka baro gida kazo hannun su, Duk wani abu da zasu saka dole kayi. Sai yanzu kikazo makarantar?”

“Yasin Gajiyalle ce bata tahe ni ba, Jia da na koma Mudi ya janyo dan akuyar ta zai sayar. Taita ife-ife tana rokan sa ya bari ai kuwa yaki yadda ya tafi da akuyar nan, Yace ai yace ta bahi kudin jari tak’i. Hi nefa naje rabiyar fadan ta tattake ta doke ni da hyarbebiyar k’afarta a salansar kirji na. Ai kuwa inaga tun duhun safiya ta fice. Hi ne fa motsin ta da ban jiba ya makarar dani, He ba dad’ewa na zo.”

“Oh ni Mardiyya! Kayan jiya kika sako, Kinyi wanka kuwa Khadija? Sallah fa kinyi da asuba?”

Girgiza kai nayi,

“Yasin da asubah ina ta narkar bacci na, daman masifar Gajiyalle ce ke tahi na, toh kuma ba tayi ba shi yasa ban san sanda akai asuhabin ba. Wanka kuma dame zanyi hi Malama? Ba kayan wankan fa.”

Na karasa fada ina sosa kai na.

“Ko dai qudubus ko kwarkwata ce a kan nan billahil lazi. Gidan d'an wanzan zanje ya yahe gahin gaba d’aya.”

“Subhan’Allah! Allah ya shiga lamarin ki Khadija. Kan naki zaki je a yashe gashin? Saboda me Khadija? Ki dena fad’ar haka. Mace yar gyara ce. Ana gyare miki kan ki dama sauran gurare zaki ji kinyi fyes abin ki. Gaki da yalwar gashi tubarkAllah.”

“Tab Malama ai gahin kayi na ya hya sharba Malama, Na takwas kenan. Domin da ya iheni da kaikayi zan je a saisaye hi, Hima dan anacen ba’a runtse hekara zai kara cika fiye da na baya.”

“Wasu na nema wasu na aske nasu. Toh anyi an gama ba zaki sake aske kanki ba Khadija. Yanzu dai bara na rokar mana Malam Auwal ya kyale ki ki koma aji. .”

Tafiya tayi ta ta nufi wajen Malam Auwal, Yana tsaye yana mulmula goshin sa inda ya bige, Ya kumburo yayi suntum. Yana kallon kansa ta wayar salula,

“Sannu Malam Auwal.”

“Sannu Malama. A gaskiya ki san yadda zaki kiwa headmaster magana ya canzamin ballagazar yarinyar can a ajina. Gaba d’aya na tsaneta tsana mai wuyar fassarawa, Sam batada kamun kai. Yadda kikasan tababbiya haka take abubuwan ta.”

“Kayi hak’uri Malam Auwal. Sha’anin Khadija sai ahankali, Yarinya ce data taso da rashin uwa, Tun tana kankanuwa mahaifiyar ta tarasu, Rikon ta ya koma hannun kakarta, Ka kuma san wani goyon kakar yadda yake, Ballantana nan kauye. And still wahalar bata k’are ba Malam, Babanta ya Kara aure, Na takaita maka zance dai a hannun kishiyar uwa take. Kishiyar uwar kuma tazo da agola. And baban ta bashi da say. Tamkar ba shi ya haife taba, Matar tagama dashi. So Khadija tana yin wata irin rayuwa ne mai ban tausayi, Shi ‘da na kowa ne, Shysa nakeson na temaka mata wallahi, Ko Allah zai dube ni ya bani nima mai jin kai. Banason wannan abun ya shafi kwakwalwar ta yasamata psychological trauma Idan ta manyanta.
Chapter 13 · 0% Book details