Sashe 113
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Insha Allahu zan kiyaye, yanzun ma matsalar da aka samu shine babyn na ganin furar aka fara nuna min ana cewa za'a sha. Kuma fa ban jima da cin abinci ba, amman kaga hadama.”
“Babu komai indai fura da nono ne bari nasa Falaki ya kawo miki mai rai da lafiya.”
Nayi murmushi tare da kwanciya kan kafadar shi Ina tuna wani labari da nake karantawa, yadda mijin yake wulakanta matarsa saboda kawai tayi ciki shi kuma be shirya haihuwa da wuri ba. Sabanin Salman dubi yadda yake tarairayata yana bani kulawa ninkin wacce yake bani kafin cikin. Sallamar Umma Hansatu ne yasa shi saurin dago min da kai, nuni ya yi min da zai gudu yana cewa.
“Bana son asan da kofar nan shi yasa.”
Na gyada kai Ina masa dariya ganin yadda yake sand'a tamkar marar gaskiya. Sai da na tabbatar ya shiga ya rufe sannan na tashi Ina amsa sallamar da take yi.
“Umma ki shigo mana.”
“Au to ai naji ba a bani izini bane shi yasa Gimbiyar mu.”
“Ai kuwa tunda kikai ta farko nake ta amsawa Ina shigowa bakiji bane.” Na fada cikin son dauke mata hankali da wani hasashen a kai na.
“Kinga barna nayi shine nake kokarin gyara gurin.”
“Asha ai da kin bari nazo nayi, yanzu ma tunda Allah ya kawo ni, Sai kije ki zauna na gyara ranki ya dade. Ga kilishin kuma tace duk Abdullah ne ya kwashe bata kula ba sai gani tayi yana ci.”
“Allah sarki Ammi na, shi kuma Abdullah yaci rabon shi.”
Muka sanya dariya saboda yanayin yadda na karasa maganar cikin wasa. Ita kuma ta gyara gurin tas ina gefe ina cin kilishi na. Bayan ta kammala ne da na tashi zan shiga toilet na tafi da ragowar furar na zubar tare da wanke kofin Ina dad'a yiwa Allah godiya da ya kubutar dani wannan tuggun. Ina fitowa na kuma hayewa gado na zauna Umma Hansatu tana bani labarurruka na ban dariya, ashe duk Salman yana ganin mu sai text message d'in shi na gani yana cewa.
“Masha Allahu love.. kina da cute smiling face, idan kika yi dariya kuwa ina kasa controlling kai na, I love you so much.”
Ban san lokacin da na kuma sakin dariyar ba Ina rufe fuska dan nasan kallo na yake yi a inda yake, Umma Hansatu kuwa tayi tunanin duk cikin labarin ta ne yasa nake kuma jin nishadi. Ta kuma gyara zama tana rattattako wasu labaran...
<>>€><>
Gaba d’aya zancen cikin dije ya gama karade masarauta da abunda ke cikin ta, Kowanne bangare maganar cikin suke yi, An sawa dije da cikin ta idanu. Sihiri, Makirci da tsantsar bakin ciki. Gaba d’aya ahalin masarautar suna cikin dimauce, Farautar ran dije suke da dan cikin nata mararan.
**** Waziri kuwa gaba d’aya ya zama tabbabbe a zuci, A Zahiri kuma ya zama wani birkicacce. Ya dena zuwa fada saboda bakar mugunta yace bai da lapia ne. Nan kuwa kullum cikin tsara surkullen yadda cikin dije zai zube yake yi. Shida su Chiroma basu hakura ba suka sami wani garin maganin awajen yar mai ganye. Ya samu wani amintaccen hadimin sa ya kai maganin cikin sashen Khadija, Aka faki ido aka barbada a miyar da Umma Hansatu keyi. Ba masaniyar abincin bana dije bane na Umma hansatun ne. Kwanan Umma Hansatu 3 tana ciwon ciki dakyar ta farfad’o, Tun daga lokacin kuwa SAS ya hana dije cin abincin masarauta baki d’aya, Saboda a kayan abincin ma Za’a iya hada baki da wani ya zuba maganin cutarwa. Shiysa kullum sai dai ayi mata takeaway a boye taci.
Waziri kuwa an sanar masa tabbas Dije taci abincin nan, Sai jira yake yaji ana koke koken ta margaya, Yanzu abinda suka sa a gaba shine gaggauta cire Salman daga karagar mulki. Da daddare bayan sallar ishai suka taru a bangaren Mama Huwaila, Waziri ya tattauna abunda ya kawo su, Kafin ya cigaba da cewa,
“Sai kuma matar sa ta farko, Gimbiya shaheedah, Duk itace ta kawo mana cikas, Kan ai Salman baya haihuwa. Bashida ishasshiyar lapia. Nace a mana iso da ita nan ta mana bayani don mu ba mutanen banza bane. Domin gaba d’aya na tattara dik hujjojin da muka tsara nayi su a rubuce zamu aikawa gwamna ya tsige shi daga kujerar sa..”
Yana rufe baki, Parlorn ya d’auki magana baki daya, Dukkanin su sun hallara anata tsara yadda za’a tuge Salman a kujerar sa. A babban parlorn mama Jaleelah sukai zaman. Ba jimawa shaheedah ta shigo kanta a kasa tana raba idanuwa. A tsorace take ainun, Sai dai dake tana ji da kambun mulki ba zaka gane ba saboda yadda take yauk’i.
“Barka da zuwa sarauniya.. Takawar ki lapia.”
Kowanne ya shiga mata kirari, Su wambai, Waziri, chiroma, Galadima, Makama da sauran yan parlorn.
“Barkan mu.. Waziri ga ni! Ina fatan lapia?”
Ta karasa fada tana duba agogon hannun ta.
Waziri yai murmushin gefen baki yana sakkowa daga kujerar daya ke zaune,
“Allah shi taimaki gimbiya.. Wani abune muka ji, Daya sanya zukatan mu a rudani, Mun ‘karyata a baya, Amman da muka tsananta bincike sai aka tabbatar mana da gaske ne. Shine mukeso muji gaskiya ta bakin ki..”
“Ban fahimce ka ba Waziri! Sanar mun abinda ya jefa zukatan ku a rudani..”
Waziri ya sake rissinawa yana dan daga murya,
“Maganar... Juna biyu da Khadija ke dauke dashi mana.”
Da sauri shaheeda ta mike tana dafe kirji,
“Juna biyu? Wacce khadijan? Wake dauke da shi? Bangane ba.”
“Au.. Ina nufin gimbiya khadija mai dakin mai martaba Salmanu na biyu.”
“Waziri!! Shin abunda kunnuwana suke jiye muni dagske ne ko kuwa? Don wane Salman din? Inde mijina kake nufi na yanzu to gaskia wannan zancen kanzon kurege ne, Domin salman baya haihuwa, Baida ishashshiyar lapiar da har wata acikin mu zata dau cikin sa. Sai dai idan awaje ta samo shi.”
Waziri ya juya yana duban sauran yan parlorn dake bin shaheedan da kallo kamar wata gaula, Domin hajjajun su tace komai rintsi ta tubure kan lallai batasan da zancen cikin Khadijan ba. Waziri ya numfasa,
“Kina nufin kice mun bakida masaniya akan juna biyun da take dauke dashi na mai martaba?”
“Zan maka Karya ne waziri?”
“Tuba nake ran ki ya dad’e, Lamarin ne da mamaki. Amman tunda ke kanki kince baki da masaniya inaga mu kuma.”
Shaheeda ta dafe hannuwanta da goshi , Irin tana cikin jimamin nan,
“Idan ma dashi din... Toh lalle bana Salman bane, Tunda kunga zahiri a yawon asibitoci da mukayi na duniya.”
Waziri ya gyada kai yana kallon galadima. Galadima ya amshe zancen da,
“Toh wacce gudunmawa zaki bamu?”
“Wacce iri kuke nufi galadima?”
“Gudunmawa dai wadda zata temaka wajen kamo bakin zare, Wadda zamuyi amfani da ita wajen tarwatsa ita ... Abokiyar zaman naki.”
Da jin haka sai ta zauna, Kasa kasa tashiga magana.
“Zan bada...Akwai general checkup results gaba d’aya wanda muka jajje da Salman, doctors ba adadi sunyi binciken su akan mu, An kuma gano shine mai matsalar.”
Chiroma ya sake matsawa tsakiyar parlorn yana rissana mata, Kamar yadda Waziri ya tsara musu su tattambaye ta.
“Allah yaja zamanin ki, A yaya sakamakon ya kasance? Takaddu ne ko kuwa?”
Shaheedah ta dan yamutsa fuska tana taune kasan leben ta.
“Duk abinda zai bada cikakkiyar gamsasshiyar amsa, Zai bayar, Domin akwai papers dake dauke da rubutun likitocin, Akwai fefan bidiyo dake dauke da bayanin komai, Sannan akwai sautin muryar likitocin wanda duk suna adane..”
“Alhamdulillahi ranka ya dade kana ji ko?”
Waziri ya gyada wa Chiroma Kai fuskar sa dauke da murmushi,
“Lalle gimbiya kin biyamu, Mungode kwarai. Wannan results din da zaki bamu dasu kadai zamu iya tsige yarinyar can daga zuciar Salman dama masarauta baki d’aya, Idan ta kama ma mu rabata da iska.”
SHAHEEDA dadi ya shiga ratsa ta tamkar ta tashi ta taka rawa don farin cikin jin Za’a fitar da Khadija daga gidan koma akashe ta baki d’aya. Waziri ya sake jinjina mata yana kakaro murmushi,
“Mungode kwarai matuk’a sarauniyar mu. Allah yaja zamanin ki. Sai ki bayar akawo mana.”
Mikewa shaheeda tai bayan ta daga kanta alamun Toh, Ficewa tai hadiman dake jiran ta awaje suka rufa mata baya. Tana futa su waziri suka tasa fefanta suna yi da ita baki dayan yan parlorn.
“Rabu da ita, Itace babbar munafukar data fara ‘bata mana wasa, Na karairakin shine baya haihuwa ba ita ba, Ina sane na sako zancen futar da Khadija kadai ba tare danace tuge Salman gaba d’aya ba..”
“Kwarai kuwa Waziri, Nima da fari nayi mamakin fad’ar hakan da kayi, Sai daga baya nagano lob’a ta kayi.”
Cewar wambai dake gefe yana cin tufa. Haka dai sukaita tofa albakacin bakin su, Lokaci zuwa lokaci su Mama Huwaila kansa baki. Ana cikin tsara yadda komai zai kasance yareemah abdulqadeer ya fita da waya a kunnen sa, Can ya dawo fuskar sa babu walwala.
“Baba Waziri..”
“Na’am Makama.”
“Wata magana ce maras dadi aka sanar dani yanzu.”
Waziri ya zare idanu yana bin yareemah abdulqadeer da kallon karin bayani,
“Meya faru kuma?”
Bakin sa na rawa ya shiga gaya musu komai,
“Khal... Khaleel dake Korea, Wanda na dora akan motsin sa yau yake sanar mun wai kwana biyu bayajin dadi....”
Ai bai gama fada ba Waziri ya katse shi,
“Khaleel dinne ba lapia?”
“Noo! Shi wanda na saka ya dinga dakko mana rahotan Khaleel dinne wai baida lapia, Sai da ya kwanta a asibiti, Bayan an sallamo shi yaje gidan da Khaleel din yake..wai baya nan, Yaje asibitin sunce yayi resigning tun tuni, Yabi diddigi ance ya bar k’asar.”
“Zancen banza, Zancen wofi. Wambai, Galadima kuna ji ko? Wannan wani renin hankali ne na daban da za’a kawo mana kuma, Khaleel din da aka kafe shi shekara da shekaru ta ina har ya iya barin K’asar duk bamu da masaniya Sai yanzu? Toh yana Ina? Nace yana ina?
A hasale Waziri yake magana yana kallon abdulqadeer, Mikewar shima yayi yana tada jijiyoyin wuyan sa, Dama shi kunya bata isheshi ba,
“Okay zan maka Karya ne? Gani kake duk hadin zance ne? Zan hada kai da Khal ne na cuce ka? Lalle kabani mamaki, Amma banyi wani mamaki can ba gaskia domin na lura bakada yad-da. Zanyi maganin ka nan kusa.”