Sashe 19
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hijabi na na janyo sabo fil dashi Bara’atu ta dinka min, Wuta ta ruru na zubata a dutsen guga, Cikin kwanciyar hankali na shiga goge hijabi na. Na kammala na shasshafa turaruka masu sanyin k’amshi dana siya a shagon Falalu.Ban tsaya wata kwalliya ba na dai goga farar hoda da basilin a lebe na. Gashi na mai matukar tsawo da cika naita ko’karin daurewa, Dak’yar ya dauru. Domin ina daure shi yana kuncewa saboda santsin sa, Ko kitso ake min kasan na warwarewa. Zura hijabin nayi, Na goggoge takalmi na samfarin sandal. Safa tama sabuwa ce sai sheki take. Wajen Baffa na nufa na coka biro a gefen kunne na, Ji na nake on top yau zan kammala sakandire, Sai kuma fanni na biyu.
Yana malale a taburma kamar ruwa, Dakyar yake iya magana. Gajiyalle na gefen d’akin girki tana kwashe tuwo. Na san ba zata bani ba bare Baffa na. Domin tunda rayuwa ta ta sauya daga bak’a izuwa fara Gajiyalle ta dena bani abinci, Duk abinda zan sanya a ciki na tadena min shi. Ko banda hantara da kyara yanzu babu abunda ke shiga tsakani na da ita. Zan gayshe ta Sau dubu ba zata amsa ba, Sosai take jin haushin karatun da nake yi. Kullum cikin yada min da magana take. Kan naki aure ina yawon ta zubar, Ga k’awaye na nan duk sun hayayyafa. Ni da Siyama da Uwande da Nafisa ne kadai ke yin karatu yanzu a sa’oin mu. Gaba d’aya sunyi aure sun tara yara. Ajiyar zucia na sauke ina kallon Baffa na, Dama ance sai ka rasu ake gama canza maka halitta. Yanzu Kalli Baffa da sumul k’alau yake. Tashi d’aya ya samu wannan ciwon,
“Baffa na..! Sannu ya jikin naka?”
Baffa ya lumshe idanu ya bud’e alamun lapia. Kafin ya bude bakin sa hankali,
“Allah... Ya bada sa’ar jarabawa Ummi na.!”
“Aamin Baffa na! Allah ya tashi kafad’un ka yasa kaffarane.”
Rufe idanu yai. Na mike dakyar jikina duk yayi sanyi.
“Na tafi Gajiyalle.”
Harara ta dankaramin ta cigaba da kada miyar ta.
“Na tafi jarabawa Gajiyalle.”
“Ko an tafi yawon ta zubar ba. Mude kada a kawo mana abun kunya gida, Atoh!”
Girgiza kai kawai nayi na fice rai na babu dadi. Nera dari da hamsin din hannu na na tsaya na mikawa Safarau me sayar da abinci,
“Gashi ki zubamin a kwanon jiya ki wanke dan Allah sauri nake zan tafi jarabawa, Idan na dawo zan tsaya na karb’a.”
Saurin Karb’a tayi ta koma wajen zaman ta. Iyayen ta sun hanata karatu sai dai tallen abinci, Wai ta haka zata tara kudin kayan daki. Abun takaicin ma mazan yar kasuwa sun mai da ita tamkar matar su. Su yita bata kudi suna taba ta. Haka na shige da tunanin da safarau ke ciki na tafi makaranta. Lalle na godewa Allah daya kadarta za’ai makaranta a kauyen mu, Da hakimi daya samo mana tallafin yi, Dama mai gari daya wayar da kan dattawan karkarar mu, Sai Baffa na, Jigon rayuwa ta. Wanda ya tsaya min a komai, Ya so ni bai kyamace ni ba kullum cikin min adduar shiriya yake. Ga bani shawarwarin yadda rayuwa ke ciki. Da yadda zan gudanar da al’amura na ba tare da na gunduri kowa ba. Bayan Baffa na sai Malamai na. Musanman Malama Mardiyya data dauke ni tamkar ‘yar data haifa, Itace mace ta farko data gyaramin rayuwa ta. Gaba d’aya acikin duhu nake. Zuwan Malama Mardiyya shi ya samar da yadda na zama a yanzu. Ba abinda zance da kowa sai fatan alkhairi.
*_GOVERNMENT JUNIOR/SENIOR SCHOOL DURBUN*_
Kide kide muka fara da bencina muka d’akko muka kawo su farfajiyar makaranta, Yau munyi candy. Mun kammala makarantar secondary. Allah mungode maka. Wakoki muka fara na candy, Muna yi fuskokin mu dauke da farin ciki da annushuwa,
_2005 muna tare, 2006 muna tare, 2007 muna tare.. 2014 zata raba mu. Malam Auwal mude kayafe mu, Mude mun yafe, Muma ka yafe mu, Malama Mardiyya mude kiyafe mu, Mude mun yafe mu de kiya fe mu..🎶_
Haka Mukai ta yi har akazo kan sunayen dalibai, Nima na mike ina hawaye,
_Khadija Basheer Inuwa inayin ban kwana, Nide ku yafen, Nima na yafe ku.🎶_
Ina k’arasawa na fashe da kuka, Saura na ban haku’ri, Mu kaita koke har aka kammala, Aka babbawa prefects kyaututtuka. Ni ce ‘sanitary prefect’ kasancewar nafi kowa tsafta. Domin tunda na Kile na koma yar gayu, Har kawaye na ke kira na da ‘Dije wanka-wanka’ Idan zanzo makaranta ko banida kudin guga tun dare nake yiwa uniform dina ninkin guga na kwanta akai da safe kuwa sai kuga sunyi ‘das dasu tamkar nasa dutsen guga.
‘’ Ina sanitary prefect? Nana Khadija Basheer..”
A hankali na mike daga zaunen da nake na isa gaban makaranta inda Malam Habu ke kiran mu dai-dai, Sunana ya tashi daga Khadija Baffa ya koma na ainihi wato Nana Khadija Basheer. Tun a Jss3 na canza lokacin da mu kai jarabawa. Malam Auwal na gefen Malam Habu yana min wani kallo tunda ga sama na har kasa,
“Dan iska...”
Na furta ahankali ina gatsine baki. Murmushi yai yayi magana da labban sa bansan meya ce ba. Malam Habu ya dankamin kyauta ta, Na tsaya muka dauki hoto da sauran malaman kamar yadda ake da kowa. A haka aka kammala komai bayan anyi walima mekyau. Mardiyya bata bari mun kara sallama ba ta tafi bayan ta dankamin number wayar ta a paper, Kan cewar zata dawo ta dauke ni muje birni nayi jamb. Nasan idan muka kara had’uwa kafin tafiyar ta sai nayi wani sabon kukan itama haka, Shi yasa ta tafi. Amma Malam Auwal ya ki tafiya yananan ya kasa ya tsare. Da wani Malamin ya kira wo ni zai dakatar da ni. Sai kace wani miji na.
Ko ta kansa ban sake bi ba, Na bi su Uwande muka dauki hanyar gidan su ganin kayan barar ta da aka kawo, Kamar hadin baki Siyama ma jibi Za’a kawo nata, Nafisan kansila kuwa an kusa bikin ma, Wani dan uwan su na birni zata aura yanada mashin dinsa Lifan. Ni kuwa ko oho. Banda Malam Auwal da kama sunan sa haushi yake bani ma sai Mubarak dan gidan Bala driver, Shi kuwa babar sa ta dira tsallen albarkar danta ba zai auri wadda tai boko ba. Muna tafe a hanya ina tunanin duniya, Malam Auwal ya shiga zabga min kira tamkar wadda naci bashin sa na gudu. Nifa gaba d’aya haushi yake bani, Ada babu wadda ya tsana iri na, Yana kallo na tamkar kashi. Duk abunda nayi bana birge shi. A kullum cikin kuntata min yake. Amman yanzu ya nanike min kamar super glue. Duk inda nai bina yake sai kace rak’umi da akala.
“Na’am..”
Na amsa masa bayan ya kira sunana a karo na ba adadi. Ya sake marairacewa yana zuba hannayen sa a aljihun jeans dinsa,
“My Baby K! Meyasa kike wahalar da zuciar masoyin ki ne? Na gaya miki tunda Allah yasa son ki ya mamaye bargon jiki na da tsoka, Kullum da begen ki nake kwana nake ta shi. “
Namiji mayaudari ji wata karya dan Allah! Duk da a k’auyen kayau na tashi, Naki jinin irin kalaman soyayyar nan. Konamin rai suke. Gashi duk karyar banza ce. Don takaici rasa me zance masa nayi.
“Baby K!”
Wai Baby K! Kamar wata diyar cikin sa. Murtuke fuska nayi na juya gefe ina dagawa su Uwande hannu alamar su tsaya ni kar su tafi.
“Malam Auwal jira na ake..”
“Naki jinin yadda kike ambatar sunana Baby K! Ni ba malamin ki bane, Masoyi ne agare ki. Ki tallafawa zuciya ta ki karbi kokon barar soyayyar ta. Shekaru nawa ina rokon ki, Ya kamata ace kin tausaya min, Gashi yau zan koma inda na fito. Kuma ba naso na koma batare da kwakkwarar amsar ki gare ni ba.”
Ajiyar zuciya na sauke, Ni kai na nagaji da kulaficin da yake yi min, Mutumin da sam baisan darajar dan adam ba, Rashin mutuncin da yai wa Baffa na bazan taba mantawa dashi ba, Yazo zance Kwana ki, Baffan mu ya fito zai tafi gona da y’ar fatanyar sa bai ko kalle shi ba. Ina tsaye ina gwada hankalin sa. Dana tambaye shi meyasa bai gaida wanda ya wuce ba? Wai ya dauka me gyara ne. Gyaran uwar baban sa? Ranar naci masa mutunci sala-sala bansan meyasa baida zuciya ba ya nanuke min.
“Kayi hak’uri Malam! Gaskia bana ra’ayin soyayya, Karatu zanyi. Allah ya baka wadda ta fini komai. Ina maka fatan alkhairi. Allah ya kiyaye hanya.”
Ina gama fada nai gaba abuna, Na barshi a tsaye ya sandare. Mukai tafiyar mu dasu Uwande, Wannan itace rana ta karshe tsakani na da Malam Auwal. Ina wa dukkanin mu fatan alkhairi a rayuwa. Muka je gidan su Uwande muka gano kaya, Wallahi Uwande tai goshi, Kaya nasha-nasha. Daga nan na tsaya na karb’i abincin dana bada Kud’i dazu, Gida na nufa, Ina shiga na hango Baffa na a inda na barshi ya kwarara amai yana numfarfashi dakyar, a sukwane na zubar da kyautar hannu na kwanon kuma na ajiye a gefe na shek’a da gudu na isa wajen sa ina tallafo shi da karshen karfi na,
“Baffa na...! Sannu! Amai kayi! Sannu! Jinjiri (Almajirin dake kula dashi Idan na tafi makaranta ko bana nan) bai zo ba? “
D’ankwalin hijabi na nasa na gogge masa fuskar sa, Kafin na debo ruwan dumi dana ke had’a masa shayi na surka na gogge masa jikin sa, Riga na d’akko na sauya masa da Wadda ya b’ata, Ina ta faman masa sannu. Gajiyalle ta fito daga d’akin ta tana wake wake, Ta shiga kitchen ta ebo abincin ta ta wuce ko kallo bamu ishe ta ba. Ni bansan meyasa Baffa ya auro taba. Silar ciwon sama itace ta haushi da kokawa ya zume a bandaki.