← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 114

Sashe 106

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Eh mun koma, Canjin aiki akaiwa Abban su, Kai Masha Allah! Gidan ki yayi kyau Khadija.. Kinga ribar hak’uri ko? Ai nagaya miki akwai rana irinta yau da zaki bani labari.”

Nayi daria kawai nima ina bin parlorn da kallo,

“Ai kuwa dai kin fada malama..”

Na dan bata labarin auren a takaice, Hararata Malama Mardiyya tai tana danna cinyar kaza abakinta,

“Yimin shiru kafin na zane ki.. Da alama a makaranta na manta ban taba dukan ki ba, Kila sai yau. Yo ai babbar sokuwa se ke.”

“Meyasa kikace haka Malama..?”

“Saboda ba yadda za’ai dan ya tsaneki ne zai auro ki ya narka miki wannan gidan da uban dukiya duk ke kad’ai? Ahh sannu, nace sannu.”

“Hmm! Malama bakisan wahalhalun rayuwar dana shiga bane.. Jini fa Malama, jini aka sakarmun naita shan wahala na dauka period ne. Ka tsorata, Da yawan jin wari gaba d’aya banajin k’amshi. Ga rashin bacci da faduwar gaba. Malama nasha wahala.. Amma dai Alhamdulillah komai ya wuce.”

“To ai Alhamdulillah tinda yanzu komai ya shige. Insha Allah komai yazo karshe Khadija. Ai ke din *KIBIYAR AJALI* ce, Wadda sulke baya tare ta sai ta wuce.. Kiga tsallake tuggun Gajiyalle ma bare nasu? Yo me zasu miki? Kedin wacce iriyar gwagwarmayar rayuwa ce baki gani ba? Wanda da Allah ya kawo k’arar kwana ma da yanzu sai labari.. Amma gaki nan tamkar me ran k’arfe. An buga dake an barki ya zasuyi dake uhm? Sai kallo daga nesa yar kanwata.”

Nayi murmushi kawai.. Inata tuno sanda taketa wahalhalu da ni a Durbun.

“Tunanin me kike Khadija..?”

“Babu komai Malama.. Kawai na tuna baya ne.”

“Kai abincin nan yayi da’di... Yau gani a gidan Khadija na.. An cikamin gabana da kayan kwalam da makulashe na gidan yan gayu..”

Nayi daria kawai ina lankwasa hannaye na,

“Ni kam ina Malam auwal?”

“Wai wai Wai.. Allah sarki Auwalu.. Wai.. Ai inaga rabona dashi wajen shekaru biyu kenan. Yace dani zai koma can shagamu dangin mahaifiyar sa zaiyi aure ya kuma fara kasuwanci, Saboda teaching dinnan ba inda zai kai shi..”

“Allah sarki Malam Auwal.. My first love..”

Muka sheke da dariya.. Malama mardiyya tacigaba da cewa,

“A’ina ya zama first love din naki? Mu da kika ‘kimu..? Kai Allah sarki shima auwal seda na ce masa karfa kiyayyar da kakewa Khadija ta juye ta koma soyayya yace aa wallahi.. Sai gashi yana roko na wai dan Allah naje gidan ku a bashi ke ya aura.. Nace wa? Badani ba wallahi..”

“Allah sarki Malam auwal..”

“Ya durbun..? Kin koma kuwa?”

“Aa wallahi tun bayan tahowata ban koma ba.. Zan je, Amma sai nan gaba kadan.”

“Allah ya kai mu. Allah ya dafa miki ya dora ki akan makiyan ki Khadija..”

“Aamin Malama mardiyyah..”

“Ko sai kin sauka lapia ba Insha Allah..”

Na rufe fuska ta da tafin hannu wai ni kunya, Malama mardiyya tacigaba da cewa,

“Ai kinsan rannan sai bayan tafiyar ki naita dana sani nace ko number ki ban karba ba, Toh Ina can ina mamakin wayewar yar k’anwata.. Ubangiji Allah yasa mutu ka raba keda mai martaba Khadija, Aita haku’ri, Rayuwar aure gaba d’aya hak’uri ce.. Kinji?”

Hira muka shiga yi sosai da Malama tacigaba da bani shawarwari akan zamantakewar aure, Na Karu Sosai da bayanan ta, Kamar a makaranta haka tadinga mun bayanin komai dalla dalla, Mun jima muna hira sosai ta kakkawomun magungunan mata irin na yoruba dinnan, Da turarukan wuta kai harda na mopping da wanki da wanka na *yerwaincense&more..* Allah sarki bata masan inada wasu turarukan ba na yerwan.

Nima na hau sama na hado mata shatara ta arziki domin Malama mardiyya idan ka cire kawunina da suke a raye da Salman da Ammi sai ita a wanda nake kauna gaskia. Zan iya cewa ma banda sama da ita ta wani fannin.

Har bakin gate na rakata, Kowannen mu fuskar sa dauke da hawaye haka muka rabu.. Domin jirgin safe zata bi ta koma birnin ikko. Amma tamun alkawarin zata sake dawowa Insha Allah, Nima nace mata idan na sake ziyarar lagos zanje wajenta tunda mun karbi lambobin juna....

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B30_

*GIM. SHAHEEDAH...*

Abubuwa ne suka taru sukai mata yawa. Ta kasa gane kan Salman, Duk sanda zata sa amata iso sashen sa sai ace sarki ya hana kowa shiga yana wani uzuri, Sai daga baya kuma yazo da kansa, Idan yazo kuma babu wani abu dake shiga tsakanin su sai dai ya tsiri dakko ipad dinsa yace wani aiki yake yi, Daga karshe tatashi tashige daki idan tafi to kuma baya nan ya tafi.

“Salman me kake boyemin ne?”

Ta tambayi kanta tana nazarin duk lokutan da suka ha’du uzurorin da yake bata duk d’aya ne, Gashi tamkar an sauya masa halaye. Babu wannan yawan ciwukan da yake. Kuma kullum kamar ransa a bace yake yana kokarin danne wasu abubuwan.

“Salman me yake faruwa ne...?”

Ta sake jefo wata tambayar tamkar shidin ne agaban ta. Mikewa tai tsaye tana kiran sadiya hadimarta,

“Ga ni ranki ya dade...”

“Sadiya... Kin bincika abunda na sa ki?”

“Nayi uwar daki na. Tabbas ance gimbiya kh...”

“Karki kuskura ki karasa sunan gimbiya kaza, Wacece gimbiya? Ta ina tazama gimbiya? Sama taka? Kodan an dosanata a ta biyu? Mata ba jinin sarauta ba komai ba, Yar kauyen kayau. Kizo gabana kina kiranta da gimbiya? Karna kara jin labban ki sunyi gigin kiran Khadija da gimbiya.. Kina ji ai ko?”

“Na fahimta gimbiya, Akasin labbana ne, Tuba nake ranki ya dade, Allah ya huci zuciar ki...”

“Sanar dani abunda kika jiyo.”

“Ranki ya dade.... A binciken danayo na kuma harhada da wanda akawo mun an tabbatar mun kh.. Khadija na nan cikin gidanta babu inda taje, Domin ance Umma Hansatu hadimar mai babban d’aki itace ke zaune da ita acikin gidan. Wasu sunce tayi wata bakuwa kwanakin baya harta rakota ma izuwa gate din sashen na su... Kuma ance takara murjewa tayi b’ul b...”

“Ya isa! Jeki.”

Sadiya ta mike ta fice, Shaheeda tai zaman yan bori tana jujjuya kai,

“Takara murjewa tayi ‘bul ‘bul... ?Hakan nada nasaba da Salman kenan? Shysa muke wasan ‘yar buya da shi? Nooo it can’t be.”

Waya ta janyo har zata kira hajian su sai kuma ta fasa, Tatafi wajen su Mama Huwaila ko zata jiyo wani labarin awajen su.

*GIM. KHADEEJAH.*

Ina zaune bayan nagama karatun alqur’ani, Waya na janyo na dan fara karanta hausa novels na online, Can na ajiye na koma parlor na zauna jira nake Umma Hansatu ta dawo daga gaisar da Ammi data je. Ba jimawa kuwa ta dawo, Sai dai yanayin fuskar ta gaba d’aya ya canza.

“Umma Hansatu lapia?”

“Lapia qalau ranki ya dade, Da akwai abunda kikeso ne yanzu na tashi nayi?”

“A’ah babu komai, Ya Ammin? Kince ina gaishe ta sosai ko?”

“Kwarai na fada Allah ya kara miki lapia, Tana amsawa sosai tace tanai miki ya jiki. Tayi miki adduoi sosai..”

“Masha Allah, Ina godia kwarai da gaske, Duk kalau suke ko? Kwana biyu inata kiran wayar ta bata shiga.”

Umma Hansatu tayi jim tana jujjuya kai,

“Menene Umma Hansatu?”

“Babu komai ranki ya dade.. Tace dai karna fada amma bazan iya kin fada miki ba, Uwar dakin nawa na kwance itama ba lapia.”

“Ammin..?”

Na tambayeta a matukar dimauce, Gyada Kai tayi cikin tabbatarwa.

“Zazzabi ne, Tashi wai taifol ne (typhoid).”

Mikewa nai na shige da’ki, Na kasa samun nutsuwa na kikkira Abdullah wayar sa off. Dan haka na kira Salman bai daga ba. Wunin ranar haka na wuni duk banjin dadi. Dakyar bacci barawo ya dauke ni ban farka ba sai tashi nai naji ana kiraye kirayen sallar magriba. Bandaki na shiga nayo wanka da alwala. Nayi sallah na Idar ina zaune akan dadduma Salman ya shigo,

“Barka da dawowa...”

“Barkan mu Zawjati.. Ya jikin naki? Ai na shigo naga kina bacci na koma.”

“Eh wallahi banmasan ya dauke ni ba, Da ina kasa tare da Umma Hansatu..”

“Okay! Kinci abinci? Me kikeson kici uhm?”

“Babu komai.. wai Ammi ba lapia? Ko bakasani ba kai ma?”

“Kai wannan Umma hansatun ta aminta dake, Ammi fa ta gargadeni kada na gaya miki, Ashe Sai da Umma Hansatu ta gaya miki?”

“Meyasa Za’a boyemun rashin lapian Ammi? Why?”

“Bakomai... Ammin ce tace dan karki tada hankalin ki ne, Wajen kwanaki uku kenan tana zazzabi a tsaitsaye typhoid ne da malaria.”

“Allah yabata lapia yasa kaffarane.”

“Kinason kije kiga jikin tane?”

Da sauri na gyada kai ina komawa kusa dashi, Ya janyo kafadata yana rungumeni,

“Idan aka idar da sallar ishai sai kuje da Umma hansatun, Tunda naga kin damu da yawa. Kinsan wani abu kuwa?”

Na girgiza kai ina kallon sa,

“Yau birthday din Ammi, Yau ne ranar da aka haifeta bazan taba mantawa ba, Mai martaba da kansa yake tsara celebrating birthday dinta duk shekara...”

“Allah sarki, Allah ya gafarta masa. Mezan bata as present?”

“Karki damu na riga na shirya komai nasa an kai inji ki, Nine tawa kyautar sai kunje zakiga wata iri zan bata.”

“Dan gayamun mana.. Haba Zawj..wayo?”

“Khal.. Khal zansa ya kirata su gaysa. Kinga dai shine wannan babbar kyauta duk duniya da Ammi zata fiso.”

“Gaskia kam, Kai Allah sarki Ammi..”
Chapter 106 · 0% Book details