Sashe 18
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“A takaici wannan hadisin na ko yarda mu yadda ake yin wankan tsarki ne, imma (janaba, haila, biki, Wankan Juma'a da sauransu). Yara idan kun tashi za ku fara ne da wanke hannayen, sannan ku yi tsarki da hannun hagu tare da wanke duk inda najasa ta ta6a, sannan sai ku yi alwala kamar yadda aka saba yi idan za a yi sallah, sannan sai ku wanke gashin kanku tare da cuccudawa, ku sanya yatsunku har zuwa kasan gashin sau uku, sannan sai ku game jikinki da ruwa. Babbar manufar dai shi ne ya kasance ruwa ya isa kowani lungu da sako na jiki, don haka duk inda aka ga ruwa be isa ba, sai a isar da shi. Kun fahimta?”
Nayi saurin cewa.
“Eh to, wani gurin dai sai an sake gaya mana.”
“Toh shikenan duk wacce ta fara ko take yi tazo ta same ni ta gaya min kunji?”
Duk muka hada baki wajan cewa.
“Eh...!”
Daga nan ta ci gaba da sanar damu yadda zamu dinga tsabtace jikin mu har aka tashi gabaki d'aya. Muna cikin fitowa daga aji ni da su Siyama muka hadu da malam Auwal na bishi da kallon sama da kasa, yasha kananun kaya farar t-shirt da dogon wanda jah ya yi kyau sai dai ji nake na fishi hakan yasa na kuma gyara mayafi na.
“Zonan Khadija.” Ya kira ni.
“Gani malam, amman kayi sauri saboda wallahi yunwa nake ji.”
“Haka dai. Daga ina kike ci ina zaki ci.”
Yai maganar yana jajjan gemunsa.
“Yooo ai lafiya ce ta iheni ba dan haka ba ai bazan ci ba, kai ma malam wallahi da zaka dinga rage ciki kana cin abinci da he kafi haka kauri.” Sai ya share maganar ta hanyar cewa.
“Ina uniform dinki?”
“Suna gida malama tace sai na wanke zan saka.”
“Toh karki sake zuwa mana da kayan kida.”
Na yatsina fuska alamun banji ba bazan dena ba, shi sai kace makarantar shi duk yabi ya takurawa yan makarantar kowa tsoransa take ji. Na turo baki ina zaro kudi na daga inda na boye ina cewa.
“Malam in rafi?”
“A'a zo muje wajan mashin dina zan baki abu.”
Ya yi gaba ba tare da ya saurare ni ba, na harari bayan nasa ina bin shi.
Bude mashin din ya yi ya dakko wata bakar leda a kulle ya miko min tare da cewa.
“Idan kinje gida kici.”
Tunda ya ambaci naci nasan cewa kyautar tawa ce.
“Malam na gode Allah ya himaka albarka.”
Ya yi murmushi banji ya amsa a fili ba amman ina tunanin ya amsa a cikin ransa. Ai banma bari naje gida ba, kawai na samu guri na bude ledar, naci karo da gassashiyar kaza. Wayyo Allah an jima ba'a hadu ba, na gyara zama na tare da janyo ledar na shiga ci hankali kwance, abin da ya bani mamaki shine da naji ina son ragewa Baffa koda kuwa zan iya cinyewa, naji na rage na kulle na tafi ina tsallen dadi tare da yiwa malam Auwal addu'a....
.
______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.
______________________
MX
*S A S*
*MX*
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI TA NAMBOBIN DAKE KASAN SHAFIN NAN.*
*10*
*Tun* daga wannan malam Auwal yake dan yi min mutunci ba wai da yawa ba, saboda a cewar sa kada na raina shi dan ba kunya ce dani ba idan yana sakar min fuska zan dena ganin mutuncin sa. Yanzu ta kai ta kawo da kai na nake zuwa makaranta ba sai an tuna min ba dan sosai nake jin dad'in yadda ake koyar damu hanyoyin da zamu yi tsafta, kula da iyayen mu da ma jin maganar su.
Yau ma kamar yadda malama Mardiyya ta koya mana, muna tashi daga makaranta na koma gida na cire kayan makarantar nasa wasu riga da skirt wanda malama Mardiyya take kawo min, na yarta ne da kuma 'ya' yan yan uwan ta shine take kawo mana nida su Uwande dan kar su ce ni kawai take yiwa shi yasa take hadawa dasu. Naje na dauki bokiti na debo ruwa a rafin durb'un, na dawo tare da dakko ragowar sabulan wanki na da nake boyewa idan ya ragu, na wanke kayana tas suka yi kyau na shanya can inda hannun Gajiyalle ba zai kai ba bare tayi min mugunta ta yarmin dasu. Sannan ne na fara tunanin abinda zanci, dan dazu da safe tas na cinye buredin da malam Auwal ya bani jiya.
Babban buri ne ya sake mamaye zuciya ta shi yasa nake son dagewa wajan ganin nayi karatu wato na zama cikakkiyar yar jarida, wannan shi ne mafarki na a duk lokacin da na samu ina shakar numfashi. Muryar Dara'ifa ne ya fito dani daga cikin daki ina daura mayafi na a kugu duk kuwa da cewar malama Mardiyya da malam Auwal sun hana ni yin hakan, amman sabo da kuma ganin al'adar kauyen mu ne yin hakan yasa na kasa denawa, ko na yafa idan na fara tafiya sai na zaro na daure a inda na saba. Na saki murmushi lokacin da na ganta da faranti a hannunta, ina ta addu'a Allah yasa ni ta kawowa.
“D'an malele ne nayi shine na kawo miki, Na rasa yaron da zan aiko shi yasa na taso da kai na kici shi da zafinsa.”
“Walle naji dadi Dara'ifa, nagode Allah ya hi miki albarka. Sittin ta Ubangiji ina ha'awar dan malele sosai.”
“Toh gashi nan kuwa ai ta sha Dijen Baffa.”
Nayi murmushi tare da karbar filet din ta tafi ni kuma na samu guri wajan dakin Baffa na zauna ina ci ina santi dan yajin ba karamin dadi ya yi ba. Cikin ikon Allah Gajiyalle ba ta fito ba har lokacin tana daki tana baccin asara. Ina gamawa na dauraye filet din naje na kai mata tare da godiya sannan na tafi wasa na gidajen kawaye na, wasu muyi fada na tafi wani gidan, idan naje muyi ta musu da su a kore ni na fito a haka har dare yayi na koma gida na kwanta.
Babu abinda yafi ilimi dadi a rayuwar dan adam, saboda tun da aka bude makarantar boko da islamiya a kauyen mu muka fara samun sauye-sauye da yawa. An dan rage kauyancin da ake fama dashi, ana barin yara mata suna karatu dan sun fara ganin alfanun karatun a cikin rayuwar mu mata. Duk da cewa bana yin na farko a ajin mu, amman ina yin gaba ina kuma zama mai kokari har ta kai ta kawo ina zuwa ta daya ko ta biyu ko uku, da taimakon malaman mu da basa fushi akan duk wani shirme da muke yi musu. Har na kammala primary muka shiga bangaran secondary, nan din ma dai malam Auwal sai da ya bimu can yana koyar damu, A hankali kuma yana ta jefa sakon soyayyarsa gare ni inda ni kuma naki bashi fuska dan gani nake tamkar so yake ya sake samun dama ta yadda zai horani iya son ransa.
*BAYAN WASU SHEKARU*
*’KAUYEN DURB’UN*
Nana Khadijaa (Dije, Dijangala ta mai gari/Oganniya yar Baffan ta!) Duk sunaye na ne na yanka dana lakani. Da farko dai: Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar mu. Mafi yawancin yan karkarar mu na kira na da Dijangala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar mu na min laqabi da Dije Oganniya. Kasancewar a lokacin ina karama ina da kiriniya da siyan fadan da ba’a kasa da ni ba.
Duk wani cincirindon ruguntsumi idan ka cakuda zaka ga ni ce akan gaba. Lamari na dai addu'a ce kawai ta kare ni. Na kasance ni kadai ce awajen iyaye na. Tun ina ‘kankanuwa mahaifiya ta ta rasu, Mahaifina ya auro wata matar, Ya zamto riko na ya koma hannun kishiyar uwa. Na taso cikin wata irin kuntatacciyar rayuwa wanda alqalami yayi ka’dan wajen bayyana muku ita, Manufa dai na sha wahala sosai. Duk da azabar da kishiyar uwa ke gallazamin, Sai Allah yasa mahaifi na yakan kyautata min a duk sanda yake da iko.
A yau January 1, Zan kammala jarabawar kare karatu na na secondary, Alhamdulillah Allah kai ne abun godia. Na karanta b’angaren art saboda inaso na karanci fannin Mass-Com/journalism. Na kanyi daria a duk sanda na tuno kuruciya ta ta da. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u, Na sake daga kai na dubi allon zayyana ta wanda nayi sauka bara a tahfiz din da su Malama Mardiyya ke koya mana.
Shekaru na goma sha bakwai a yanzu. Ina kuma sana’ar kitso, Na kuma fara koyon dinki a gidan Bara’atu tela (Babbar mace bata ajin mu ba) Alhamdulillah da wannan yar sana’a tawa nake rik’e da kai na dama Baffan mu. Wanda a yan shekarun nan ya kamu da lalurar nakasar shanyewar barin jiki (hemiplegia/hemiparesis.)