← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 114

Sashe 75

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karan ni ce nai shiru saboda tunanin abinda ke zuciya ta. Ta ya ya zan yadda na daukar masa alk’awarin da ban san ko na menene ba, ni da ba zama nazo yi gidan shi ba? amman zan iya karba ai tunda amana sai ranta ka ci ta sannan ne ka sab'a. Zan karb'a idan yaso ko nan gaba bamu tare zan yi kokarin rike masa duk wani sirrin sa. Naja numfashi tare da cewa.

“Na amince zan karba, kuma ni ma nan gaba ina son kayi min wata alfarma.”

Sai da ya dan matsa yatsu na sannan yace.

“Ba damuwa.”

“Ina sauraronka menene kake son bani amanarsa?”

Salman ya daga mu a tare muka tashi tsaye ya kama hannu na muka doshi wajan wasu littattafai. Wani guri kawai naga ya bude sai ga abu kamar keypad ya danna kawai sai gurin littattafan nan ya fara budewa a hankali, sai wata kofa ta bayyana muka karasa wajan ya murda handle din muka shiga yana rike da hannu na. A rai na mamaki nake yi, sak irin boyayyar ma'ajiyar nan irin ta turawa da nake gani a films. Na ware ido lokacin da naga jerin computers, mamaki ya kamani nai saurin kallon Salman din dan jin karin bayani.

Mamaki yake bani idan naga yana abu cikin sanyin jiki tamkar wata mace, ya fara kokarin cire min hijabi na ki yadda, sai ya samu guri ya zauna ba yana bude wani file yace.

“Idan kin shirya na nuna miki.”

“A shirye nake wallahi.”

“Toh ni bana son aikin da hijabi a jikin ki.”

Na zaro ido cike da mamakin jin abin da ya fada, shi kuma ko a jikinsa bama ni yake kallo ba, ga dare nayi haushi kamar ya kashe ni haka na cire hijabi din ina karawa a jikina nace.

“Toh ka gaya min ko mene gashi na cire, ni ban taba ganin aikin da za a ce ba a yi da hijabi ba”

“Harda wanka?”

Yai maganar tamkar ba daga bakinsa ta fito ba. ni kam dai yau naga ikon Allah wajan Salman, ai kuwa ban sake yin magana ba har ya waigo ya kalle ni tare da tasowa yazo gabana ya tsaya. kwace hijab din ya yi tare da cilla shi gefe nai saurin saka hannuwa na ina kare jiki na saboda yar karamar riga ce, gashi ta fito da albarkatun kirjina (Fitilu biyu inji jerry Aneesa didi😂).

Murmushi ya saki tare da kawar da kai yaja hannuna muka nufi wajan computers din, ya kunna wani waje gabaki daya suka kawo haske, zaunar dani ya yi akan kujerar da take tsakiya. Sai ya yi min runfa da jikinsa, ma’ana ya rankwafo ta bayana yana danna keyboard cikin nutsuwa. Ni kam fuska na cakune dan naga sai wani shige min yake yi, ga shi idan kwantaccen sajen sa ya gogi wuya na sai naji jini na yana yawo, amman na dake dan karma ya yi tunanin dad'i nake ji.

Gabaki daya masarautar ta bayyana a ciki, sashe-sashen dake cikin ta suka fito cikin ko wanne screen. Harda sashen Ammi sashen gimbiya Shaheedah da nawa da duk wani guri dake cikin masarautar Bassannabas. Gashi nan kowa yana harkarsa ashe yana ganin komai da yake faruwa a kowanne sashe duk da naga ba a ganin wasu gurin kamar bedroom da toilet, amman ana ganin nawa da na Shaheedah. Ji nai ya hura min iskar bakinsa cikin kunne na, da sauri na rintsa idanuwa, yaci gaba da magana cikin wata irin murya wacce tamkar yana jin bacci.

“Wannan gurin babu wanda yasan ina dashi a cikin masarautar nan sai wadanda suka yi ginin shima kuma a boye akai, sannan sai Falaki da Alhassan sai kuma ni yanzu kuma kin shigo cikin wadanda suka san da gurin nan.”

Yaja numfashi ni kam idanuna suna kan sashen Gimbiya Shaheedah wace ke hakimce a parlour bayin ta sun zagaye ta daga mai yi mata tausar kafa sai mai matsa mata kafad'u sai masu fifita da wace take rike da basket din kayan marmari. Mulki kawai take zubawa saboda an tsotsa har an rasa ina za a sanya izzar mulkin. na kuma maida hankali na sashen da su Galadima suke tsaye jikin wani gini da alama wata maganar suke yi mai mahimmanci a gare su.

“Na yarda dake a dan zaman da nayi kina tare dani, duk da nasan kin tsaneni. Zanyi wata yar tafiya ne ina son kisa min ido akan masarautar nan, ina ji a jiki na kamar masu min zagon kasa sun mamaye ni. Khadija ki min alkawarin zaki rike sirri na ba tare da kin gayawa kowa ba, nai miki alkawarin idan nai tafiyar na dawo zan bayyana miki abin da baki sani ba, zai saki farin ciki ki manta duk wani abu da ya shud'e kinji?”

Yai maganar tare da kai min sumbata a gefen wuyana. Na kasa cewa komai sai wani irin fitsari ma da yake neman takura min saboda kusancin mu yayi yawa, duk ya nanike min kamar wani mage.

Haka Salman ya zauna kusa da ni ya dinga koya min yadda ake controlling cctv din da yadda ake recording da komai, mune har Kusan karfe hudun dare Salman yana ta nuna min abubuwa dangane da sirrinsa. Allah sarki gaskiya yana da mugun kawaici, Cikin rai na ban san lokacin da na dinga zuba masa addu'o'i kala-kala ba. Sai da ya tabbatar na gane yadda suke gashi daman nasan wani abun saboda yanayin aiki na, sannan ya tashi yaje ya dakko min hijabi na yasa min tare da kashe abubuwan. wata kyakkyawar kofa ya bude, abinda ya daure min kai shine ganin mu a cikin tsakiyar bedroom dina wanda nake bacci a cikinsa. na kalli gurin wanda duk a tunanina decoration ne ashe wai kofa ce a gurin, cikin rai na nace 'Shege bature' yasan takan tsiya kala-kala.

“Ga hanya nan, Sai da safe, sai ki kula da mutane karsu gane ta. idan zaki shiga ba sai kin bi ta apartment dina ba kai tsaye kawai ki shiga ta nan. Good night yar jarida, sai na dawo ki kula min da komai.”

Yana kaiwa nan ya juya ya tafi, ni kuma na karasa wajan ina tab'a hanyar da tai matukar daure min kai. Komawa nayi tare da hayewa kan gado, sai kuma nayi saurin tashi ina kalle-kalle ina son ganin a ina aka kafe min cctv camera amman ban gani ba, haka na gaji na barshi na dawo tunanin ta yadda zan fara yi masa aikin nan ba tare da kowa ya san da zaman gurin ba bare har na karya alkawari ba.

*SOUTH KOREA*
(GANGNAM HOSPITAL)

Adaidai asibitin motar da aka dakko Salman daga airport ta tsaya. Falaki ya fito ya bude masa murfin motar, Sanye Salman yake cikin kananun kaya samfarin riga da wando yan kanti. Kansa yasa pcap. Yayi kyau sosai, Idanunsa saqale da spectacles dinsa na gado mai dauke da tambarin givenchy, Tafiya yake cikin kasaita, Daga shi sai Falaki. Sunyi ‘badda kama ba zaka taba cewa sarki bane da matemakin sa.

*consultant Ibrahim (Khal) AS*

Dai dai kofar shiga dakin suka tsaya suna duban juna, Falaki ya dafa kafad’ar Salman alamun kara masa karfin gwiwa...

“Ranka ya dade mu shiga kawai dan Allah...!”

Kad’a Kai Salman yayi, Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Falaki ya koma can waiting area ya zauna. Salman kuma ya sa hannu a hankali ya bude kofar, Dai dai lokacin da Khaleel ya daga idanu don ganin waye ke shigowa. Sosai suke kalon kalo tsakaninsu, ko wanne da yanayin yadda yake tunanin dan uwansa. kamar kuma an tsunkuli Khaleel haka ya zabura ya mike daga inda yake zaune.

“Ya...Yay... Yaya Salmaan ne???? Is that you? Is that really you? Ya Salman Kai ne ko kuwa idanu na ne kemin gizo..”

Salman yai murmushi hade da jingina bayan sa da kofa..

“Ni ne Khal...! Ni ne Salman.. Ashe rai kanga rai? Shekaru nawa rabon dana sakaka a idanu na Khal?”

Wasu zafafan hawaye suka zirarowa Khal a saman kyakkyawar fuskar sa. Ya share hawayen dake gangarowa a fuskar tasa yana mai jujjuya Kai...

“Noo Yaya.. I love miss you soo much!”

Da sauri suka rungume juna.. Sai kuma kuka ya kwacewa ko wannen su sharrr,

“Ina Ammi take...?.”

“Tana gida Khal...”

“Ina Abdullah? Yaya ashe baku manta dani ba.?”

Murmushin da yafi yake ciwo Salman yayi, Ya kamo hannun sa suka zauna yana kalle kallen office din.

“What a nice office you’ve got...Congratulations Khal..”

Da sauri khaleel ya mike ya sabule white coat din jikin sa.

“Muje apartment dina Yaya. Kai kadai kazo?”

“Noo....”

“Da aminin ka da na sanku tun tuni ko....? Indai kuma ban manta ba... Falaki ne”

“Well... Yes”

Fitowa sukai su biyu Kowanne fuskar sa dauke da murmushi, Duk kuwa da glasses din fuskar Salman kallo daga zakai musu kasan yan uwan jini ne. Khaleel ya rungume Falaki suka tafa, Kafin su isa parking lot yaja su suka tafi apartment dinsa. Sai da ya musu ordering abinci suka ci suka koshi, Banda Salman daya caccakuna domin shi ba ma’abocin cin abinci bane sosai. Tukun sannan Khaleel ya gyara zama ya shiga yiwa Salman tambayoyi. Shi dai Falaki fita yayi ya basu waje saboda su gana sosai..

“Wallahi Ya Salman ban yada ku ba.. Bansan meyasa ba, Danayi yunkurin zuwa gida ko kiran waya sai na kasa.. Nayi attempting several times Yaya na kasa...”

Fashewa yai da wani kukan mai cike da bakin ciki, Salman ya riko hannuwan sa yana bubbuga bayan sa alamar rarrashi,

“Na shiga fiye da yanayin ka Khal, Nasan kuma yadda kaji. Presently ma ni tamkar an juyamin tunani na.. Na jima bana tuno Ammi da ku, tamkar an shafemin sanin ku a kwakwalwata Khal gaba d’aya na shiga cikin matsalar rayuwa..”

“Subhan’Allah...! Kenan ba jimawa komai ya dai daita awajen ka?”

“Eh to.... Kasan na kira ka last month ko? Zan iya cewa daga lokacin memory d’inku ya fara dawo min, Ammi kuma ba’awani jima ba. So yanzu dai kasan bazai yiwu na nuna na san inda mahaifiya ta take ba, tunda naga hakan ne ke sa su yi mana makarkashiya, Kasan yadda masarautar nan take. Bana son a cutar da ita da ku shi yasa ban nunawa kowa ba.”
Chapter 75 · 0% Book details