← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 114

Sashe 90

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya bani amsa yana zaro min sabuwar rigar wanka yazo ya nannade ni a ciki tare da daukata gabaki daya muka fito.

Zai kwantar dani akan gadon sa nai saurin riko masa wuya Ina faman hade rai nace.

“To kayi hakuri tunda kaji haushi. Ai kai dinne da laifi. Kuma ni dai Sashe na zaka mai dani, daman ai har gorin riga kayi min”.

Kallo na yayi domin daukar jarirai ya yi min, na rufe ido Ina turo baki kawai naji ya sumbace ni akai na bude ido ina cewa.

“Ka bari dan Allah ina da alwala.”

“Ai naga ne duk kin zama me tsiwa, gwara nayi maganinta kafin sadakina ya gama hucewa”

“Okay, ashe da mugunta dama kayi? To Ka kai ni daki na ni”

Sosai ta bashi dariya. harya kasa dannewa sai da yayi kadan. Yace,

“Ina ni ina yima gimbiyata mugunta. ?kawai dai a cikin game ne. Kiyi hakuri kiyi sallah ki huta sai na kai ki.”

“A'a bana son nan.”

Babu yadda zai yi haka ya nufi sashe na Ina ta faman tsuke fuska, a kan bed ya kwantar dani sai faman cije baki nake saboda har yanzu Ina jin zugi. Wardrobe dina ya bude ya dinga karewa kayan nawa kallo kafin ya zaro guda, daya, yana warwarewa yaga doguwar riga ce Abaya, ya nuno min nayi kamar ban san me yake yi ba yace.

“A dako wannan.?” Cikin son kona masa rai nace.

“Bana so ka barshi zan dakko da kai na.”

Sai yaki jin haushin Sai ni da raina ya kuma sosuwa.

“Haba hajiya ai ba zaki Iya bani haushin ba, ki bari dai ni da na jangwalo nayi miki komai.”

Idanu na gwalalo waje. dan na fahimci a fili nai maganar ashe. Ganin ya kalloni nai saurin dauke kai na, na share shi kamar ban ganiba.

Shima watsar dani yayi ya juya ya ciro min riga da zani na atamfa, inda nake ya dawo fuska babu alamar wasa ya taimaka min nasa ya saukeni kan sallaya sannan yace min.

“Kafin ki idar bari naje na shirya sai nazo nayi jinya.”

“Ka barshi ni dai bana so.” Nai maganar a hankali kaina a kasa. dan inhar ya cuskule fuskarnan tsoron kai masa wargi nakeyi. kusa dani yazo dab da fuskata.

“Haba baki da lafiya fa, idan anzo ance meke damunki ai ni zan gaya musu. Kedai kawai kiyi sallah tare da addu'ar Allah yasa mufi haka kusanci, Allah kuma yasa yarima ya isa masaukinsa” ya kare maganar yana dora hannunsa a marata da wani kashemin ido cike da shakiyanci.

Harara na sake narka masa bance dashi komai ba na ture hannunsa na tayar da sallah.

Shi kuwa Salman dariya ya fita yanayi, ta dauka yana jin haushi idan ta harare shi ba tasan kyawunta yake sake gani ba, yana ganin tamkar shagwaba ce take masa ta soyayya. Juyawa yai ya koma sashen sa dan ya shirya kasan cewar yau yasan akwai bakin da zai ta gani a fada saboda taron bikin nan.

**

Ni kuma Ina idarwa na mike zan koma kan gado na kasa tafiya sosai, na saki kuka ganin babu mai taimaka min. bansan na furta sunansa ba ina hawaye. Babu yanda na iya dole sai na rarrafa na kama gadon sannan na dafa naje na kwanta ina tariyo duk abinda ya faru a daren jiya kamar a mafarki ko film. Tunawa na dinga yi wani abun inji haushin kai na saboda ai kamar yadda ya fada ne tana bashi gudun mawa wajan nuna son ayi, amman ita kanta ba tasan maganadisun da ya dinga janta ba har ta dinga biye masa.

Ina nan kwance cikin tunanin abinda ya faru, wani ya sakani haushi wani murmushi. Tabbas na sake yadda Sarki Salman yana so na. Sannan shi din na dabanne. Wai nice yau matsayin matar sarki salman, matsayin abu daya?. Wani iko sai Allah. Dije nan ta kauye mai dan karan jahilci da neman fada. Baiwar gajiyalle. Hawayen da suka cikamin ido nasa hannu na share. Samun kaina nai da dora hannuna saman marata saboda tuno maganar Yarima da yayi dazun. Lumshe idanuna nayi a hankali, sai naji knocking. ba damar na iya tashi hakan ya bawa mai bugun damar murdawa. Hadima tace kanta a kasa tai sallamar tare da durkusawa daga can bakin kofar tace min.

“Allah ya taimaki Gimbiya, munga baki sakko bane shine muke son ganin ko lafiya.?”

Gada sai na nemi na rikice, banda a kwance nake nasan tsab zan Iya faduwa. Yanzu me zan ce mata fisabilillahi? Na daure dai na ce mata.

“Karku damu kai na ne yake ciwo shi yasa. Kuje kuci gaba da hidimarku, yau biki kuma ku ci bikin ku.”

“Asha, sannu Gimbiya Allah ya baki lafiya ya yaye miki, ko maimarta ya sani? Idan be sani ba gwara a je a sanar dashi kar....” Na dakatar da ita.

“Karki damu na sanar dashi ta waya.”

“Toh shikenan ranki ya dade amman za'a kawo miki abinci ko?”

“No bana sha'awar komai idan anjima naji Ina bukata zan kira in sanar miki.”

“Toh ranki ya dade na barki cikin aminci da salama, Allah ya kara lafiya.”

Fita tayi na sauke ajiyar zuciya. A lokacin ne Salman ya shigo hannunsa rike da tea cup dayan kuma vanilla cake ne a cikin sosa. Lumshe ido nai tamkar mai bacci, har ya karaso kusa dani ya zauna ban motsa ba dan ko ido bana son mu hada.

Rankwafowa ya yi kai na tare da shafa min fuska idanuwana suka fara motsi still naki budewa.

“My love ki tashi kisha tea Kar Yarima na ya farajin yunwa”

Ko motsi naki yi.

“Okay bacci kike yi? Ba zai yiwu ba ki yi wannan abun kuma ki zauna da yunwa salon Kema ulcer ta kamaki Ko ta kama min yarima”

Yana kaiwa nan ya ajiye tea din a bedside ya fara Kokarin cire min hijabi nai saurin bude ido Ina turo baki.

“Ni dai gaskiya ka rabu dani.”

“Zan rabu dake amman Sai naga kinci wani abun sannan K da yarima”

“Na koshi ni. Wai waye yarima kabi ka isheni da zancensa”

“Zaki sanshi” yayi maganar yana wata munafukar dariya.

Fuska na sake ciskulewa nace
“To nama fasa cin”

“Ba zai yiwu ba my love. Dole kisha saboda yanzu da zan taho mukai waya da Ammi tace kina ina lafiya dai ko? Nace mata baki jin dadin jikin ki, tace to na tabbatar kinsha magani kuma kinci abinci kafin tazo dubaki. Dan na fada mata yau kin zam........”

A mugun zabure na tashi zaune. Cikin rawar baki nace,

“Kace mata na zama me?”

Kwashewa yayi da dariya sosai.

Na zuba masa harara ina komawa na kwanta.

“Yi hakuri wasa nake miki bance mata hakaba fa”

Kin kallonsa nayi nasa hannu kawai na karbi cup d'in, a hankali na ke sha yana gutsuro cake d'in da fork ya samin a baki, ban ma san Ina jin yunwa ba sai da naga na shanye tea da cake d'in.

“Yauwa Good girl. Yanzu me kike ji? Akwai ciwo a gurin?”

Samun kai na nayi da daga kai still Ina ta turo baki gaba alamar har yanzu ban huce ba. Ya kwantar dani a hankali nayi rigingine kawai naga bawan Allah yana shirin daga min zani, da sauri na rike tsakiyar zanin Ina zaro ido cike da mamaki.

“Menene haka?”

Salman ya sosa habarsa ya kasa bari mu hada ido. Can kuma naga ya kalle ni tare da matsowa ya dafa kafadata yace.

“Duba miki zanyi ko wani abun ne a gurin, amman yaci ace kin mike tunda kin gasa dan nasan ba da karfi na....”

“Wai kai dan Allah meye haka? Kai yanzu Sai ka lek....” Na kasa karasawa saboda kunya, Sai kawai na ture masa hannun na juya tare da rufe ido.

Bakinsa ya kai kan hannu na ya sumbata sannan ya mike yana fadin.

“Sorry baby na tafi zan dawo na kuma ganin lafiyar ki, nasan lokacin kin huce ko cewa nai zan kuma zaki karba.”

Hannu nasa tare da toshe kunne na alamar ko yayi ba zan ji ba. Ina jinsa ya juya ya tafi yana dariya, ni kuma na bude ido Ina bin hanyar da uwar harara. Lallai ma guy d'in nan, ashe haka yake daman? Anya kuwa ba kwanan nan ya zama haka ba, dan idan ka ganshi ko yana maka magana Sai ka rantsa da Allah ba zai Iya wadannan abubuwan ba. Amman dubi yadda ya yi min, duk da cewa ma ni ya yi ne cikin rainin hankali, da Ace babu wannan game d'in da yasa ban san abin da zai faru ba sai Allah.

Ina cikin wannan tunanin bacci ya dauke ni mai cike da mafarkai. Muryoyin da na dinga ji ne yasa na farka ina murza ido. Wasu manyan mata na gani kai da ka gansu kasan cewar ko wacce ji take da kanta. Na sake ware ido bayan na juyo yadda zan gansu sosai, manya ne da kowacce a cikin su tayi uku na saboda girman halitta.

“Kece amaryar Salman d'in?” Wata farar mata sanye cikin wani shegen lace take tambaya ta.

Na sunkuyar da kai Ina wasa da hijabi na, suka girgiza kai dayar tace.

“Kece kishiyar Shaheedah kenan?”

Nan na ban amsa ba kuma ban kallesu ba saboda ban san dangin waye a cikin masarautar ba. Zagaye suka farayi na dinga satar kallon su kasa-kasa zuciya ta na ta karanto addu'o'in neman tsari. Can na jiyo muryar daya daga ciki ba wacce tai tambayar farko ba sannan ba wacce tayi tambaya ta biyu ba.

“Me yake damunki baki fito gurin shagalin ba.?”

“Bana jin dadi ne.”

“Wane irin rashin jin dadi ne bakya ji?” Samun kai na nayi da cewa.

“Zuciya ta ce bata min dadi, komai duhu nake Jin sa ban san dalili ba.” Na karasa magana cikin jimami.

Murmushi suka yi dukannan su sannan ta farkon tace.

“Kin sanarwa da Salman.?”
Chapter 90 · 0% Book details