Sashe 25
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Hm kibar dangin miji! Basu da farin cikin daya wuce shiga tsakanin ka da mijin ka, Ai nagaya miki nace Kiyi taka tsantsan baki ji ba.”
“Wallahy Na dauka tunda yar kauye ce, Irin makarantun nan haka na yakubayi za’a sata, Har nace su shukra su hada kuncen kayan su na babbata, Ashe ashe.”
“Yanzu wai meya faru..?”
“Ina centre dinnan ta British Eng? Me shegen tsada?”
“Sabuwar nan da akai shekarun baya ko?”
“Ita dai.. wadda har yar Hajian Badawa ma ta kasa shiga, Nima da kyar da jibun goshi da magiya Wallahi ya yadda ya saka su Hameeda lokacin. Yace tayi tsada, Yanzu kuwa kudin ta yayi doubling.”
“Nagane Haj. Nima nan ba Sameer bane kadai yayi?”
“Toh wallahi ina kai ki dai ya yanko mata form ta fara zuwa, Ga Buk nan ma ya samo mata admission, Yace Hameeda ga MasterCard dinsa ta kaita shopping malls ta siyo mata komai, Ta bawa Senegalese tailor dinmu ya mata dinkuna..”
“Kai... katarar ubancan! Alhajin?”
“Hmm Wallahi Hajia! Nace masa sede driver amma Hameeda ba zata ba.”
“Shine ya harzuka Yace shi zai kaita, In k’ark’are miki zance dai, Ya lafto mata uban kaya, Ga latest waya datafi tasu Hameeda, Ga kayan gyaran jiki, ke Kinga yadda ya dawo da ita a rana d’aya kacal? Komai designers wallahi Hajia. Hmm ai ya kawomin alaka’kai gida..”
“Kuma Hajia yar kanwar sace?”
“Wallahi yar kanwar sa ce mai rasuwa, Ke da ba haka ba Ai sai muce auren ta zai yi. Toh Allah yasa ba aure a tsakani.”
“Toh Hajia ki tashi tsaye.. Zahiri yarinyar nan tazo da dan asiri daga kauyen su, Ke yan kauyen nan fa wasu ba Allah a ransu.”
“Nima nayi tunamin hakan, Domin Jummai ma tafara gayamin haka. Toh ai kuwa bata isa ba, Bazata sab’uba Wallahi..”
“Ina bayan ki Hajia. Ki kuma nunawa Alhajin bacin ran ki kawai akan haka.”
“Ai wani irin murdadden hali ne dashi, Wannan botsattsen idan ya tsaida ra’ayin abu wallahi baya canza shi. .”
“Gaskia Alhaji yabani mamaki”
“Ya baki koya bani? Duk cikin yan uwan nasa ba wanda yace zai karbeta sai shi uban tausayi, Saboda anga yanada abun duniya. Yazo sai fiffita bare akan ‘ya’yan sa. Wallahi ban taba kawo abubuwan da zai yi mata sun kai haka ba. Shegiyar yarinya yar iska.”
“Simi simi da ita, zubin munafukai.”
“Wallahi na dauka ta Allah ce yarinyar nan, Zata dauki maraicin ta ta iya talaucinta, Shegiya wai masscom zatai. Hm!”
“Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu Hajia. Amma dai yarinyar nan sai kinyi dagaske, Kar ta raba uba da ‘y’ay’an sa..”
Haka dai Hajia Abeeda da kawarta su kaita aibata Dije, Haj ta jima a gidan k’awarta na sake mata famfo, Ta dawo gidan ranta a bace,
Muryar Mami na jiyo alamun ta dawo, Ina tsaye agaban Ya Shukra ina rokonta data temaka ta gayamin ma’anar wasu kalmomi. Mami ta bugo kofa tashigo, Ta dube ni a harzuke tana ajiye mayafi,
“Meya haka.?”
“Mami aiki zata koyamin..”
Na bata amsa ina nuna Littafin hannu na, Ya Shukra ta ajiye biron hannun ta tana kallon Mamin a tsora ce,
“meaning din wasu words ne tace dan Allah na gaya mata.”
“Toh idan kin gama kizo daki Ina neman ki.”
Kada kai Ya shukra tayi , A dubibice ta gama koyamin ta shige dakin Mami, Ina jiyo sanda Mami tasa key ni kuma nai saurin hayewa sama gudun kar ma na jiyo Abun da zai hanani bacci. Toh haka zaman namu ya kasance, Yau dadi gobe babu. Ni dai zaman nan din yafu min sau million dari akan na Durbin. Domin nan ba duka, Ba zagi, Ba hana abinci. Sai dai mita da bakar magana da Mami kan yab’amin. Wani lokacin har fada take janyowa tsakanin mu da su Ya Hameeda.
B<><><><
Hutun first semester da aka fara yi mana mai dogon zango, Kawu yasa na shirya driver ya fara kai ni gidajen yan uwan mahaifiya ta da suke nesa, Jos muka fara zuwa nayi sati biyu a gidan kawu Kabiru, Sunji dadin zuwa na, Suka min shatara ta arziki, Daga nan kawu ya yankamin ticket na garin lagos inda kawu Hashim yake. Tab Dije a jirgi, Na danyi kauyanci kadan inata kalle kallen cikin jirgi, Dak’yar na sai ta kai na muka karasa birnin ikko. Sati na biyu acan nan ma kafin na dawo gida da d’imbin kayan alkhairi. Duk inda naje sun mini kyauta ta mutuntawa, Daga nan Kawu da kansa ya zazzaga ya da ni gidajen yan uwa na cikin kano na gaggayshe su, Lalle dangi rahama ne.
Dake hutun wata biyu ne, Kawu ya sanya ni a computer school inda nayi certificate na tsawon sati uku ne. Hakika dik wani gata Kawu yana yimin shi. Gashi yanada temakon al’umma mabukata da masu shi, Yana temakawa marayu, Ga foundation da yake da ita na tallafi. Gaskia Kawu mutum ne. Saboda temakon da yake yi ne ashe yan kasuwar manya da masu kana'oin sana'oi suka kada 'kuri'u suka tsai dashi, ‘Shugaban kasuwar Singa. Saboda temako da yake yiwa masu karamin karfi a kasuwar. Kuma Doctorate degree din sa ma honorary doctorate ne da university of east london ta bashi.
*BAYAN WASU SHEKARU*
Alhamdulillah Ya Rabbi! A yau ne sunana ya fito a call-up letter na Nysc. A kano nayi orientation camp dina na sati uku, Kawu ya samomin wani gidan rediyo da talabijin na kasa mai suna Dokinkarfe24 wanda keda sashe anan kano. Anan na fara service dina na shekara d’aya. Har Allah yasa na kammala lafiya.
*DOKIN ‘KARFE24 TV/ NEWSPAPER AND RADIO STATION*
Alhamdulillah! Na shiga jujjuya offer dina a hannu na aiki, Da gaske ba mafarki nake sun karb’e ni a matsayin ma’aikaciyar su? Lokacin da nazo service (place of primary assignment/Nysc) Koda wasa bantaba kawowa zasu dauke ni a gurbin ma’aikaciyar su ba, Wai yau ni Ni Nana Khadijaa na zama cikakkiyar yar jarida kuma ma’aikaciyar gidan tv na Dokin Karfe24? Kaf kano babu gidan talabijin din daya ko kamo k’afar sa. Sune na d’aya dake tashe ance tun shekarun baya. (Television/ Radio station/ Newspaper) Duk Dokin karfe24 na kammale dasu. Kamar sabuwar tabi haka na tsaya ina kallon offer ina murmushi. Cikin haka Mas’oud saurayi na yazo ya same ni hannunsa rike da kwalbar maltina sanyayyiya. Yana zuwa yaja kujerar kusa dani ya mikomin yana murmushi,
“Maman Waleeda da Waleeda..”
“Na’am Baban Waleeda da waleed”
Domin mun rigada mun tanada sunan da zamu sanyawa yayan mu na farko idan munyi aure, Saboda tsabar yadda mukeson junan mu. Mas’oud ya dakko jaridar gefen sa ya shiga min fiffita a fuska,
“Sannu tawan.. Congratulations! Ai na gaya miki you wud surely made it, Kuma wallahi ko kadan banwa boss zancen ki ba, Su suka ga cancantar ki.”
“Hakane Nawan! Alhamdulillah! Nagodewa Allah. Kai ma na gode maka yadda kake encouraging dina. Thank you so much.”
“Anything for you, My love!”
Rufa fuska ta nayi da tafin hannu na, Saboda yaja kalaman ‘My love’ din. Kai Mas’oud karshe ne a iya soyayya! Anya akwai na biyun sa kuwa a tsarin iya tattalin mace?
“Tunanin me kike yi ne tawan?”
“Tunanin ka mana Habiby..”
Na karasa fada ina kanne mai ido d’aya, Murmushi yai yana gyara zaman hular kansa,
“I’m all yours My love.. Sai yadda ki kai da ni. So ya zaki fara aiki ne yau ko sai nextweek din kamar yadda boss yace?”
“No sai nextweek ko? Saboda na dan kara shisshiryawa.”
“Banda dai heavy makeup, cuz I wont tolerate that my love, Banso sauran maza su rika kallemin ke. Ni nafuso ma ki rika saka hijabs da safar hannu data kafa.”
Cuno baki nayi gaba domin wasu dabi’una na rigima ban dai naba, Na fari da idanuwa na kafin na narke su akan sa,
“Ni ni ni gaskia a’ah! A wannan zafin Habiby? Ayi hak’uri dai.”
“Oh rigimatu na.. Na hak’ura! Idan kin zama Mrs Mas’oud ai dole kisa. Muje nai dropping dinki a gida.”
Handbag dina ya dauka da sauran kayayyaya ki na, Muka jera muna tafiya gwanin sha’awa, Motar sa muka shiga ya kai ni har kofar gida. Kawu ya dawo domin ga motar sa nan da direba a waje,
“Zaka shiga ku gaysa da Kawu?”
“Afuwan My Love! Zan dai yi fixing lokaci, Kinga yanzu ba’a shirye nake ba. Zanzo zuwa na musanman.”
“Kullum haka kake cewa Habiby..”
“Worry not My love! Ina nan tafe. Kinsan zuwa gaida manyan nan sai ka shrya tukun, Kuma so nake idan nazo gaisuwar ya kasance da yan kwanaki a kawo komai na aure.”
“Hakane! To Allah ya kai mu. Ya tabbatar mana da alkhairi Aamin.”
“Aamin”
Sallama mukai irin ta masoyan da suka reni kansu da soyayya! Domin har gaban abadan zuciya ta bazata taba son wani Da namiji ba face Mas’oud. Saboda shine saurayi na na farko wadda zucia ta ta amsa sak’on soyayyar sa. Na riga na gina sonsa a zucia ta, Babban buri na yanzu a duniya bai wuce na zama mata agare shi ba. Da wannan tunanin na shige cikin gida, Fuska ta dauke da farin cikin abubuwa biyu. Zamana cikakkiyar yar jarida da kuma neman aure na da Mas’oud zai zo. Alhamdulillah Yaa Rabbi!
<<<<>>>>> <<<<<>>>>>
Fitowa ta daga wanka kenan ina tsane jikina da towel kasancewar har kai na sai da na wanke, shigowar Ya Shukrah tana faman danna waya sanye cikin riga da wando kanta babu dankwali sai faman taunar chewing gum take yi, na dan saki murmushi duk da cewa ba kulani suke yi yanzu ba sai wulakanci da rashin mutunci da suke yi min ganin daddyn su yana min komai irin nasu baya ko banbantawa, shine dalilin da yasa suke tsangwama ta. Na ajiye small towel din akan stool ina shirin janyo man shafawa nace.
“Ya Shukrah tsifa kika zo nayi miki ne?”
Ta sakar min harara tare da yi min kallon sama da kasa kafin tace.
“Ban sani ba, da yake in zaki yi min tsifa tasowa zanyi nazo kiyi min ko? Wai me yasa duk abinda ya danganci yar kauye sai ta nuna a wajen? Mtseww village girl, Mami zaki je ki gyarawa daki mai bin maza kawai.”