← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 114

Sashe 32

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Haba Alhaji ai mune da ban ha’kuri, Ayi hak’uri, Bafaden sarki ya tafka kuskure, Sabon d’auka ne kansa yana rawa ya aikata haka, Sarki yace a baku hak’uri dan Allah. Tafe nake da asusun bankin sa yace a lissafa dik nawa aka kashe sai a biya. Domin bafaden da ya tafka ta’asar ma tuni an sallame shi ya koma cikin yan lufudi..”

“Haba! Ba wani abu wallahi, Da kam dai banji da’din rashin nuna kulawar da masarauta tayi ba, Amma tun zuwan ka da kayi asibiti an sheda min kuma komai ya wuce wallahi, Lefi kuma bana bafade bane shi kadai harda diyata Khadija.. Kuruciya ce itama da kwadaituwar hazakar aikin ta yasa tayi wannan shirmen. Idan ba haka ba Ina ita ina tambayar sarki kai tsaye.? Uban taro guda? Tayi kuskure itama sosai, Saboda haka a bawa sarki hak’uri Shima dan Allah, Khadija ta tafka babban kuskure, Ina fatan Allah ya huci ran sarki ya yafe mata.”

“Babu komai Alhaji.. Allah ya yafe mu gaba d’aya. Toh amma wani hanzari ba gudu ba. Sarki yace yana son ganin ka ido da ido a fadar sa.. Nan da kwana ki biyu kacal. Da yammaci bayan an tashi daga fada.”

“Tohh! Ni? Toh Allah ya kai mu.. Na karbi wannan gayyata da hannu dubu. Allah ya bamu ikon ganin lokacin.”

“Aamin Yaa Rabbi..”

Sallama Alhassan yayi masa ya tafi. Dr. Isma’el ya shiga tunanin abinda yasa sarki keson ganin sa? Ko dai bayan ta’asar da Khadija tayi ranar ta kara da wani abun aka boye masa? Tunani ya shiga yi shi kadai yana dirkawa cikin sa ruwa. Zuciar sa dauke da addu’ar Allah dai yasa alkhairi ne yake kiran sa ba sharri ba.

Kafin ranar ta zagayo kullum sai Dr. Isma’el ya tambayi Khadija akan gaskiar lamarin da ya faru awajen sauka sau ba adadi. Ranar da zai je masrautar ma sai daya sake tambayar ta tace daga tambaya bata kara ce masa komai ba. Kad’a Kai kawai yayi ya fice yana jinjina wannan al’amari.

Kawu Daddy na fita na sake sauke gwauruwar ajiyar har ga Allah na tsani sarkin nan, Wallahi bana son sa, Kai duk abunda ya dangance su na tsane su.

“Shege.. Mumugunci, Uban fadin rai. Wannan sarkin matar sa ta shiga uku da izzar sa. Bare kuma a kai ga yan aikin gidan..”

Na sake jan wani dogon tsaki na juya daga kwanciyar da nai. Domin tun da la’anannen bafaden sarki ya rafke kai na ban koma aiki ba, Na dauki sick leave. Sannan duk wasu aiyuka na gida Kawu daddy ya dauke min su, Yace duk Wanda ya sake sa ni wani aiki sai ya mugun sab’a masa. Gaba d’aya yan gidan zaman takun sak’a suke yi da ni.

“Wayata na janyo na rubutawa Habiby na message na masoya, Na tura masa.

“Dear Habiby.. Nothing in this world can ever keep us apart from each other. We’ll always be together no matter where life takes us. I love and miss you so much. Yaushe zaka Zo? Hmm har yanzu ka ki zuwa ka kwashi gaisuwa wajen Kawu Daddy ko?”

Minti biyu tsakani ya min reply,

“I choose you. And I'll choose you over and over, Without any doubt,. I'll keep choosing you my love, My heartbeat.. My shining light. I love and missed you most. Ina nan tafe love. Zan zo na gayawa Kawu abinda ke tsakanin mu In Shaa Allah!. You are the pillar of my life. I love you.Thank you for being a part of my life.”

Karantawa nai na lumshe idanu ina tuno yadda muke ragargazar soyayya a wajen aiki. Kowa kiran mu yake da Romeo and Juliet.. Da wannan tunanin na mike murmushi fadade a fuska ta na shige bandaki don yin wanka.

*MASARAUTAR BASANNABAS*

Tunda aka tashi daga fada yake jin tamkar yaje amma ya kasa. Ya jima yana kallon sashen da zai sadaka da wajen mai babban daki (mahaifiyar sa) tamkar ya sauke yaje, Amma da yayi taku d’aya biyu zai aiwatar da hakan sai yaji tamkar an fusgo shi ta karfi an hana shi. Wani bangare na zuciar sa na aiyana masa abubuwa marasa dadi. Kallon wayar sa yayi ta gefen ido. Akwai abinda yakeson aiwatar wa amma ya rasa menene? Lokaci zuwa lokaci ya kan tuno sunayen Khaleel da Abdul a zuciar sa. Amma shin su waye su ma? Rike goshin sa yayi da tafin hannun sa na dama, Dakyar yai ajiyar zuciya kawai ya shiga gyara zaman alkyabbar jikin sa, Sakin labulen yayi.

Ya sauka daga stairs din sashen sa, Masu bashi kariya na biye da shi da fadawan sa suna take masa baya. Sai kirari ake masa. Ya shiga cikin fada idanun sa saqale da bakin shades dinsa. Wani parlorn sirri dake cikin fadar ya shiga ya zauna. Hannun sa na dama yasa ya dafe k’irjin sa yana taune kasan lips dinsa ta cikin rawani..

“Yaa Rabbi....!”

Wani madanni ya danna, Sai ga bafaden sa Alhassan da Dr. Isma’el Sai raba idanuwa yake. Domin dik kudin ka da kamalar ka inde kazo gaban sarki Salman sai ka rissina. Ma’abocin ado da zatin sarauta. Me kwarjini da farin jini abun so ga kowa. Kwasar gaisuwa Dr. Isma’el yayi awajen Sarki Salmaan. Aka basu waje su biyu, dama parlorn soundproof ne ba’a iya jiyo komai dake wakana. Sannan babu cctv aciki.

Gaban Dr. Isma’el sai dukan tara tara yake. Ya sosa k’eyar sa yana numfarfashi da sauri.

Gyaran murya Sarki Salman yayi. Dr. Isma’el ya dago kansa sai kuma ya mayar saboda cikar idanun da sarkin ya masa. Gashi dai matashi yaro dashi amma sai kwarjini.

“Allah ya karawa Sarki lapia...”

Izzar sarauta da kuma halitta irin ta sarki Salman na rashin son magana yasa ya jima kafin yace,

“Ya....Mai jiki?”

“Da sauki ranka ya dade. Taji sau’ki tamkar bata yi ciwo ba.”

“Alha....Alhasan ya gaya min komai. Kun yafe abunda aka kashe na asibitin ko..?”

“Allah ya kara maka lapia. Yasa kafi haka! Allah yaja da zamanin ka. An kammala komai ranka ya dade. Ai lefi na ita yar wajena ce. Ina ita ina yiwa uban kowa tambaya a bainar jama’a? Amata afuwa karamar yarinya ce, Kuma sabon shiga ce a aikin nata.”

“Ma....”

Shiru Sarki Salmaan yayi yana ayyana yadda zai fito da maganar,

“Ma.. matar aure ce ne?”

“Ranka ya dade ba matar aure bace. Ba ta dai tsada tsayayye ba amma tanada manema sosai. (Tanada su ko?) Dr. ismail ya karasa fada yana mai tambayar kansa, Domin shi bai ma taba ganin tana zance ba. Bare yaganta da wani saurayi.

Jujjuya me ze fada Sarki Salmaan ya shiga yi. Shin ga zancen a bakin sa amma yanajin nauyin fada, Wai shi mighty Salmaan shi zai furta yana neman amincewar mace yau? Siririn Tsaki ya saki wanda har sai da Dr. Isma'il ya dan dago ya dube shi.

“Idan babu damuwa... Zaka bani auren ta, ina da bukatar masu irin aikin ta a kusa dani. Amma idan har babu neman auren wani akanta, Domin neman aure akan aure haramun ne.”

Wani dindirus Dr. ismael yaji zancen, me kenan sarki yake nufi akan na bashi auran ta? Taya zai tambayi auran Dije bayan yasan wadanda suka fita a cikin duniyar nan. 'Hadin Allah' yaji zuciyar shi ta bashi amsa ganin dole yana bukatar hakan. Sai kuma wani farin ciki ya mamaye ransa, Yarasa me zeyi ma, Tamkar yayi tsalle ya rungume sarkin dan murna, Samun kansa yai cikin tsananin farin ciki, Wai Dijen sa ce yau Sarkin Basannabas yake neman auren ta. Allah kadiran Allah man yasha, tabbas wannan shine gata na biyu da zai yiwa Dije, wato ya aura mata mutum mai daraja da mutunci. Cike da tsantsar gamsuwa da amincewa yace.

“Allah ya karawa sarki Lapia da kwanciyar hankali.. Khadija ‘ya ce awaje na. Mahaifiyar ta Kanwa ce agare ni. Marainiya ce uwa da uba duk sun rasu, Rikon ta ya dawo hannu na. Tabbas a yadda na sani Khadija babu neman auren kowa akanta, A matsayi na na mahaifin ta, Ranka ya dade, Na baka auren ta, Na baka damar auren Dije. Ina fatan hakan ya zamo alkairi a gare ku baki daya...”

Sarki Salman ya samu kansa cikin madaukakin farin ciki na jin an bashi auren Khadija, Yarinyar da yasan a yanzu duk duniya babu wandanda ta tsana kamar masarautar shi..

“How sweet..? Beautiful soul....”

“Masha Allah! Ranka ya dade magana kake?”

Sosa bayan rawanin kansa sarki Salmaan yayi, Yai saurin girgiza kai yana hade fuska tamkar ba shi yayi magana ba. Ya sake jan numfashi yana jin tamkar ana ingiza shi akan lamarin, wanda beyi tunanin shi ba ko kusa, wato kara aure bayan matarsa da suke tare, Ya numfasa tare da cewa Alhaji Isma'il.

“Ina son auren ya zama sirri, bana son maganar ta yadu a duniya. Abin da nake so kawai shine. Ka tanadi waliyanta, ni kuma ni zan zama waliyin kai na.”

“Duk abin da kace dai dai ne ranka ya dade, kuma Khadija yarinya ce mai tsantsar biyayya. Nasan ba zata watsa min kasa a ido ba, bare idan taji labarin kai ne zaka aure ta, nasan zata yi farin ciki tabbas.”

Sarki Salman ya yi shiru, duk da cewa yana cike da tsantsar farin cikin amincewar da aka yi masa, amman ba zai nuna ba saboda izzar sarauta.

“Idan babu damuwa, ina son ayi komai a cikin wata d'aya kacal.”

Cewar sarki Salman cikin nuna iko. Alhaji Isma'il ya sake dukawa tare da kai gaisuwa yace.

“Ko a yau kake son a yi, za a yi shi ranka ya dade da ikon Allah. Allah ya kaimu lokacin yasa a yi damu baki d'aya.”
Chapter 32 · 0% Book details