Sashe 49
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ficewa sukai, Suna gaba yana biye dasu baya. Cikin kayan sarauta da rawanin sa mai kunne biyu. Designer shades din dake idanun sa ya sake amsar kayan jikin sa. Tafiya yake cikin k’asaita , Matashin sarki mai jini a jika. Mai madaukakin kwarjini da hasken annuri. Har kujerar da zai zauna sai da suka Kai shi, Dogaran sa guda biyu na gaban sa. Kujerar tasama wadda zai zauna ta alfarma ce mai dauke da tambarin ...’His royal highness ‘Emir of Basannabas. Salman Aliyu Salmanu. (SAS), Kowa sai da ya rissina masa, Guri ya dau shiru na yan mintinan girmamawa. Wani zama yai na sarauta. Ya mike kafafun sa akan table din gaban sa.. Ta cikin rawani kuwa jan leben sa yake. Kunnen sa d’aya da bluetooth yana sauraron voice-notes din da Galadima ya turo masa kan lalle abunda zai ce kenan idan jawabi yazo kansa...
*MASARAUTAR ‘BULLO...*
(FADAR MAI MARTABA SARKI IBRAHIM HASHIMU)
“Shin fulani da sanin mai gidan ki kikazo nan...”
Cewar sarki Ibrahim mahaifin gimbiya Shaheeda.
“Bappah na kira shi sau ba adadi bata shiga, Nagaji da wulakancin da yake min. Bappah ace zaiyi aure amma bansani ba?” Gimbiya Shaheeda ta karasa fada tana kecewa da kukan makirci.
“Ya isa! Bar kuka.. Ni nasan Salman bai isa ya tsallaka karan dasu Galadima suka ajiye ba. Sai dai idan wata kullalliyar aka shirya..”
“Bappah suma wai acewar su Gimbiya Najwa diyar sa tace ko shi galadiman bai sani ba, Sannan ko ciroma bai sani ba shima. A tak’aice dai Bappah bawanda yasan da auren da yayo.. Sai dai idan Sa’adatu ce (mahaifiyar SAS)”
“Itan da ko kallo bata isheshi ba? Kai akwai kullalliya dai..”
“Ko ni Bappah ca nai sai dai idan ita yarinyar ce tayi asiri. Domin Salman ko kallo mutane basu isheshi ba.. Kuma Bappah yar rik’o ce fa. Ashe ba shine mahaifin ta ba.”
“Eh haka naji labari da nasa akamin bincike. Kiyi hak’uri. Mu dai burin mu baya w...”
Kasa karasawa yai sakamon yadda matar sa ta shigo tana baza kamshi sai rausaya take, An girma ba’asan an girma ba.
“Yar baffan ta ashe kina nan...?” Cewar Gimbiya Asma’u (Matar Sarki Ibrahim ta farko. Mahaifiyar su gimbiya shaheeda.)
“Ina nan Hajia...”
“Ranka ya dade. Afuwan zan dau fulani na yan wasu mintina. Akwai masu jira awaje, Su magatakarda, Da shamaki, Da. dokaje.. Naga jakadiya Yaruwaiyya sai tare-tare, Nasan dai badan ta tsare ka da surutu ba aida kana tare dasu.. Fulani tashi muje, Allah yakara maka lapia, Bari muje.”
Bakin sarki Ibrahim a hangame suka fice, Sai murmushi yake kaman sabon tabi.
*SASHEN TORO BABBA*
(GIMBIYA ASMA’U)
Suna komawa gimbiya shaheeda ta zube a kujera tana yatsina fuska,
“Shikenan na zama kaskantacciya kenan Hajia? Shikenan na zama bani da gata kenan? Hajia kuna raye har Salman ya kara aure? Bayan alkawarin da kika yimin na dagani ba ‘kari? Kwata kwata shekara nawa da auren namu? Amma harya kara aure.”
“Ya isa haka Fulani.. Kibi komai a sannu, Ta karkashin kasa zamu bi. Yadda ta shigo haka Zata fita. Da gundumemin sharri ma kuwa, Bazata koma gidan su ba sai da tabo. Malam na gangare ya tabbatar min da hakan. Ba zaki koma ba sai da boma boman harka..”
“A hayye.. Hajjaju tawa..”
Karaf suka tafa suna shewa..
“Kince plan 1 dinku yayi har kin ganta da mask ko?”
“Eh hajjaju. Amma fa kyawunta ya tsorata ni, shegiyar akwai yalwar gashi da jiki mai kyau. Too bad yar talakawa ce. Dana rena kai na..”
“Haba wa ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Uta din banza? Yadda ta shigo da tsunmomaran kayanta da jikin ta haka Zata fita dashi da dankwalelen tabo ma kuwa..”
“Hajjaju na.. Shiyasa kike sake shiga can cikin zucia ta. Ta gaban goshin Bappah, An buga dake an barki ya zasuyi dake..?.”
“Farin wata...”
“Sai kallo Hajjaju na.. Ki da’de kiyi karko.”
“Kome zasu kitsa miki, Ki bar su a haka..Kuyita tafiya a haka. Muga gudun ruwan su.”
“Ai dama bana nuna komai, Kome suka ce yi nake.”
“Yauwa sai da kwantar da kai... Ina Sa’adatun kuma?”
“Oho mata wallahi... Tana sashenta a yashe..”
Dariya suka shiga babbakawa a tare, Tamkar masu tabin hankali.... Suna yi Suna shirya surkullen da Shaheeda Zata tafi dasu Masarautar Basannabas. Wanda gaba d’aya duk na kauce hanya ne. Haka bokan nasu yazo, Shima da tulin layoyi kowace laya da allura ajikin ta guda 99. Da barkono tsidugu guda 7 an rubuta sunayen Khadija akai. Ta kona kowanne guda d’aya sau bakwai. Kowanne da ranar sa, Da sauran abubuwan kauce hanyar da bazasu lissafu ba........
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *_
_*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*_
*2__7*
*MASARAUTAR BASANNABAS*
Bayan waziri sun gama waya da sarki Salman, ya tara manyan yan majalisa ya sanar dasu abinda suka tattauna. A take kuma ya dauki wayar ya kira Gimbiya Huwaila cewar ta kira babban d'an ya dawo za'a mishi mukami, ta amsa tare da katsewa har da rawarta a cikin bedroom. Bata wani jira ba ta kirashi kusan sau biyar sannan ya yi picking , dan kar ma ya tsaya bata lokaci ta sanar dashi sakon waziri, cike da murna kuwa yace gashi nan zuwa.
*SASHEN GIMBIYA JALEELA.*
Gabaki d'aya ta rasa inda zata sanya kanta taji dadi, tunda Gimbiya Huwaila ta sanar da ita sakon Waziri hankalinta yake a mugun tashe, tabbas tasan duk cikin su itace ke cikin siradin rayuwa saboda rashin samun ‘da namiji. Ta juya tare da kallon yaran nata, wani madacin abu ya tokare mata wuya saboda bakin ciki, yanzu duk gidan wani zasu tafi su barta, babu wanda zata yi iko akai sai dai ayi mata iko da su. Ba abin taje ta kai kukan ta wajan mahaifinta ba sam ba zai saurareta ba, yana matukar yi mata kokari wajan ganin ta kwantar da hankalinta, hakan yasa ba ta fiye kai kuka gurin shi ba, gara taje wajan Galadima ko Ciroma ko kuma Wambai.
Mtwww ta kuma jan tsaki a karo na ba adadi, ta kwalawa yarta Sabeera wacce tana ji amman ta yi shiru taci gaba cin abincin ta.
“Baki ji ina kiranki ba ne Sabeera?”
“Haba Mah gani ga ki amman ace ki ta kwalamin wannan uban kiran, gani ai duk abinda zaki fada zan ji ki.”
“Kunsan dai komai zan yi akan ku ne, so nake naji wai har yanzu kuna tare da d'an gidan vice- president d'in nan kuwa?”
Sabeeera ta yatsina fuska sam bata son yaron nan saboda yaudara gare shi ta masifa, akwai wanda ita take so kuma shi sai wahalar da ita yake yi yana ja mata rai. Ta ture plate din gafe tare da kallon mahaifiyar ta tana cewa.
“Wallahi Mah ko maza sun kare ba zan auri Kamal ba, yaran nan mugun dan iska ne.”
“Toh ke ina ruwan ki da iskancin shi? A jikin ki zaki yafa ko kuwa? Ni a gani na kuna yin aure zai dena. Yaron nan gaba baban shi ne zai rike mulkin kasar nan, ki zama first lady me ye na cewa ga aibun shi Sabeeera?”
“Ni wallahi bana son Kamal Mah, bana son shi I hate....”
“Ya isa karki karasa, abin da nake nufi s....”
Ganin mahaifiyar ta na nema takura mata sai ta mike ta bar mata gurin. Gimbiya Jaleela ta dafe goshi, ita kuwa ta shiga uku, ba magajin sarki ga yaran nata mata duk sai a hankali, idan ta taro wannan sai waccan tayi can gurin. Dole ta mike ta dauki alkyabbarta ta nufi wajan Gimbiya Sa'adatu ranta a d'an bace. Bayan an yi mata iso ta shiga ta tarar da ita a kishingid'e, ta nuna mata gurin zama amman ta girgiza kai alamar bata bukatar gurin zaman. Sai da ta dade tamkar ba zata yi magana ba sannan tace.
“Kina ganin kinyi sa'a a cikin rayuwarki ko? Saboda kin haifi yara maza zaku gaje masarautar Basannabas. Toh wallahi bari kiji, idan har shegen abokin danki ya auri Sabeeera, na rantse da Allah sai kunyi nadama. Nasan duk wani makirci daga gareki ne na sani, toh ko da bokan ki kike yawo na fiku wulakanci da rashin mutunci. Sa'adatu ina son duk wani abu da ya shafeki kar ya kuma rabo ni, idan kuma kin ki uhmmm.”
Gimbiya Sa'adatu ta yi kasa da kanta, bata gane abin da duk Jaleela ke magana ba, sannan ba ta san a cikin ya'yan nata wanne take nufi ba, sai kawai ta shiga bata hakuri cikin karya wuya. Jaleela ta kada alkyabbarta ta fita, yayin da Sa'adatu ta girgiza kai tana nemar musu shiriya idan suna da rabo. Sun ki su barta taji da damuwar da take ciki. Da sunyi abubuwan su suka ga babu nasara sai su takura mata cewar ita ce ta yi musu wani abun. Juyawa tayi taci gaba da yin hailalarta tare da neman Allah ya shiga cikin lamarin ta dana yaranta.
*BAYAN WASU AWANNI....*
*Kishingide* Gimbiya Sa’adatu take, Lokaci zuwa lokaci hawaye kan kwarara a kyakkyawar fuskarta. Yar dattijuwa ce wadda bata manyanta can ba. Kana kallonta kasan akwai jin dadi a tattare da ita, Amman rashin kwanciyar hankali shi ya mai data ta dan rame ta idanuwan ta manya suka kara furfitowa. Fara ce sol tamkar ita tayi kanta. Kallo d’aya zaka mata kasan tanada manyan kyau. Sai dai ace tubarkAllah kawai. Domin Allah yayi mata zatin halitta.