← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 114

Sashe 70

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa nai na zauna ina bin karatun tare da ci gaba da kankare farce na. Sallama naji daga kofar shigowa, na daga kai na kalli hanyar ina mai amsawa. Abin mamaki su Ya Shukrah ne, Sai wasu da alama kawayensu ne tunda ni dai ban san su ba. Kamar nai tsalle naje na rungume su dan murna, amman wata zuciyar ta kwabe ni cewar. 'Kar ki rawar kai Dije, ki tuna cewa ke yanzu kin girma, ya kamata ki nuna musu cewa jiya ba yau bace.' Fuskata dauke da murmushi tare da fara'a na kuma Mike tsaye suka karaso. Ya Hameeda (ni xoxo wlh na manta ainihin sunan ta, Kamar dai haka ne, Man kai na ya tsiyaye) da ta kasa jurewa saboda mamaki tace.

“Lallai har yanzu gigin auran sarkin nan yana kanki Dije.”

Maganar ta bata bata min rai ba, dan yanzu na gano cewa su kananun marasa mutunci ne, yanzu ina cikin gagaruman dan haka duk abin da zasu min ba zai dameni ba ko meye shi kuwa. Murmushi kawai na saki ina nuna musu gurin zama da hannu, suka ki zama sai kallo na da suke yi musamman wata yar dwalf dake ta kallon ciki na tamkar wacce ta hango wani abu a ciki, nai saurin komawa na zauna tare da dora kafa daya kan daya ina girgizawa.

“Dije wai kuwa kinji dadin zuwan mu? Bafa yau kadai muke zuwa masarautar nan ne man ki ba ace bakya nan, honeymoon kuka je ne keda shi?”

Na dan yi murmushi ina wasa da cover din wayar hannu na da na dauka, sannan nace mata.

“Ko daya Ya Hameeda, kawai wata yar tafiya na yi amman ai gashi yanzu kun zo mun hadu. Ku zauna mana sai mu gaisa.”

Suka jinjina kai sannan suka karasa kujerar duk suka zauna. Hadimai suka fara aikin nasu na kawo kayan motsa baki, ni kuma ina hakimce kai kace nice sarkin saboda yadda nake karkada kafafu...

_Afuwan lovelies.. A bini bashi😅🤲🏻Insha Allah next page zaiyi tsawo.. Masu comments, Ina godia sosai, Sakon ku yana isowa gare ni.. Kibiyar ajali... Zai cigaba da zuwa muku a hankali cikin nishadantarwa da fad’akarwa... Kaunar kauna❤️❤️_

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

PG: 11&12
BOOK 2.

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

......Kallon yanayin parlorn suke yi da alama ya tafi da duk wani imani nasu saboda sun kasa sauke idanunsu daga dubawa. Ni kuma sai murmushi nake yi nasan ko babu komai zasu gane cewa maraici ko talauci basu hana d'an adam yin arziki, inda ma aka samu matsalar zuciya ta Sam ta kasa amsar Salman a matsayin miji na.

”Ina kuma mai gidan naki..?”

Cewar Ya shukrah tana mai ci gaba da karewa gidan kallo.

Na shiga jujjuya amsar da zan basu, Don ni rabon da na sashi a idanu na tun rannan dana same su shida Shaheedah a bedroom d'in sa, Ni kunyar sama na keji wani lokacin saboda kar ya dauka har zuci nake wannan acting din.

“Suna meeting ne.. Shi da yan majalisar sarki.”

Tabe baki Ya Hameeda tayi tana mai kallon kayan kwalam da makulashen gaban su. Ni kam na shiga tambayar su Kawu Daddy da Mami..

“Sunanan qalau.. Amman Dije yaushe kika dawo nan sashen? Kamar da ba nan muka kawo ƙiba ko.?”

“Eh Ya Shukrah! Daga baya na dawo nan d'in..”

“Ina kuma kishiyar ki.....? Ita anan saman take kenan, Ke a kasa?”

Sai da nai murmushi tare da sauke kafata na kalleta sosai yadda zata fahimci bayanin da zan jefa mata sannan nace.

“A'a ai ba zai yu a had'a mu haka ba, kinsan gidan sarauta ba kamar sauran gidajen mutane bane da za'a iya ajiye mata biyu a part d'aya, dole ko wacce da nata bangaran.”

“Yanzu dai kina nufin nan duk naki ne?” Cewar Ya Hameedah tana son jin tabbaci.

“Eh nawa ne.”

Na bata amsa a takaice ba tare da na kuma yin dogon bayani ba, dan na lura har yanzu mamaki suke yi.

“Amman dai kafin mu tafi zaki had'a mu da shi angon mu gaisa, ni ban taba ganin inda ango be san ainahin yan uwan matarsa ba sai yanzu. Ya dai kamata mu ganshi, dan yasan mu muma mu san shi ko Hameedah?”

“Kwarai ma kuwa sissy, wai duk tsahon lokacin nan bai taba zuwa gida ya gaishe da Daddy ba bare kuma Mami, ke kuma tunda kika samu duniya shikenan ba ruwanki da neman mutane.”

Ganin suna shirin gaya min magana a gaban kawayensu da ban san ina maganar zata iya kaiwa ba yasa ni saurin nemo amsar da zan basu cewar.

“Kai ai shi ba ya san hayani, baki ga ko da ina gida be taba zuwa tadi ba? Shifa sam baya san surutu, ni kai na duk surutu na idan ina gabansa hadiyewa nake. Shima Daddy ya sani dan a bakinsa na fara jin cewar sarki Salman baya san magana da hayani.”

Suka kalli juna cikin zaro ido tare da rike baki alamar mamaki, ni kuma na gaya musu iya gaskiya ta d'an kara suyi zaton irin mazan nan ne masu yawan surutu ko shisshigewa yan uwan mata.

“Ke nan muma yanzu ba zamu samu damar ganin shi ba?”

“Gaskiya dai, tunda kunga yanzu yana meeting ban san ma lokacin fitowarsa ba. Babbar matsalar ma ba nice dashi ba Shaheedah ce, idan taga ina zarya gurin shi sai tai zaton wani abu. Amman kuyi hakuri duk sanda kuka dawo zan yi kokarin hada ku dashi sai ku gaisa.”

“A'a a'a kedai kawai kice boye mana shi kike yi, lallai Dije abin naki dada shahara yake yi amman ba komai.”

Ya Hameedah ta fada tana janyo bowl d'in pepper soup d'in cow leg, daga nan suma sauran suka fara dibar abinda zasu ci. Wayar telephone dake can gefe ita tai ringing, ba kowa bane face Salman dan shi kadai ne yake kira a cikin ta idan yana nema na urgent. Cikin rawar jiki hadima ta dake kusa da gurin ta dakko ta kacokam ta kawo min, na karba sai dai ban daga ba saboda jan aji, ta katse ya sake kira, still ban daga ba sai da ya sake kira karo na uku sannan nai picking na kara jikin kunne na.

“Please..I need your help.”

Cike da takama kamar ina gabansa nace mai.

“Yaushe fa.?”

Yace.

“Yanzu please.”

“Ina da baki ne, sisters dina sun zo. K...”

“Na ce yanzu.”

Ya fada cike da nuna iko, karo na farko kenan da ya nuna min ikon sa a kai na. Ya kuma katse nai murmushi dan kar su yi tunanin wani abu na hada da cewa.

“As you wish.”

“Ya fito daga meeting d'in kenan?”

Ya Shukrah ta tambaye ni cikin zakuwa, ashe duk kunnuwan su yana kai na oho ni Dije.

“A'a bashi bane ba.”

Na samu kai na da shirga musu karya, nan san me yasa ba haka kurum bana son su hadu dashi yanzu, kodan nasan har yanzu ni kai na ban san matsayina a gurin sa ba.

“Ku gama ci bari naje na dawo.”

Na fada tare da tashi na shiga daki. Sake gyara fuskata nayi na kuma dauki mayafi na yafa sannan na fito na bi ta d'an wani corridor yadda ba zasu gane nayi wani gurin ba, cas na fada sashen Salman ina ta mamakin wannan kiran nasa da ya yi min.

Kamar yadda nayi tsammani hakan ne ya kasance, wato sashen nasa shiru sai fadawa dake aikin gadin ko wane sashe na part d'in. Duk inda na gitta sai sun gaishe ni har na karasa bedroom d'in sa, wani irin kauri naji wanda yasa ni kwarewa babu shiri, nasa hannu na toshe hanci na ina kalle-kalle dan son hango inda yake.

Bathroom naji an bude, nai saurin kallon gurin naga shine ya fito, sai dai ya rufe duka fuskarsa da towel d'in wanka alamar shima mafita yake nema.

“Yar jarida...”

Nija ya fada a hankali, ban san lokacin da na harare shi ba.

“Sunan da nake dashi a gurinka kenan? Tukunna ma wannan kaurin kuma fa daga ina?”

“Kina ina please.?”

“Gani nan.”

“Toh d'an matso.”

Kamar wata sokuwa haka na matsa kusa dashi, yasa hannu ya lalibo ni bayan ya gama yawo da hannunsa a jikina.

“Kinji warin nan ko? Toh nima haka naji shi har ya sani amai. Dan Allah ki taimaka kisan yadda zaki sa na dena jinsa.”

Haushi ya kamani, me yake nufi to da zai ce na kawar masa da wannan fitinannan kaurin bayani ni kai na ban san ta ina yake biyowa ba. Ko yana tunanin nice na saka masa har ya yanke shawarar kirana dan na gyara?

“Nima fa ban san daga ina yake fitowa ba, dama na sani ne da sauki.”

“Please yar jarida bazan iya zama a cikin dakin ba.”

“Ikon Allah, wai laifi na ne?”

“I dunno, ni dai ki taimaka min bana son warin.”

“Shikenan to sakar ni naga me zan iya yi.”

Babu musu ya sake ni nasa mayafi na nima na toshe hanci ina ta karanto adduoi . Na dinga dube dube amman banga komai ba, na kalleshi yana tsaye yaki bude fuskar kamar wani karamin yaro. Cikin sauke numfashi na mike tsaye ina cewa.

“Toh waye ya shigo cikin dakin? Ni dai na duba banga komai ba wallahi da yake sa wannan kaurin.”
Chapter 70 · 0% Book details