← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 114

Sashe 80

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Banji dadi ba da ka tabbatar mata da cewa ni ne, naso ka barta a sunan ni Chiroma ne. Shegiyar yarinya ka bibiya bokayenta ba a kasar nan suke ba, dubi yadda muke b'arin kudi akan ta amman kamar muna yi akan iska haka aikin yake wucewa ba tare da komai ya same ta ba. Duk duniya a yanzu babu wacce na tsana sama da yarinyar can wallahi.”

“Rabu da ita ai idan tasan wata to bata San wata ba, zamu yi maganinta tun kafin wadanda zai auro su shigo. Karka ga yadda Humaira take masifar son Salmanu, amman shi be ma san tana yi ba taki ta bayyana masa saboda gudin wulakancinsa.”

“Kuma haka ne fa Wambai, wallahi idan muka samu yaran nan suka shiga daga ciki, ba wannan yarinyar ba kadai ba, hatta Shaheedah sai ta dawo karkashin mu.”

“Uhmmm-uhmmm Galadima, gwara dai mu dinga rage kiyayyar mu akan Shaheedah, kasan dai mahaifinta shi da kansa yake yiwa kansa duk wani tsibace-tsibbace a masarautarsa ta Bullo. Idan muka shiga gonarsu tabbas zamu Iya rasa mukaman mu ba mutunci ne dashi ba kasani. Gwara dai mu tsaya Iya Salmanun da ita wannan talakan takalak din matar da ya kwaso.”

Galadima ya jinjina kai da haka har suka karasa runfar da sauran yan majalisar suke suna jiran fitowar sarki Salman dan su karasa cikin fada.

Ni kuwa ina zuwa sashen Ammi na tarar da wasu matasan yan mata, ban gane su sam dan babu wacce na taba gani a cikin su. Na yi sallama duk suka juyo suna kallo na amman babu wacce ta amsa min sallama ta sai Ammi wacce ke zaune tayi kasa da kanta da alama ba mutanan kirki bane ba. Har na karasa kusa da Ammi babu wace tai min magana bare gaisuwa, hakan ya kuma girmama hasashena akan sanin su waye. Muka gaisa da Ammi cikin mutunci sai dai da ka ganta kasan ba ta cikin walwala.

“Baki kika yi ne Ammi?”

Kafin ta bani amsa naji muryar daya daga cikin yan matan tana cewa.

“Mu ya kamata mu tambaye ta bakuwa ce ke ko kuwa, dan bamu sanki ba a cikin masarautar Bassannabas.”

Murmushi na yi cikin rai na ina cewa kila jinin masarautar ne, dan naga Isa da kasaitar ta yi yawa. Amman dai ban ce komai ba saboda a gaban Ammi ne da na gaya musu abinda zai hana su yin walwala a yau.

“Munaya kuyi shiru dan Allah, wannan ko babu komai Yaya ce a gurin ku tunda matar shi ce.” Da sauri suka hada baki wajan furta.

“Wa...!?”

Nai saurin basu amsa dan naga Ammie tana jin nauyin furta sunan shi nace dasu cikin gadara.

“SAS, idan kuma baku gane ba ina nufin Sarki Salman Aliyu Salman. Nasan yanzu kun fahimce ni tsab. Kuma zaku gane ni kodan gaba.”

Duk sai suka bi juna da ido suna bude baki, na saki murmushi ganin yadda suke mamaki dan bamu taba haduwa dasu ba, basu sanni ba nima ban San su ba sai iyayen su kawai. Na dakko jarkar ruwan da na gani kusa da Ammi na bude tare da zuba mata cikin cup na mika mata ina cewa.

“Ammi sha ruwa ki kwanta, naga kamar har da bacci a idanunki.”

Naji dadi da bata musa min ba, ta karba Tasha na janyo mata pillow tasa kai tana lumshe idanuwa. Nai saurin mai da kallo na gurin su ina kare musu kallo, daga masu riga da wando sun dora wata munafukar after dress, sai masu dogayen riguna da suka bayyana surorin jikin su, na ce.

“Amman dai baki ne ku ko?”

“Ke dalla can bama san bariki kinji, mu zaki rainawa hankali dan kina matar juya da bai Iya ajiye magajinsa ba kamar yadda aka ajiye shi. Kin ganmu nan ko? Kakaf din mu jinin sarauta ne, jinin da yake yawo a mahudanar mijin naki, shine muma yake yawo a jikin mu, Kinga har gobe zamu Iya samun sarautar nan da yake kai.”

Na saki murmushi Ammi dai ba ta sake cewa komai ba dan taga nima dai-dai nake dasu, kuma Ina Iya yina wajan ganin ban furta abin da zai sa ta yi mamaki na ba sai dai su nayi su dinga jin kamar zasu tsire ni. Ganin naki magana yasa Baheeya yin magana, gata yar karama amman rashin kunya a bakinta kamar me, tace min.

“Kin yi shiru ko babu amsa?” Ina shafa fuska nace.

“Bani da time din magana daku yanzu, amman zaku Iya zuwa ku bincika wacece ni ta yadda ba zan dinga baku wahala ba wajan jiran amsoshin tambayoyin ku.”

Carab Nadiya ta cabe zance.

“Kema kin zata yana haibuwa ne kika aure shi? Aunty Shaheedah fa har yanzu ta kasa haihuwa saboda ance shi bashi da lafiyar da zai haihu.”

Wannan karan mamaki ne ya cika ni, na kalleta ganin ta yar firit da ita amman wai har ta Iya yanko wadannan manyan zantukan. Na rike baki tare da kallonta nace.

“Ke yarinyar nan har kin fara zancen wanda yake haihuwa da wanda bayayi? A bakin wa kika ji cewar baya haihuwar?”

Ta murguda baki tana fari da idanuwa irin na rashin kunyar nan, su kuma sai faman jinjina mata suke yi. Sabeera ta mike tana dariya tana tafa hannaye tace.

“Toh karya tayi ne? Da yana haihuwa kila da yanzu Aunty Shaheedah tana da yaranta. Amman da yake juya ne kinji shi shiru, dama suma ba ta hanyar Allah aka samar da s.....”

Ban san lokacin da na tashi naje na shako wuyan ta ba, duk suka taso suma zasu shigar mata nai saurin juyowa Ina musu wani irin kallo mai cike da fita hayyaci, duk sai suka tsaya suna huci kamar wasu zaku na nace.

“Duk iskancin da zaku yi karku sake ku iskanta min miji, idan kuma ba haka ba zaku yi yin nadama marasa tarbiya kawai. Kuma ku tashi ku fita tunda ba sashen iyayen ku bane.”

Na sakar mata wuya na tsaya kuma Ina jiran su fita dan idan suka tsaya komai zai iya faruwa tsakanina dasu. Don basu sanni bane, Oganniya nake ta Gajiyalle mai yar hakiya.. Dijangala yar baffanta. Aikuwa suka fice suna ta zage-zage, naja tsaki tare da komawa na zauna raina a mugun bace. Ammi ta dinga lallashi na tana cewa na dena biye musu idan ba haka ba abubuwa zasu kara baci tsakanin mu da iyayen su. Da kyar na samu na iya hakura saboda taji dadi, amman a zuciya ta na kuduri aniyar sai na gyara musu zama a cikin masarautar nan, Bayan mun dan yi hira ne na tashi na koma sashe na.....

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.
_I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_A dear page goes to a dearest one.. Dear billyn Abdul... May you be forever blessed😍❤️kaunar kauna tawaje na.. 🧚🏻‍♂️_

_PG:18_
_BOOK:2_

*GIM. KHADIJAA*

*Ina* shiga sashe na zauna a parlorn kasa ina kallon tv dake yi ita kadai. Can na canza channel din zuwa iqraa inda suke karatun alqur’ani. Takwas dai dai, Saura awa d’aya naje wajen Salman. Nagaji saboda da yar tazara tsakanin sashen da nake zuwa na Ammi. Kitchen na shiga na samu Na’imah amintacciyar hadimata da Gwaggo ta fada ta samamin. Na sata ta matsemun ruwan dankalin turawa guda d’aya, Na hada da ruwan lemon tsami d’aya shima. Zama nai a kitchen din na shafe fuskata dashi da kuma hannu na. Bazan manta ba Adda Maryama ce tabani sirrin yana gyaran fata sosai. Minti goma sha biyar yai na wanke da ruwa mai dumi, Sannan nayi wankan turare (bath khumrah) Banyi wata kwalliya ba, Na dai canza kaya na zuwa doguwar riga ja mai dogon hannu, Na yafa mayafin akai na, Turaruka masu sanyin kamshi na shashshafa: Shekha/Night oud/Danal banat) Na dan shafa man lebe kadan a baki na.

Zama nai ina jiran lokaci ya cika, Yana cika na mike na shiga hannu na d’aya rike da jotter da na rubuta komai. Bakina dauke da sallama na shiga. Yana zaune akan dinning table hannu biyu ya dafe kumatunsa, Dagowa yai yana kallo na, Nai saurin saukar da kai na kasa.

“Barka da dare....”

“Barkan mu....Zawjati!”

“Ga ni..”

“Bismillah... Zo ki zauna.”

Mik’ewa yai ya janyo kujerar kusa dashi yana nuna min, Zama nai ina cije kasan lebe na, Saboda ciwon mara nakeyi nasan nan Kusa mai jar mota zai zo.

“Ina jinki... Naga kinyi abbreviating wasu words din.”

Bude jotter din nayi, Ina nuna masa daga inda nake zaune, Mikewa yai ahankali ya zagayo ta wajena, Ya saqalo wuyan sa saitin fuska ta. Cikin wata irin murya ya nuna wasu kalmomi,

“Wadan nan fa...?”

Na shiga raba idanuwa, Na kasa magana

“Uhm....Me suke nufi....? Khadijaaaa”

Ajiyar zuciya na sauke, Turaren jikin sa sai sani cikin wani yanayi yake. Ahankali cikin dauriya nace,

“ NSMHSHDSWDYAKGTB na nufin: Nace su Mama Huwaila sun hadu dasu waziri da yamma a kofar gabas ta bayi.”

“Nan fa..... Uh hummm.?”
Ya furta Uhum din cikin kunne na, Ba shiri na mike ina sosa kai na,

“Zan tafi..”

“Ina zaki tafi?”
Ya tambaya yana daria wato yana sane kenan yasan abunda ya aikata.

“Zan koma inada abun yi..”

“Ai nan dinma ba shirme kike ba, Assignment na baki kike presentation.”
Chapter 80 · 0% Book details