← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 114

Sashe 37

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda yai mafarkin nan yake jin jikin sa yana rawa, Tunani ne dankare a kirjin sa. Amma ya kasa samun nutsuwar yadda zai warware shi. Dafe kansa yai ya rintse idanun sa. Yana zaune a fada amma bai bada damar aiwa kowa iso ba. Jakadiya sai zarya take tana sanar masa isowar mutane. Dakyar ya bari tabawa waziri dama ya shigo,

“Allah yaja zamanin sarki adali. Allah ya Kara Maka lapia da nisan kwana mai amfani ranka ya dade!”

Hannu sarki Salmaan ya daga masa yana dafe da habar sa,

“Allah ya tausasa ran sarki! Allah yakara maka dattako baban kowa. Shin akwai abunda ke damun Sarkin mu ne? Sanar min ko menene shi shugaba na.”

Sarki Salmaan ya d’anyi murmushin jin dadi. A duk duniya waziri na cikin sahun mutanen farko da yake so. Saboda a kullum sai ya tambayi abinda ke damun sa yana kuma k’ok’arin ganin ya yaye masa matsalolin sa,

“Waziri... Nayi mafarki irin na kwanaki. Menene gaskiyar al’amari?”

“Allah ya karawa sarki lapia. Tabbas shakka babu zamu iya fassara hakan da cewar sharri ne na mafarki. Amma kuma idan aka auna abun a mizanin hankali za’a gano akwai kullalliya ko makircin bil adama..”

“Menene mafita to...?”

“Kamar dai yadda na nemo maka hayakin nan da ka yiyyi kwanaki? Yanzun ma zan koma wajen Malam din na karbo maka wani..”

Kada kai SAS yayi kafin su cigaba da magana data shafi fada. Mikewa sarki yayi. Dogaran sa suka rufe shi ya wuce sashen sa jin yadda yake wani irin jiri mai gigita kwakwalwa, ga ciwon kai da yake kuma barazanar faduwa. Waziri ne ya cigaba da zaman fadar, inda ya zauna dasu Galadima, ciroma, wambai da sauran su. Ya sanar da su rashin lafiyar sarki Salman tare da umartar wani babban hadimin sa da cewar yana son ya kuma karbo masa wannan hayakin a wajan malam kamar yadda ya taba karbowa kwanaki.

Galadima ya kalli ciroma suka saki wani murmushi ta cikin rawanin su, da alama wata damar ce zasu samu wajan kuma yiwa sarki Salman wani makircin. Nan dai suka nuna jimami da alhinin rashin lafiyar, amman a zukatan su ba haka abin yake ba, wata muguwar manufa ce a rasu. Ciroma da kanshi yaje ya karbo wasu kayan tsibbun wanda yake dauke da tsana mai karfi tsakanin sarki Salman da mahaifiyarsa, ganin ya fara mafarki da ita sun tabbatar zasu iya shiryawa, wanda shirin zai iya wargaza musu duk wani shiri da suka yiwa masarautar. Shi kuma tunda ya shiga daki ya kwanta yake wani irin bacci mai nauyi da ko wane irin ihu ba zai iya farkar da shi ba.

____Cikin wasu furanni masu launin shudi da rawaya yake hangenta, sanye da kaya na alfarma sai faman murmushi take yi. Shi kuma yana daga gefe zaune da jarida yana dubawa sai idanunsa suka sauka akan ta, ya dinga kallon ta yana son kuma ya gano wa take yiwa wannan fara'ar mai tsadar gaske. Ya mike cike da kasaita yana isa gurin da take sai yaga shi take yiwa dariyar, ya kuma kallon ta tare da kamo hannunta sai kawai ta shige jikinsa tana kankamewa, murya a raunane yaji tana cewa.

“Nagode ya kai annurin da yake haskaka min zuciya ta, tun dazu nake nan ina jiran zuwanka.”

Shafar bayanta kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shan kamshin nan nasa yana sake sanya ta cikin begen sa, ta dago fuskarta tana kallon tashi tace.

“I love you my hubby.”

Sai ga Shaheedah tazo gurin, gabansa ya yi mugun bugawa, amman sai yaji Dijen ta rike shi tana cewa.

“Kadena jin shakkarta saboda ita ba komai bace face azzaluma, ba ta son ka shi yasa take cin zalinka. Allah ya fita babu abin da ta isa ta yi maka ina tare da kai my hubby.”

Ya samu kansa da tsayawa a gurin na ta duk da tsoran da yake tattare da shi na Shaheedah. Daga gefe ta tsaya itama tama miko masa hannu wai yaje, sai ya kalli Dije ya kuma kallon Shaheedah yana tunani yadda zai yi. Zuwan wani saurayi gurin yana kuka shine yasa Shaheedah barin gurin, Dije kuma ta kama shi suka tafi daki. Sai ya kuma jin nutsuwa yana yiwa Allah godiya da ya bashi Khadija matsayin mata abar alfahari. Sam be yi zaton a bacci yake ganin hakan ba sai sa ya farka ya ganshi a tsakiyar gadon sa yana juye-juye a kai. Tabbas yaji a jikinsa Khadija itace zabin zuciyar shi, dole ne ya ci gaba da farautar neman auran ta koda kuwa yin auran zai janyo abubuwa da dama a cikin masarautar. Sai da ya yi wanka ya shirya sannan ya nemo amintaccen bafadensa wato Al-hassan, suka kebe yace masa yana son a ci gaba da shirye-shiryen auran sa kamar yadda suka fara. Ya amsa sannan ya sake komawa wajan Alhaji Isma'il wanda ya tabbatar da cewar zai je dangin mahaifin Khadija ya sanar dasu, idan yaso yana dawowa sai ya sanar da a shirya daurin auran.

Haka kuwa aka yi Alhaji Isma'il be sanar da su Mami zai je ba, sai shiryawa ya yi da shatara ta arzikinsa ya je ya sanar dasu komai, suma dai be gaya musu wanda zata aura ba, ya ce musu dai ya amince da tarbiyar yaron dan gidan mutunci ne iyayensa masu daraja ne. Suka amince tare da bashi ragamar aurar da Khadija, a cewar su ai shine uwa da uba na ta dan haka babu wani abu da zasu ce sai fatan Alkairi a cikin auran. Bayan ya dawo ne yake sanar da Mami cewa yaje can sun gama komai sannan ya kira yan uwansa suma ya gaya musu sunce idan lokacin yazo yasu bar komai su zo ayi dasu. Bata damu ba dan bata yi zatan wani mai daraja za'a aurawa Khadijan ba.

Tunda aka fara wannan abun Dije da Mas'oud basu yi zaton ba junan su zasu aura ba, basu zaci hangen da kawu daddy ya yi ba akan su yake ba, sai da abin yazo gab har ana sauran sati daya biki sannan ne yace da Dije zai kuma yin magana da ita idan ya gama komai. Kasan cewar da yamma ne ta gaya mata kuma Jumma'a ce yana ganawa da mutane yan kasuwa, shi yasa ta bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu.

°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°

*WASHE-GARI*

Tunda Kawu daddy yace zamu yi magana daren ranar ban runtsa ba har wayewar gari. Kasan cewar asabar ce, Ina malale akan gado gaba na sai dukan uku-uku yake. Shin akan me zamu tattauna? Nasan tabbas lefi nayi. Kuma duk yadda akai akan bana bari TK ya dakko ni wani lokacin idan na fita. Ko kuma su Mami ne suka qulla min qullalliya a gurinsa? Ko kuma zancen iyayen Mas'oud zai min kila yace nace ya turo. Ganin sha biyu ta kusa ban ci abincin safe ba hakan yasa na diro daga gado ina mika, Band’aki na shige nayo wanka na canza kaya cikin doguwar rigar A line marar shape. Na taje kai na dakyar saboda inayi yana zamewa saboda santsi da cikar sa, Na d’aure da ribbon. Dauri me sauki nayi na shafa man baki na sauka kasa. A dinning area na tarar da Mami dasu Ya Shukrah suna cin abinci suna hira.

“Mami ina kwana..? An tashi lapia.”

“Lapia lou..” Ta bani amsa a tak’aice tana mai cigaba da kurbar tea dinta.

“Ya Shukra ina kwana? Ya Hameeda ina kwana.”

Kowannen su ya amsa babu yabo babu fallasa. Ganin haka na mike na daddebi abinda zan ci a plate na koma k’arshen parlorn nakeci acan. Sai bayan na kammala ina zaune ina karanta wani book na wajen aiki sai ga Kawu daddy yafito. Sanye cikin jallabiya.

“Kawu daddy...Barka da safiya Kawu daddy! An tashi lapia?”

“Alhamdulillah Khadija.. Muje ko?”

“Toh Kawu..”

Su Mami suka bimu da kallo, Yana gaba ina biye da shi ya shiga parlorn sa ya zauna akan babbar kujera ni kuma na tsakure a gefe,

“Hau kujera ki zauna mana.”

“Nan ya isa Kawu....”

Gyaran murya yai. Ya rage volume din CNN dake faman yi,

“Kafin dai mu fara magana ina son tabbatarwa kai na Kamar yadda kika sani, wannan maganar da muka yi dake a baya na aure ita ce ta kuma tasowa. Amman Shin ki na da saurayi ne dake zuwa neman ki gidan nan? Kai bama wannan ba. Akwai wanda ya taba yi miki zancen aure? Dan ni dai nasan da akwai zan sani ko kuwa..? Dan naje munyi magana da dangin mahaifinki, sun kuma bar min komai a hannuna cewar na yi komai da komai a game da auranki.”

Wani daskararren abu naji ya tokare min a wuya. Shin menene yake shirin faruwa dani.? Ko wani sharrin aka kullamin?

“Magana nake miki Khadija kin yi shiru...”

“Kawu daddy.. Ba.. babu!” Na samu kai na da bashi amsa haka! Kawu daddy ya sake yin shiru na dan wani lokacin kafin yace,

“Tun wannan dai wanda nazo nace miki na yaba da hankali da tunaninsa, gashi kai tsaye ni ya nema kinga kenan da gaske yake yi ko?”

Sake samun Kai na nayi da kada kai. To me zance? Shi kansa Mas’oud din yana namiji ya boye alakar mu bare ni Mace?

“Toh shikenan! Alhamdulillah tunda babu wata magana tsakanin ku da wani. Kinsan babu kyau neman aure akan aure. Wannan yaro me hankali da dattako ne, ya fito daga gidan mutunci. Yana neman auren ki.. Kuma azahirin gaskia ma nace na bashi. Saboda ko da kina da wanda kike so din a matsayina na mahaifi agare ki. Babu wanda ya zo ya same ni. Manya basu shigo ciki ba, Dama already blood sample/genotype dinki sunyi kyau. Kowa zaki iya aura, Kuma Khadija...”
Chapter 37 · 0% Book details