← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 114

Sashe 88

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai dai lokacin da ya gama furucinsa ya balle min bra din gabaki daya, ni kuma naji wani irin abu yana taso min a tsakiyar kirjina wanda na rasa komenene. A hankali yasa hannu ya zare bra d'in, duk da cewar idona a rufe yake, amman yadda naji komai tsit ne ya tabbatar min da cewar kallonsu yake yi. Na kasa bude ido bare na gani saboda duk jikina a mace yake, gashi hannuwana suna gefe ko Iya dagawa bana yi.

Bakinsa kawai naji akan daya yana wani irin abu da harshensa.... Nan da nan na fara wata irin kyarma jikina yana rawa Sai faman girgiza kai nake yi alaman na shiga wani stage din na daban. Ganin Ina nema fita daga hayyacina yasa shi dakatawa tare da rungumeni ya hade fatar kirjinsa da albarkatun kirjina, yana zura min harshensa cikin kunne yana yawo dashi, daga bisani yaci gaba da magana cike da shauki.

“Ba zan iya jurar ganin bacin ran ki ba koda na dakika daya ne ba, wannan shine dalilin da yasa a koda yaushe nake rokon Ubangiji mahalicci akan wannan kyakkyawar halitta da ya yi mun baiwar mallakar ki a mastayin matata ta auren sunnar ma’aiki (S. A. W). Tun ranar da Allah yayi mun baiwar mallakar ki a matsayin matata a wannan ranar nafi kowa farin ciki a rayuwa. Ina kaunarki yake Abokiyar ta. Kin San Annabin Rahama (SAW) ya gaya muna cewa ana iya Auren mace saboda kyawon ta, Asalin ta, Kudin ta ko Riko da Addinin ta, amma sai yace idan da zamubi shawarar sa to mu auri Mace mai Riko da addini. Alhamdulillah. Na godewa  Allah da yadani da mace mai riko da Addini wacca Annabin Rahama (SAW) ya baiwa kowanne d'a namiji shawara ya Aure.”

Ya yi shiru tare da sanya bakinsa cikin nawa ya fara sarrafawa cikin kwarewa, nifa gabaki daya na manta da wa nake tare balle na tuna cewa jikina mallakin Mas'oud ne. Gabaki daya Salman ya mantar da ni a wace duniya nake bare na iya tantance da wa nake tare cikin wannan daddad'an yanayin. Sai da ya rabani da komai na jikina ya kuma rikeni gam kamar za a kwace masa ni, naji tattausar muryarshi yana magana.

“So gamon jinine, tabbas sonki ya zamo jinin jikina saboda kaunar da nake miki my love, jinina tare da naki yake kewayawa ni dake mun Zama daya a duniyar Masoya, ina fatan ko a gidan Aljannah Ubangiji ya had'a mu a matsayin mata da miji mu rayu har gaban abada. Kin fita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar mace sai ke, Koda yake idan nace kamar babu kyakkyawar mace kamar ke ban yi miki adalci ba, nidai a gurina kece Sarauniyar mata kuma 'yar autar mata daga ke na rufe babin soyayya.. Yau zan nuna miki yadda nake jinki a cikin jinina.”

Yana kaiwa nan naji ya daukeni gaba dayana ya sauka daga gadon. Idona a rufe suke, shi yasa ban san ina muka dosa ba. Sai kawai saukar ruwa naji a kanmu. Sassanyar ajiyar zuciya na sauke tare da kuma cusa kaina cikin kirjinsa da ruwa ke sauka dan na fahimci shima babu riga a jikinsa sai sulbin fatarsa da na ruwan dake jikamu. ina jiyo sautin murmushinsa.

Murmushi mai sanyi sarki salman ke saki yana kallon yanda ta kunshe kanta a kirjinsa. Hanayenta duka sakale da wuyansa. Bakinsa ya matsar saitin kunnenta ruwan na cigaba da sauka a kansu. Cikin wata irin murya yace min,

"Wanka fa Zaki min.”

Bammasan lokacin dana d'agoba tare da sakin hannuwana dake sakale a wuyansa. Saurin rikoni yayi da kyau jin zan subuce masa. Tare da azamar manna bakinsa cikin nawa dan ihu na wage baki zanyi saboda tsoratar da nai na tunanin zan fadi kasa. Da wannan damar yayi amfani wajen sai-saita rudanin da nake ciki. Kafin ya ajiyeni a hankali har lokacin bakinsa na cikin nawa. Saurin mannewa nai da jikinsa na kankamesa dan kunya. Bana son ya ganni a yanda nake.

Bakinsa ya zare yana sauke numfarfashi, ya mika hannu ya jawo sosan wankansa tare da tsiyaya shower gel a kai ya fara gogamin a gadon baya.

Duk zamewar da nake da sinne-sinnen kai sai da yayi min wankan nan shima ya sakani nayi masa. Sai dai har aka yi aka gama idanuna a rufe suke. Inaji yanata min dariya kasa-kasa. Rigar wankansa ya saka min, ai kafin ya gama saka tashi tuni na nufi hanyar fita zan gudu ya rikoni.

"Zo kiyi alwala sai ki gudu sarkin kunya."

Fuska nadan kumbura. Sai kuma na juyo kaina a kasa nai alwalan. A zuciyata kuwa mamakin yanda na kasa daukar wani mataki nake yi. Sai kace ya kafeni a dakin. (Ahh munafuka dije.. Soyayya ce ta rufe miki idanu😏)

Alwalar nayi muka fito tare. Inata faman sinne kai. Ba tare da nasan ya matso kusa da ni ba sai ji nai kawai ya zare hular wanka da ke kaina, wadda ta bama gashina kariya da ga jikewa. A hannunsa ya tattara gashin ya tufkesa yanda bazai dameni ba.

"In ara miki rigata?"

Ya fada yana dora hannunsa akan habata ya dagomin fuska. Idanuna nai saurin lumshewa dan banason mu hada idanu. Nadan bata fuska muryata can kasa nace,

"Yanzufa nai wanka amma ka sakani karayi. Ka barni naje dakina zansa acan.”

Durk’usa wa yayy gabana hannayensa duka cikin nawa yana murzawa a hankali.

"Yau matata a dakina zata kwana. Ko kin manta da alkawarinmu ne?.”

Kallonsa nai da sauri, da iya gaskiyata nace,

"Ai babu zancen kwana a daki daya dai".

"Inji wa?..."

Yayi maganar yana waro idanu waje.

"Na rantse bakace da kwana anan ba.”

Fuskarsa da murmushi yace,

"Toh yanzu na fada. Akwai kwana daki daya a cikin game d'in. Akwai cin abinci tare. akwai wanka tare. Akwai zaman hira tare........"

"Gaskiya wannan wayo ne.” Na katsesa da sauri.

Mikewa yayi yana dariya ya nufi wajen kayansa. Na bisa da kallo kawai ina yaba tsarin halittar da ubangiji yai masa a cikin raina. A bazata ya juyo ya kamani. Da sauri nai kasa da kaina. Dariya ya karaso yanayi. Ya ajiye kayan daya dakko yana fadin,

"Anaso ana kaiwa kasuwa. Ki rage gulma Allah.”

Harararsa nadanyi. Ya wani lumshe ido irin hakan ya masa din nan.

"Harara na miki kyau."

Ya fada cikin kunnena yana sumbatar kuncina. Ban iya tanka masa ba ni dai. Ya mikomin farar jallabiyarsa.

“Tashi ki saka ki tayani sallah.”

"Taya salla kuma? Dama ana taya wani sallah ne?”

"Eh mana. Tunda ke matata ce zaki Iya taya ni.”

Jinai zuciyata ta dan tsarga, dan yanzu kam hankalina ya fara karkata a wani hasashe na daban. Sai dai kuma nai azamar cewa 'kai a'a bazai aikata min hakaba har sai na yarda'.

Da wannan tunanin na saka rigar ina kare kirjina. Hijjabin daya mikomin na amsa, saida na saka sannan na saki hannuna danaketa kare kirji. Shi dai yayi kamar baiga abinda nake yi ba. Ya hau saman sallayar daya shimfida yana nuna min bayansa. Babu musu na tsaya. Cikin nutsuwarsa ya tada sallar.

Munyi salla raka'a biyu, ya juyo ya dafa kaina yayi addu'oi. Ni dai kaina a kasa na kasa dagowa. Baice dani komai ba ya mike ya fita.

Shigowa yayi hannunsa dauke da tray na saki tagumin da nayi ina kallansa da mamaki, bai ce min komai ba har ya ajiye a gefen gado inda nake shima ya zauna yana tsiyaya dafaffiyar madara a cikin glass cup. Bakinsa ya kai ya dan Sha sannan ya miko min na kawar da kai gefe.

“Idan baki shaba yau bake babu bacci.”

“Na koshi ne nasha lemo tun a daki na.”

“Wancan ya zazzage ki kara da wannan please.”

Babu yadda zanyi dole na juya ya kafa min a baki na Sha, shima ya Sha ta inda lips dina suke tabawa. A haka har muka shanye tas ya ajiye cup d'in tare da sauke tray d'in kasa.

“Ko Zaki ciro min jallabiya ta?”

Da sauri nace.

“Wacce?”

“Ta jikin ki mana ai aro daman na baki kiyi sallah.”

Ido waje na kalle cikin mamaki ban san ma lokacin da nace.

“Sai na zauna tsirara?”

Ya yi murmushi tare da cewa.

“Is better, dan sai kin fi kyau ma.”

“Kai...”

Na fada cikin tsantsar mamaki, ganin yana dariya ne yasa ni juyawa na kwanta Ina daga gefen gadon kafafuwa na suna kasa. Salman ya rage wutar dakin ta koma light green ya karaso tare da dauka ta ya dora a tsakiyar gadon yana cewa.

“Baby ai sai kiyi ciyon jiki idan na bari kika kwanta a haka bayan kuma ni na roki tayin kwanan nan.”

Ban kula shi ba ni dai saboda bacci nake ji duk kuwa da cewa masarautar ta fara cika saboda yan biki. Na lumshe ido na kawai naji ya rungume ni yana magana a hankali.

“Kin san nan dakin tsoro ake bawa mutane, bari na rike ki kar kema kiji tsoro idan muna bacci.”

Yadda yake magana numfashinsa cikin kunne na shine yasa tsigar jiki na tashi, ya dinga yawo da hannunsa ina jinsa amman kasalar da nake ji ta hanani koda motsi Sai ma jin dadin abin da yake min nake.

Daga nan kidan ya zanza salo saboda jin bakinsa a wani sashe na daban, yanayin da ya sanya ni suman da ni kaina ban san lokacin da nai bacci ba. Sai bude ido nai na ga Salman yana ta kallo na. Da sauri na yunkura zan tashi naji kasa na ya amsa da wani irin azababban zafi da rad'ad'i tare da wani irin zugi mai zafin gaske da ya sa na saki kara mai karfi na koma da baya na kwanta Ina.......
Chapter 88 · 0% Book details