← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 114

Sashe 9

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuwa likafar talle na taci gaba, Kaf karkarar mu ba inda bana zagawa don asai kayana. Idan naga zai yi kwantai ma har fada nake janyowa ta yadda dole mutum ya siya asarar sa.. Ho ni Dije- Dijengala Yar Baffan ta. Ta Gajiyalle mai yar hakiya.. Dijama mai kayan koli. k’anwar Mudin bakin tasha..”

Kirarin da nakan yiwa kai na kenan aduk sanda nayi ciniki. Gajiyalle kan bani kudin batarwa. Idan kuma banyi kasuwa ba ta lakadamin duka ni kuwa na rama akan dabbobin ta na targada shegu...

..
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
*KIBIYAR AJALI.....!!!!*
_(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)_
🏹👑👩‍❤️‍👨💝

*MALLAKAR:- NANA HAFSAT*

*(MISS XOXO)*

*©️®️ZAFAFA 5 2021*

*BABI NA 5*
(LAST FREE PAGE: SHAFIN KARSHE NA KYAUTA)

••. ••. ••

Sana'ar da Gajiyalle take dora min ta karbe ni sosai ina jin dad'in yin ta fiye da komai a rayuwa ta, har wasu kauyukan nake bin masu talla muje, gashi abin burgewa duk abin da na daga sai an siya. Babu laifi duk sanda na kai kudi cas ina samun abincin da zanci na koshi, sabanin idan na kashe wasu ranar sai naci duka kuma duk da haka sai na takura mata ta dora min na fita da kayan na siyar. Bangaran Baffa kuwa ya rasa yadda zai yi dani da Gajiyalle akan na shiga makaranta amman muka kafe, gashi mai garin ya sanya idanuwa sosai, dan mutane sun fara saduda suna ta barin yaran su na zuwa.

Wata rana na dawo daga talla na tarar da Baffa zaune a kofar gida ya zabga tagumi, nayi saurin karasawa kusa da shi tare da aje farantin kayan kolin nawa, hannu nasa na zare tagumin nasa tare da ciro cinikin ina karkada masa shi baki na a washe kamar mai tallar makilin. Yaki kallon kudin na kuma kaiwa kusa da fuskar sa amman duk da haka yaki kallansu, hakan ya tabbatar min da cewa ransa a bace yake.

“Baffa wai baka ga cinikin da nayo ba? Sai nuna maka nake yi kaki kallo na.”

Cikin sanyin muryarsa yace dani.

“Tashi ki shiga ciki tun kafin ta jiyo muryarki tazo ku tara min mutane.”

“Amma dai Baffa an bata maka rai ko?”

Yayi shiru.

“Haba Baffa ko ni nayi maka laifin ne?”

Abin mamaki sai naga ya yi saurin daga kai alamar 'eh' ni ce.

“Na higa uku ni Dije me nayi maka Baffa? Koma dai meye ni nasan ban kula ba nayi maka shi dan Allah ka yafe min kaji Baffa na?”

Baffa ya ja numfashi tare da kallo na karo na biyu tun zama na kusa dashi, yana shirin yi min magana muka ji muryar Gajiyalle a kan mu tazo ta rike kogu tana karkada jiki da alama masifa take ji da ita. Hannu ta miko min alamun na bata nayi dariya saboda nasan su ta biyo saman, ai idan har kasan Gajiyalle to idan ta yi maka wannan tsayuwar indai baka bata abin da take so ba, babu shakka ka taro babban aiki. Na dora mata kudin ta hau lissafawa, ta gama sai kuma ta saki guda tana raye-raye.

“Ahaiyeeee nanayeeee cas! Tabbas Dije kina da goshi ke din mai sa'a ce walle, nayi miki alkawarin samira mai uku aradu lokacin bikin ki, ke harda kumbo da kwalla tasa da fanteka heeee ras!... Dije ta Gajiyalle mai kayan koli.”

Tana gamawa ta juya tare da komawa gida tana lissafa kudin ta cike da farin ciki. Ni kuma na sake mikewa zan tashi Baffa ya yi saurin dakatar dani yana cewa.

“Ummina ki zauna magana zamu yi.”

“Allah yasa dangin inna ta zaka kai ni Baffa.”

Ya yi murmushi yasan ina son zuwa amman baya so ya kai ni su rike ni gabaki d'aya dan dama duk haushin Gajiyalle suke yi dan suna jin labarin yadda take gana min azaba.

“Ummina ke nan, zan kai ki dangin innarki amman da sharadi guda daya.”

Cikin zumudi nace.

“Fadi Baffa ko meye zan yi indai zaka kai ni.”

“Yauwa Ummina, sharadin shine ki yadda ki fara zuwa makarantar can, kinga ko dazu sai da mai unguwa ya yi min maganar cewa mai gari yana sanya ido akan duk wadanda suka kai yaran su. Kinga yana ganin mutunci na dan Allah ki yadda ki fara zuwa.”

Tunda ya fara magana nake yatsina fuska tsanar mai garin ta fara shiga zuciya ta, yana kaiwa karshe kuwa na cona baki gaba ina cewa.

“Rabu da mai garin nan Baffa, yo hi makarantar ya yi da zai ihi mutane akan zuwa? Ni wallahi aradun Allah ban zuwa, nama fasa zama irin na radiyo d'in da na talabijin d'in tunda sune suke sake janyowa kace sai naje.”

“Ikon Allah! Ummina ni ba haka nake nufi ba, kinga wan....”

Nayi saurin mikewa.

“Baffa ni fa bazan yi bokon nan ba, kaima fa baka yi ba kuma kaga nan da rai da lafiyarka, ni wallahi bana son makarantar can.”

Na shige gida ina buga kafa alamar bana so ban yarda ba. Haka Baffa ya rabu dani, ya zamana suna yar buya shi da mai gari dan besan wace karyar zai yi ba dan ya kare kansa a wajan shi. Ni kuwa naci gaba da yiwa Gajiyalle talla yanzu har wani mutunci muke yi da ita zamu yi jira harda shewa mu tafa da hannaye cikin nishad'i.

Mudikalle ma babu ruwan shi da makarantar, dan a lokacin da Baffa ya bashi fom dinsa a gurin ya daga sama ya yi mata gutsin-gutsin tare da watsar da su iska ta tarwatsa. Kuka ne kadai Baffa be yi ba, hakan ne kuma ya hana shi bani tawa dan yasan nima zan iya yin yadda Mudi ya yi.

Ranar Litinin da safe naje siyo koko da kosai ina shayo kwanar da zata kai ni wajan makaranta na taci karo da wannan malamin da ya tsinko bulala zai doke ni, amman nayi kamar ban gane shi ba naje zan wuce kawai naji ya tsaidani.

“Zo nan yar tallah.”

Haushi ya kamani da naji irin sunan da ya kira ni dashi, na riko kuguna tare da cewa.

“Ba suna na bane, idan zaka kira ni ka ce Dije ko tagala ko yar gatan Baffa da Gajiyalle.”

“Bazan kiraki da su din ba, yar tallah zan fada ko zaki doke ni?”

Nasa yatsa a baki ina ciza naga alamar mutumin nan bashi da mutunci kuma babu abinda ya hada ni dashi bare nace ga dalilin da yasa yake takura min.

“Toh ai hi kenan sai kai ta fada ba sai na amsa maka ba sannan zaka ji dadin kuma gaya min ba.”

Ban ankara ba naji ya dauke min keyata da duka, nayi saurin dafe gurin ina furta.

“Kut! Kai... Kai... Kai! Allah ya...” Ban karasa ba ya kuma sakar min wani wanda yafi na farkon.

“Ni zaki zaga dan ubanki? Ke baki da mutunci ko? Toh na rantse da Allah zan yi maganinki a cikin kauyan nan naku. Daman tunda na ganki nasan baki da tarbiya, zo ki wuce ki shiga ajin nan daga yau zan koya miki tarbiya farar aljana da idanuwanki kamar na mage ta ga bera.”

“Ajin me zan shiga?” Nayi furucin ba tare da na san ya fito ba.

“Ya za ai kisan aji kina yar tallah? Yau dai nake son ki shiga kisan ko menene shi.”

“Lallai ma, indai makaranta ce bazan higa ba ana dole ne? Toh na gaya maka Baffa ma ya yi ya gama bare kai da ba uba na ba ma.”

Ina gama fadar haka na faki idanunsa nace kafa mai naci ban baki ba, na ruga da gudu kamar ance ya biyo ni. Malam Auwal ya bini da kallon sakarya ni kuma har da yi masa gwalo, na shiga gida ina dariyar mugunta. Gajiyalle ta karbi koko da kosan ta sammin nasha daga nan nayi tafiya ta talla. Haka dai rayuwa ta taci gaba da kasan cewa na kasa tsayawa na karbi shawarar da Baffa yake bani.

Sai da yaga da gaske nake bazan yi bokon ba sannan ya dako fom di na ya bani yace duk abinda naga dama naje nayi, ganin ransa ya yi mugun baci ya fita a harkata duk wasu abubuwa ya dena yi min sannan ne na fara tunanin yadda zan yi na samar masa da farin ciki ko Allah zai sa ya dawo da jin dadin sa gare ni.

Kwana biyu na dena yin talla, tun Gajiyalle na daukar abin wasa har dai taga na dage nace ni Baffa zan farantawa rai, boko zan shiga ko da ba'a so nayi zan yi ko zan mutu a ciki. Tun daga lokacin ta dawo da bani azaba wacce tafi ta baya, amman nima na kafe cewar bazan yi talla ba sai dai ta kashe ni.

*GOVERNMENT GIRLS JUNIOR PRIMARY/SENIOR SCHOOL DURBUN*
Chapter 9 · 0% Book details