Sashe 101
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwance nake akan gado, Hawowata kenan daga kasa, Domin Ammi tace na dena zuryar zuwa sashen ta tunda yanzun bani kadai bace. Ajiyar zuciya na sauke fuskata na kumshe da murmushi, Kaunar da Salman da Ammi kemun yanzu ta kara nunkuwa, Wata irin tarairaya nake samu daga kowannen su. Gwaggo ta fada ma kullum cikin aikomin da tofi take, Addah Maryama ma kullum cikin zuwa ta duba ni take. Lamarin sai godiya ga Allah daya had’ani da miji nagari mai kaunata, Suruka ta gari da kuma yan uwan miji masu gatanta ni.
Yanzu babu abunda na nema na rasa a duniya sai rashin iyaye, Wanda su Kawu daddy su Ammi suna iyakar ko’karin su wajen maye gurbin su. Sai dai iyaye daban ne a duniya, Ni yanzu da za’a kwace komai nawa a dawomin dasu sai nafi farin ciki.
Kwakwar manja ta dake gefe na janyo na shiga ci hankali kwance ina lashe yatsu na. Cikin haka sai ga Salman ya shigo sanye cikin jallabiya hannun sa rik’e da flask din shayi da kofi da cokali. Tinda ya taho nake bin hannun sa da kallo domin ni yanzu banda bacci da ciye ciye ba abinda nake.
“Zawjatii.. Maman unborn. “
Zama yai a gefe na yana kallo na cike da tattali.
“Na’am Zawj.. Tea ne ko kunu?”
Daria ya kyalkyale da ita yana shafa gefen fuskata,
“Kunu ne... Ammi ta bayar akawo miki. Kunun gyada.”
Yunkurawa nai, Zan mike yai hanzarin tare ni.
“Yi hak’uri tawan. Idan kika tashe shi yana bacci fa? Ki dinga yi ahankali.”
Na kalli shamilallen cikin nawa ina dariya.
“O ni ‘yasu... Toh nide nide nide yunwa nake ji ai.”
Na fada ina turo baki gaba cike da shagwaba.
Zubamun kunun yai a kofi ya jinginar dani a k’irjin sa yana kafamun cup din akan baki na,
“Ungo asha lapia.”
Gani nai zai batamin lokaci na karb’e kofin na kafa kai na shanye, Sai danasha sau uku sannan naji ya isheni. Na wanko baki na. Na dawo kusa dashi na zauna.
“Allah sarki Ammi naa..”
“Ni Fa? Ni ba naki bane?”
Hannuwana biyu nasa tafukan na rufe fuskata. Kunya ta kamani.
“Ammin ce akwai kirki, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, Allah ya juyo da hankalin Yareemah Ibrahim agare ku ya waiwayo gida shima.”
“Aaamin Yaa Rabbi...”
Ahankali ya sumbaci tafin hannu na yana sake rike ni sosai tamkar Za’a kwace ni. Cikin rada ya shiga cemun,
“Na fad’a miki wani abun farin ciki...?”
Da sauri na gyad’a kai na ina kallon kwayar cikin idanun sa. Wadda nake samun nutsuwa sosai a duk sanda na kalle ta.
“Khal... Wato Yareemah Ibrahim ya farfad’o daga sihirin kafewar da akai masa a korea. And Alhamdulillah hankalin sa ya dawo jikin sa. Zancen da nake miki ma ya kusa shigowa kasar nan ...”
Bansan sanda wasu zafafan hawaye suka shiga reto a fuska taba..
“Nooo....! Kuka? Subhanallah! Mena miki Zawjati? Na fa’di wani abun daya tayar miki da hankali?”
Ahankali na girgiza kai na, Nasa hannu na na riko nasa ina murmushi,
“Kukan farin ciki ne Zawj.. Kukan dadi ne kawai. Shin Ammi tanada masaniya kuwa?”
“Ah’ah tukunna dai... Akwai lokacin da muka gama tsara komai, Kinsan dawowar Khal masarautar nan akwai ruguntsumi fa. Saboda love kina ji?”
Gyada kai nayi alamun ina sauraron sa. Cikin nutsuwa ya cigaba da cewa,
“Saboda sun dauka har yanzu bansan matsayin Khal ba awaje na, Sun dauka har yanzu Khal na can yadda suka kafe shi, Kuma sun dauka har yanzu Ammi na cikin kangin rayuwa na rashin mu a kusa da ita... Kuma sun dauka dagaske bana haihuwa...”
Na dago da sauri ina kallon sa. Ya gyada kai cikin tabbatarwa.
“Ke haske ce acikin rayuwata Zawjatii, Na gaya miki kece mahadin rayuwar Salman ibn Aliy. Dake Allah yayi zamu samu KIBIYAR hallaka makiyan mu na masarautar nan. Domin kedin dashen Allah ce...”
“Yanzu idan suka nemi kashe ni fa..?”
“Karki damu da yardar Allah babu abunda zai faru dake da abun dake cikin cikin ki, Domin mun dogara da Allah shi din mubuwayi ne gagara misali.. Sai abu na biyu Dr. Fiddau zata dinga zuwa kullum tana duba lapiar jikin ki.. Sannan Za’a kawo amintattun hadimai da zasu dinga kula dake, Motsin ki, Baccin ki, shawagi, Abinci, anything dai daya dangance ki zasu tsaya akan ki. Kada ki manta kina da ni kuma ga Ammi... Ai zawjati ke yargata ce gaba da baya...”
Nayi murmushin da hakorana suka bayyana, Duk kuwa da kasan zucia ta a dankare yake da fargaba sosai. Na gudun kar a hallaka ni da abinda ke tare da ni, Hannu nasa akan marata ina shafa wajen ahankali. Wani irin sanyi naji yana ratsa ni. Cike da karfin gwiwa nace,
“Allah ya temake mu... Allah ya kara kare mu da kariyar sa. Mugun ji mugun gani Allah ya kiyaye..”
“Aamin Zawjati.. Allah ya miki albarka, Ya kara miki so na a zuciar ki, Tunda nide duk minti sonki nunkuwa yake acikin zucia ta. Ke kuwa har yau baki gayaman wasu kalamai da zan tabbata kin mallakamun zuciar ki ba. Inaga sai na kara zage damtse sosai na yak’i ragowar burbushin kaunar m...”
Ban bari ya karasa ba nai saurin hade bakunan mu waje d’aya, Ni kaina nayi mamakin hakan da nayi, Amma na tabbata hakan shine ka’dai zai iya bashi amsar tambayar sa. Sai da na tabbatar ya gamsu sannan na zare baki na ahankali. Ido cikin ido na kalle shi,
“Waya gaya maka bana kaunar...? Ka cire dik wani waswasi dake tasiri azuciar ka, Ni Khadija daga rana irin ta yau.. Na mallaka maka zucia ta da gangar jiki na sai yadda kayi dasu. Ina kaunar ka, Kauna marar gauraye. Tun ina durbun lokacin Ina cikin SIRADIN RAYUWA, Nayi ta addua Allah ya bani miji nagari wanda zai so ni ya kaunace ni, Na maka ta larabci MIN QALBi na nake kaunar ka tsakani da Allah, Da ace dan adam yasan ABINDA KE CIKIN ZUCIYA to da tabbas zaka son matsayin ka awajena ya wuce ‘kima. Kada ka damu da masu mana SARAN BOYE zawj.. Domin Insha Allah ni Khadija dashen Allah ce, Na tsallake tarko kala kala na rayuwa, Saboda haka da yardar Allah sai na zamowa makiyanmu KIBIYAR AJALI.. Kai de ka zuba idanu...”
Lumshe idanu Salman yai ya bude su akaina yana wani irin tsadadden murmushi,
“Na yadda my love... Na kuma tabbatar kafin wata dayan dana kiyasta tacika a game dinmu dake, To tabbas kaunar zata ninku fiye data yau...”
Murmushi nai nima na shagala da kallon kyakkyawar fuskarsa,
“Tabbas kuwa Zawj.. Insha Allah lokacin nasan kagama dani, Na gama dilmiyewa acikin kogin kaunar ka.. Kalli tin yanzu ma bare nan gaba.. koya kace?”
“Lalle na cancanci kyauta daga wajen gimbiya..”
“Tabbas kuwa ka cancanta.. Amma hak’uri zakayi kata shi ka shirya zuwa zaman fada..”
Hannuna ya kaiwa sumba me matukar ratsa jiki da bargo, Ya sake narkemun ajiki yana wasa da jelar gashi na,
“Ai gaba d’aya gimbiya kin maida Salman tamkar ba sarki ba, Ni fa gaba d’aya mantawa ma nake da wata sarauta idan har ina gaban ki. Barin ace yadda muke dinnan jikin ki na gogar nawa, Gashin ki mai matukar k’amshi yana busa kamshi,...Zawjatii! My unending love for you is my vision, my hope, my goal, and my soul. Ina kaunar ki sosai Zawjatii na. Please ki bari naji dumin jikin ki, Dan kadan zamu yi fa. “
Ya karashe maganar yana kokarin dage rigata, Daria nayi kawai na kamo hannun sa na sunbata a hankali,
“Zawj....”
“Zawjatii..!”
“Kayi hak’uri.. Ka tashi ka tafi dan Allah.. Kaji?”
“Zan sa waziri fa ya zauna, Zance banda lapia, Yanzu zansa ayimun iso dashi.”
“A’ah..! Ka tashi ka tafi.”
“Yanzu haka zan tafi ba abun da zan samu?”
Mikewa nai na riko hannun sa ya tashi tsaye shima,
“Muje na shirya ka katafi kaji..?”
Gyad’a kai yayi, Hannu cikin hannu muka koma dakin sa. Na shiga fito masa da duk abubuwan da zai saka. Na temaka masa ya kara yo wanka, Na shiga shirya shi ina masa kirari,
“Kaga dawisu sarkin ado nawan, Da kwalliyar ka ala hallice ka Zawj, Taka a hankali lu’u lu’u abun son kowacce mace! Amma fa sai dai suyi hak’uri domin wannan lu’u lu’un nawa ne ni kadai.. Ko shaheedah sai ta kama kanta.”
Murmushi naga yayi ya sake tallabo ni yana kissing kan hanci na. Na sunkuya ahankali ina faffesa masa turare ajikin kayan sa,
“Kaga katangar zinare majingin mace, An gayshe da sarkin sarakuna, Mai basannabas, Tsarin jikin ka da hankalin ka na shugaba mai shugabantar masu rauni. Takawar ka daidai ranka ya dade mai dogon zamani, Sun buga sun barka ya zasuyi dakai? Girman kane Allah ya baka, Ya zasuyi?.. Waya isa ya amsa balle har ya amshe? Kai ka iya kai zakayi ranka ya dade.. Kai ne gaba muna biye. Nawaje na.. Allah ya dawomin da kai lapia..”Cc:OD
Na k’arashe ina zura masa glasses dinsa cikin idanun sa, Lalle Salman anyi kyakkyawan sarki mai kyakkyawar halayya. Gaba salamun baya salamun. Wata iriyar runguma yayi mun, Ya saqalo hannuwan sa muna kallon kanmu tacikin mudubi ya d’aura kansa akan kafada ta. Nasa hannu d’aya ina shafa kwantaccen sajen sa...
“Zawjatii na... Na biya ki da kai na, Ruhi na da Qalbi na. Na biya ki da amanata da dik wani sirrina, kece kofar mabudin alkhairi na, Kuma kece katangar mahallakar makiyana. Hakika ke kika cika Salman ibn Aliy ya zama cikakken sarki mai cikakken Iko....”
Nai saurin riko hannunsa Na juya muna fuskantar juna,
“Kalaman ka sunyi tsau.....”
“Karki karasa rabin rai na.... Nan gaba kadan zaki tabbatar da hakan. Amma kafin sannan dole na baki ladan kirarin nan.”
Daukata yayi a hannu ya kaini dakin da nake dazu ya kwantar da ni, Ya janyo bargo ya lullube kafafuwana. Ya zauna a gefe hannun sa cikin nawa,
“Zawjatii naa.. Ina kaunar ki sosai. Zantafi fada sai na dawo, Amana addua”
Ya karasa yana rungumeni kamar Wadda Za’a dauke a gudu, Cikin muryar lallashi ina shafa gadon bayan sa nace,
“Allah ya kare mun kai, Ya dawo mun da kai lapia. Allah ya dora ka akan makiyan ka, Ya Kara maka madaukakiyar kasaita da kwarjini da nasara akan kowane lamuran ka.”