Sashe 79
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba dayan su su ukun suna hakimce a kujeru, Gimbiya Huwaila ta kishingid’e a doguwar kujera mai cin mutum uku, Najwa kuma ta yi wani zama itama na sarauta ta dora kafafunta akan tum-tum. Jaleelah kuma tana hakimce itama akan kujera ana mata kitso, Mai kitson na tsaye a haka take mata..
Hannu tasa tana tattaba kitson,
“Meye hakan? Sam bai kamu ba, Kalli wannan yayi gefe da yawa. Kunce duka nan bangaren ki sake wasu..”
Takarasa tana jan tsaki.. Jikin me kitson sai ‘bari yake yi.. Haka ta shiga kunce shi tana sake wani.
“Ni kuwa akwai cigaba a turaren da muka yayyafa a sashen Salman na kwanaki dinnan? Sam banji ance ya kwanta ciwo ba.”
Gimbiya Huwaila ta tambaya tana mai cigaba da danna wayar dake hannun ta..
“Gaskia dai kwanakin nan inata tunanin abun.. Ni fa har jakadiya na bigi ciki ta nuna ba abunda ya faru dashi. Kenan malamin nan ninke mu yai kome?”
Najwa ta bawa Huwaila amsa.
“Anya kuwa..? Domin aikin na kan dutse akwai ci, Sai dai idan shaheeda ce ta batamana shirin..”
Cewar Jaleelah..
Gimbiya Huwaila taja dogon tsaki kafin tace,
“Ko d’aya makirar ba... Ummiyo (Hadimarta) Tacemin sau uku tana cin karo da Ita Zata shiga sashen sa’adatuh.. Y’ar wahala.”
“Y’ar wahalar gaske.. Ai kinji da aka turawa Salman list din kayan bikin su Munaya bece komai ba, Wambai yace a wajen yace ayi transferring kudin.”
“Yo me zece Jaleelah? Ai sullutu daban yake. Kadan ma yagani.. Ni yanzu jira nake kawai asa yayi murabus, Abdulqadeer ya hau karagar mulki.. Koya kukace?” Cewar Huwaila.
“Kibari kawai... Ai ranar da sai na zuba ruwa a kasa na sha.. Allah de ya kaimu, Kuma yakamata mu sake komawa kauyen nan. Domin naga alamun yarinyar nan da ya auro tsageriya ce, Duba fa kiga aikin sa akai akanta amma tamkar ba’ayi, Sai wani daga kai take..” Najwa ta k’arasa fada tana karkada kafadu..
“Rabu da ita... Yadda tazo haka zata tafi.. Bara na koma sashe na.. Zanga likita saboda kai ya matsamin.”
Hajia Huwaila ta k’arasa fada tana gyara zaman laffayar jikin ta..
“Okay Yaya... Allah kara lapia.”
Cewar Jaleelah
“Okay! Sai kin dawo. Allah bada lapia.”
Najwa ta fad’a tana murmushi.
Bayan fucewar Gimbiya Huwaila, Su Najwa suka tasa fefenta a gaba,
“Munafuka... Babu fa inda zata je. Shirin su suke itada abdulqadeer.”
Cewar gimbiya Najwa tafada tana tabe fuska,
“Hmm ki bari kawai Hajjaju.. Ai nasan karya take yi, Yo wannan matar kanta kawai tasani. Danta ya kwaci gado ta fantama ita kadai. Mu zuba mugani.”
Haka suka yita gulmar gimbiya Huwaila, Suna mata zagon k’asa, Bayan ta tafi ba jimawa, Gimbiya Najwa tayiwa Jaleelah sallama itama tatafi.. Tana futa itama Jaleela tafara yi da ita, Ita dai mai kitso sai raba idanu take,
‘Yayan iska.. Wai ku masu ‘yaya maza ko? To ku zuba idanu kugani babu wacce ‘danta zai karbi ragamar mulkin basannabas.....”
*GIMBIYAA KHADIJAA*
Sashen Ammi na nufa bayan na tashi daga bacci, Acan naci abincin safe. Lokaci zuwa lokaci mukan taba hira da ita. Abdullah na gefe yana scrolling sunayen universities da zai zaba. Can ya mike ya haye sama.
Wayar dake gefen aljihun rigata samfarin A line na zaro na rissina na mika mata..
“Ammi... Gashi Inji Salman yace yana gaydaki.. Kuma yana kewar ki sosai, Nan da lokaci kalilan zai zo wajen ki ya gayshe ki. Amma kafin sannan Wai ya canza miki sabon sim zakuyi magana ta ciki.”
Idanuwan Ammi suka kawo ruwa, Hannunta na rawa ta karba tana jujjuya wayar, Da alamun ta tuno wayar da kuma abunda yafaru ranar.
“Yace bayason asan komai ya daidaita yanzu sai nan gaba zai bayyana komai idan ya gama binciken da yake.”
Sam Ammi batai magana ba sakamakon hawayen da take faman zubarwa, daga karshe ya zama kuka Sosa wanda ya saukar mata da mura. Mun jima a haka tana kukan farin ciki kafin tace dani,
“Nagode Khadija.. Mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Tabbas samun ki a sirika alkhairi ne, kin zamar mana wani haske na warwarar matsalolin mu. Allah ya biyaki da gidan aljanna Khadijaa. Nagode Nagode Nagode.“ Ahankali nace
“Aamin..”
Ban wani jima ba na mike na mata sallama Zan tafi, Har na kai bakin kofa tace mun,
“Amma fa se kina dan takura masa akan abinci... Baya son cin abinci shi yasa ulcer tai masa mugun kamu...”
“Insha Allah Ammi zan dinga yi.”
Na sake mata sallama sannan na fice na koma sashe na ina kambama dattako irin nata. Allah sarki uwa da ‘da.. No wonder bana ganin yanacin abinci ko an kai masa, Ko yaushe yana fama da ciwon ciki.. Girgiza kai nayi na koma cikin sashe na. Kan gado na haye kawai, Sallah ce ke tadani na kuma sake kwanciya.
Banda juyi babu abinda nake yi akan gadon, Gaba d’aya tunanin dazu da asubah na shiga yi, Na sauke ajiyar zuciya, Can na rufe idanu na na kara lulawa duniyar tunani a haka bacci yai awun gaba dani.. Nide Ranar haka nayi bacci rabi da rabi, Da safe na shiga sashen Salman nan sarkin dogarai yake cemun sarki baya nan yayi tafiyar gaggawa tun jia da yamma, Banma sani ba.
*WASHE—GARI*
A hankali na bude idanuna, kawai naga mutum a tsaye ya kura min ido ko kiftawa bayayi.
Nai saurin tashi zaune Ina kara bude ido, Sanye yake cikin jallabiya ruwan zuma, tayi masa masifar kyau. Bai ce min komai ba sai guri da ya samu ya zaune a gefen gado yana kuma bina da kallo ta cikin glasses din fuskarsa.
“Good morning... Bar..barka da dawowa.”
Yaki amsawa sai cewa yai dani.
“Any news?”
Kamar ban fahimci abinda yake nufi ba, na sosa cikin idona Ina cewa.
“Na me fa?”
Ya juya yana kallon kan bedside drawer din dake kusa dashi, yasa hannu ya dauki jotter da biron da ya gani akai. Cikin sauri na yunkara zan kwace yasa daya hannun nasa tare da kamoni yana min kallon kurullah, na gane hakan ne ganin yadda ya janyo fuskata kusa da tashi.
“Ni ka bani abu na.”
“Baki aikin da na baki bako?”
Yayi maganar yana kokarin bude jotter din, still kuma yaki sakar min jiki na. Haushi ya sake kamani da sauri na fincike dan naga alamar idan bana yi da gaske zai Iya cin galaba a kaina, bayan kuma babu soyayyarsa ko kwayar zarra a cikin zuciya ta. Ina yi masa abubuwa ne kawai saboda alkawarin Gwaggo ta Fada dana karba na bada gudin mawa wajan ceto rayuwar su ba dan nafi kowa ba sai dai sunan da nake takawa a gareshi shine zai ba da damar isar da wani tallafin gare shi.
A hankali ya dinga bin bayanan da na dinga dauka kadan kadan na fara bincike akai, hakan ne ya shagalar dashi be sake bi ta kaina ba. Na zabga masa harara cikin zafin zuciya na tashi na nufi bathroom ina jin takaicin ganin yadda baya damuwa da tawa matsalar sai tashi. Ina shiga nasa key dan kar ma ina wanka ya biyo ni, nai kwanciya ta a cikin bathtub saboda na dad'e nasan idan ya gaji da jira na dole ya tashi ya tafi. Shi kuwa Salman yana zaune yana duba jotter din amman ya kasa gane abin da take nufi, sai ta fara tubutu tiyan-tiryan sai yaga ta goce ta rubuta wasu arbitration yadda ita kadai zata gane abin ta. Jin shiru bata fito ba gashi lokaci yana ta tafiya kuma zai je fada yasa shi tashi bayan ya bar mata dan note.
Sai da na tabbatar ya fita sannan nai wanka nayo alwala na fito, ina goge jikina da towel na hango pepper din akan gado na dauka tare da karantawa.
“Anjima ina nemanki 9:00pm.”
Tab'e baki nayi tare da yaga takardar na dauke jotter din naje na boye sannan na fara shirya kai na. Ina gamawa na sakko kasa na nufi kitchen inda ma'aikata na suke ta faman aiki cikin tsari da nutsuwa, duk suka gaishe ni na amsa musu cike da fara'a sannan duk suka fita, daman yawanci haka suke yi duk lokacin da na shigo kitchen din sai su koma waje saboda na fi son na samawa kai na abinda zanci saboda tsaro ba dan tsoro ba. Dan waken flour nayi sai green tea dana dafa ina gamawa na zuba nayo parlour hankali na kwance. Sai da na gama ci sannan na tashi na sake komawa bedroom na kuma yin nazarin da nake yi, daga karshe kuma na fito dan zuwa sashen Ammi.
Ina baro gate dina na hadu da su Wambai suna tafiya bayin su na take musu baya, nai kamar ban gansu ba saboda tun lokacin da naga sun shiga gurin su Gimbiya Najwah tare da basu wasu layoyi na tsane su, shakku ya shiga tsakani na dasu. Ina gaf da wucewa naji suna miko min gaisuwa wacce nasan ta munafinci ce, basa gashe dani sai sunga idanun jama'a da yawa saboda sun tsane ni.
“Ranki ya dade za a dan zaga masarauta ne?”
Sai na samu kai na da jin izza lokaci guda, hakan kuma ya bani damar buga musu tambayar da ta kusa dabar-barta su.
“Eh zan dan zagaya. Ku kunje gano iyali, ya aka baro su?”
“Wa? Mu wai ranki ya dad'e? A a wallahi can wajan sarkin dawakai mukaje mun tarar dokuna biyu sun mutu.”
“Ayya Allah ya tsare gaba, mai martaba ya sani kuwa?”
Na tambaya cikin son Jin karin bayani dan Ina da yakinin ba zasu sanar mai ba idan ban sako musu zancen ba.
“Ah'ah'ah ai yanzu abin ya auku muka je, idan ya fito fada zamu sanar dashi.”
“Allah ya taimaka ya kara lafiya Baba Wambai da Baba Chiroma ko?” Nai alamar tambaya Dan na sake tabbatar da su waye.
“A'a Wambai ne da Galadima ba Chiroma bane.”
Cewar Wambai yana ta faman murmushin yake, mukai sallama suka wuce nima na tafi wajan Ammie. Su kuma suna yin nisa Galadima ya saki tsaki tare da gyara rawaninsa yace da Wambai.