← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 114

Sashe 67

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

PG: 8&9
BOOK 2.

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

____*Sai* da ya shiga ya zauna sannan dogaran sa suke rufe shi sauran yan zaman fada suka fara shiga, Kowanne sai an masa kirari, Tukun sannan ya zube ya kwashi gaisuwa wajen Sarki..

Shi dai Salman yana zaune ne kawai, Gangar jikin sace anan, Amman gaba d’aya zuciar sa na ga tunanin acting din Khadija..

“Unbelievable...”

Ya furta batare da yasan ya fada ba.

“Allah ya k’arawa sarki lapia, Magana kayi..?”

Shiru yai ya cigabada sauraran bayanin shamaki. Gaba d’aya zaman fadar ranar cikin walwala yayi ta, Tacikin rawani yake murmusawa a duk lokacin da ya tuno kalaman Khadijaa...

Bayan an tashi daga fada manyan yan majalisar sarki suka nemi ganin sarki, Ya basu dama bayan ya tashi daga inda yake ya koma parlorn sirri. Daga shi sai waziri daya musu iso..

Har cikin babban parlorn sirrin sa dake cikin fadar sa suka shiga bayan an musu iso, Salman na daga kishingide kansa a sama. Da alamun har yanzu ya lula duniyar tunanin Khadijaa.

“Ranka ya dad’e, Allah ya kara wa sarki lapia, Ga su wambai, Galadima da Chiroma za'a yi magana da kai..” Cewar Waziri.

Salmaan na daga kishingid’e ya mike zaune yana gyara zaman glasses d'in fuskar sa.

“Gurin ka muka zo... Tunanin me kake yi haka? ba haifa kayi ba balle ace hayaniyar yara ce ke chake maka kai...” wambai ya fada yana daria.

“Kaji wambai da wata magana, Mutumin da bai da kwan halittar haihuwa? Ta ina zai same su.” Galadima ya bashi amsa yana murmushi shima.

“Me ake cewa namijin da baya haihuwa ne? Mace dai juya ake cewa ko? Namiji kuma sai dai ace masa baho.” Cewar chiroma dake gefe.

Suka sheke da da dariya baki d’aya, Banda Salmaan da waziri, Waziri ya hade rai tamau yana muzurai, Cikin tsananin bacin rai ya dube su.

“Menene haka ne dan Allah? Wannan wane irin wulakanci ne da tsawagaran shirme? Ya zaku zo kan sarkin mu kuna wasu maganganu..? Da nasan shirme zaku zo kuyi da bazan yi muku iso bama.”

“Yo waziri banda abunka ai shigowa sashen sarki ko an mana iso ko ba’ai ba dole mu shigo.. Su waye suka dora sarkin akan kujera idan bamu ba? Karka kauce hanya yanzu ba sai anjima ba sai mu nemo sauran yan majalisa a sauya ka da wani.. Daman kai shisshiginka ya yi yawa a gurin yaron nan” Cewar galadima, Yana magana ne cikin izza.

Waziri yai shiru ransa a mugun bace, sai dai bai kara cewa komai ba, Salman dai yana zaune yayi shiru kawai yana sauraron sa.

“To kai Salman wajen ka muka zo, Kuma gaskia magana ba zata yiwu agaban waziri ba, dan besan ma maganar da muka zo yi ba..”

“Saboda me ba za’ayi agaba na ba dan ban san abin da zaku tattauna ba? Ban isa bane ko ban kai ba?..” Waziri ya tambayi chiroma cikin tsantsar mamaki.

“Baka isan ba..Kuma baka kai din ba, Saboda haka ka tashi ka bamu waje, kai ma bama shigowa idan kuna tare.”

“Babu inda zanje, Ku baku isa ku bani umarni ba wallahi.. Nan wajen gaba d’aya maganar mutum d’aya zanji kawai, wato Sarki Salman! Bayan shi babu mahalukin daya isa. Na taba hana ku shigowa idan muna tare dashi? Me zai sanya ni kebewa dashi kamar wani marar gaskiya?”

Su Galadima suka harzuka suka fara magana sama-sama, Sarki Salman ya cije leben sa na kasa yana d’aga musu hannu a hankali.

“Enough please! Waziri zaka iya tafiya, Kayi hak’uri.” Waziri ya zube a kasa yana d’aga hannuwa,

“Tuba nake ranka ya dad’e.. Amman me suke nufi da ina kebewa da kai? Kenan zargi na suke yi da yin wani abun? Wallahi ba zan cutar da kai ba ranka ya dade, kai amana ce a guri na, a rai na ma banji zan iya cutar da kai ba bare har na aikata. Amman Allah ya kara maka lafiya da kwarjini, Zan fita yanzu. A huta lapia.”

Ficewa yai bayan ya zabgawa su Galadima harara don yana da yakikin zuwa sukai su yi masa wani abun na tilas. Wani dogon tarihi suka fara dakkowa Salman, Wannan ya saki wani ya kama, Haka suka yi tayi. Duk Salman ya gaji sai lumshe idanu yake a hankali. Wambai ya kar’kare da,

“Yanzu dai abunda mukeso kuma muka yanke shawara, Kamar yadda kaka da kakanni suka yi, Har hakan ya zama al’ada ya zama wajibi akan kowane sarki, Kaga kuwa akan ka ba za’a soke ba..” Chiroma ya cigaba daga inda wambai ya tsaya,

“Bayan bula mana kasa da kayi a idanun mu ka auro bare, Wacce ba jinin sarauta ba, Bata cikin rakunun sahun masu mulki ko sarauta, Ka jajibo mana yar talakan talak marar usuli, Wanda kakan ta na goma bana tunanin yayi arziki. Amma saboda tsabar ka rainamu shine har sai za’ai daurin auren ka sanar mana.. Shin yaushe ka fara d’aukar Kan ka kai sarki ne? Nace yaushe.”

Salman dake gefe yai shiru kawai yana kallon gefe, Galadima yaja tsaki yana ture flower vase din dake gefen kujerar da yake, Wanda har sai da hakan ya zamto sanadiyar fashewar ta,

“Ana magana kana shiru ko? Wannan dan iskan halin awajen uwar ka ka samu, Itace duk ta koya muku girman kai, Kuna jin Kan ku, Yo ai barewa batayi gudu danta yai rarrafe ba. Baban ka ma haka ya rakito mana mahaifiyar ka yar dogari, Me yafi wannan kaskanci? To ka bude kunnen ka dakyau kaji, Kodai ka karo auren mata biyu yan cikin dangin sarautar mu, Ko kuma ka sauka daga karagar mulki wanda ya dace ya hau... Ina fatan ka fahimci maganata?”

Salman yai shiru kawai yana binsu da kallo, Sai da Galadima ya sake maimaiatawa tukun sannan da k’yar ya cire idanun sa saqale da glass ya kalle su,

“Yanzu bana jin dadi.. Kuma a gani na tara matan aure a gare ni bashi da wani amfani tunda ba haihuwa nake yi ba, idan har na tara su a haka na zalince su. Shaheedah taji ta gani tace zata zauna dani a haka, wannan ma akwai dalilin auran mu kuma....”

Be karasa ba Galadima ya katse shi da sauri yana cewa.

“Zancen banza kawai, toh yadda wadannan suka yadda zasu zauna da kai ba tare da sun haihu ba. Suma wadanda zaka kara aurowa zasu zauna me ye a ciki?”

“Shikenan Amman zanyi shawara!”

“Shawara da wa? Waziri ko? Hohoho yaro baisan wuta ba sai ya taka.. Lalle daga kai har wazirin kuna gab da yin murabus kuwa.. Kasan an ce sarkin yawa yafi sarkin karfi, Bama wannan ba yanzu ace wancen ginin da kasa aka narka dukiya sama da kasa daman na shegiyar amaryar da kayo ne? Dama bana Wambai bane? Shine gidan sa ke yoyo idan anyi ruwa? Ko abdulqadeer da zaiyo aure kwanan nan.. Tukun nama wa, Wanne munafikin kabawa kwangilar yin ginin? Har akai nisa ba wanda yakeda masaniya sai gab da gamawar sa? Toh zancen komawar matar ka ta biyu babu shi, Sai dai gimbiya Shaheedah ta koma, Ko wambai ko abdulqadeer yai aure ya zauna aciki...”

Chiroma ya karb’i zancen da,

“A zahirin gaskia dai Salman baka kyauta ba, Ya za’ai har ka aiwatar da aiki ba tare da masaniyar mu ba? Shin me ka dauki kanka? Sarki?..”

Wambai ya kece da dariya yana bubbuga hannun kujerar da yake kai,

“Wato kila yanda mutanen gari suke masa kirarin sarki shine yasa yafara jin kansa shi sarki ne ko? Har yake ganin masarautar nan tasa ce ya yanki fili yayi gini.. Dukkanin mu nan tsatson sarautar nanne, Don haka kowanne acikin mu yana da gadon wannan gidan daka gina.. Kowanne yanada ikon zama acikin sa..”

Salman yai shiru kawai yana jujjuya zoben azurfar hannun sa.

“Ku tashi mu tafi, Duk abunda ya biyo baya ka kuka da kan ka..”

Ficewa su kai baki dayan su, Ransu a matuk’ar b’ace, Waziri ya shigo, Kallo d’aya yaiwa Salman yasan yana cikin tashin hankali. Kwantar masa da hankali ya shiga yi, Yana karfafa masa gwiwa. Sai daya tabbatar zuciar Salman ta d’anyi sanyi sannan yai masa sallama ya tafi.. Yana fita Salman ya mike ya shiga bandakin cikin parlorn yayo alwala ya fito, Zai tada sallah wayar sa tafara haske, Shaheedah ce ke kiran sa, Kashe wayar yai gaba d’aya. Ya tada iqama yafara sallar nafilar sa, zuciar sa na kara nutsuwa, Yai sujjada yana mai rokon Allah zabin alkhairi acikin rayuwar sa...

*GIMBIYA KHADIJAA*

Ina koma bangaren Ammi na zube a kujera ina haki, Ni kaina mamakin kai na nake, Lalle nayi kokari sosai, Na kuma ballowa kai na ruwa. Ammi na sama, Hakan ya bani daman kiran Addah Maryamah a waya na sanar mata komai, Ta yabamin hade da sake bani shawarwari, Tace kuma gatanan tafe.

Ba jimawa kuwa tazo, Na rakata saman Ammi, Anan ta sanarwa Ammin kancewar zan koma sabon ginin da akai a sashen sarki Salman, Ba karamin dadi Ammi taji ba. Domin yadda fuskar ta ta kara fadada da murmushin farin ciki zaka gane taji dadin komawar da zanyi can.
Chapter 67 · 0% Book details