Sashe 91
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na shiga girgiza kai alamun A'a kamar zanyi kuka na kuma dora hannu na a kai na da alama ko sunan Salman bana son su furta, kuma ban san dalilin da yasa nake yi musu wannan acting d'in ba, ko kuma dan sun ambaci Shaheedah ne oho min. Kamar hadin baki duk suka fita Ina jiyo dariyar su har wata na cewa.
“Lallai wannan aikin na Shaheedah ya fara aiki.”
Na sauke numfashi da karfi tare da rufe ido Ina sake yiwa Allah godiya. Wato da na nuna musu cewa na sanarwa Salman zasu yi tunanin Muna manne, yanzu da na nuna ko sunan shi bana son ji shine suke tunanin aikin bokayan su sun yi tasiri a gare mu. Oh duniya Ina zaki damu wajan son zuciya da neman duniyar ba ta hanyar Allah ba? Lallai Sai na yi taka tsantsan idan ba haka ba kuma na shiga uku daga ni har ganye na.
...Ni dai gaba d’aya har aka kusa kammala bikin su Munaya dakyar naje event biyu, Shima sai da na gayyato su ya shukrah saboda kar ace ba wani a dangi na da yazo, Dakyar suka yadda suka zo, Amman dai sun fidda ni kunya domin sunyi ado na kece raini. Nima nasha kyau cikin wani dakakken lace da Ammi tabayar aka kawomin a dinke, Lemon green da dark army green. Na nada laffaya itama rantsattsiya ta cikin kayan lefe na. Ba karamin kyau nayi ba. Event biyu naje na walimah/Budan kai. Daganan sai hawan sukuwa da akai da dawakai, Shima dan Abdullah ya haune shysa na leka banjima ba na dawo sashe na, Ko sau d’aya ban hadu da shaheedah ba, Naji dai ana cewa tazo events din da akai na baya. Ita tasani.
Duk wani abu da zai Kara had’ani da Salman a inuwa daya na guje shi, Y’ar wasan buya nake dashi yanzu. Bana taba bari ya rabeni saboda azabar danasha a hannun sa rannan, Har yanzu fama nake da kai na, Na kuma tabbatar wannan wasan ba irin nawa bane na manya na ne. Haka aka kammala bikin aka kai amare gidajen su. Sai fatan Allah yasanya alkhairi.
*****Ina kwance akan kujera na idar da karatu kenan, Na shiga tunanin yadda zan tunkari Salman da zancen barina naje gidan Kawu Daddy, Domin Tunda akai aure na banje ba, Inason na zazzagaya dangi ma inda hali, Amma tayaya zan tambaye shi bayan wasan buya nake dashi? Karar waya tace ta katsemun tunanin da nake,
‘Zawj habibyy..!”
Shine sunan da ya fito akan screen din, Na ware idanu ina sake karantawa. Nide sam bangane wanene ba don ban saving sunan kowa da haka ba. Wata zuciar ta sanarmun da Salman ne ya rubutawa kansa haka. Gaba na na faduwa na dauka ina raba idanuwa tamkar yana gani na..
“Hello......!”
“Assalamu Alaikum... Ya zawjati aleaziza .. kayf halika? ahbuk waftaqadk kathirana.. Deeeja! Kina jina?”
Yadda yake magana ahankali cikin wata irin murya yasa na sauke ajiyar zuciar da ban shirya ba. So yake ta karfi da yaji ya sururuta ni wallahi. Shiru nayi har sai da ya maimata sau uku,
“Barka da rana...”
“Nace miki ina son ki kuma nayi kewar ki sosai.. Babe.. I love and miss you so much. Meyasa kike hana idanuna ganin ki ne? Shin Kinsan yadda kike azabtar dani kuwa...? Zuma naaaaa.”
“Ai ni ba Y’ar iska bace..”
Nayi subul da baka, Ashe ya jiyo. Dariya najiyo yayi mai sauti. Yadda yake wani rage murya yana lankwasa harshe kai ka rantse da Allah da budurwar sa yake magana.
“Naji.. Inde akan ki ne.. Ni dan iska ne number daya. Kina jina? Love! Kefa halaliya ta ce.... Anjima bayan isha’i kishirya zan fara zuwa zance. Duk acikin wasan ne. Karki kuskura kice a’ahh.. “
Kit ya katse Kiran, Nabi screen din wayar da kallo ina maimata kalmar ‘zancen’ daya ce. Wane zance kuma bayan ya auro ni gaba d’aya? Naja tsaki Ina mai wurgi da pillown kusa da ni. Tashi nai na shige bandaki ina jinjina al’amarin Salman...
*GIM. SHAHEEDAH*
Gaba d’aya a razane take, Ta tattare ta koma k’arshen gado ta kudundune da bargo, kwallin idanunta duk ya zazzago, Tamkar ta fece da gudu yadda take a dimauce. Sai rawa jikin ta yake tana mai toshe kunnuwanta, Tana mai nanata,
“Wayyo Allah hajjaju na.. Gasunan sun zagaye ni, kingan su Kowanne harshen sa ya zazzago. Wayyo zasu cinye ni hajjaju. Kinga kwaduna zasu cinye ni hajjaju...”
Wajen kofar dakin kuma hadiman tane Kowanne ya tsaya cirko cirko sun rasa yadda zasuyi. Cikin haka saiga jakadiya Abu (Zainab)ta shiga hankalin ta a tashe,
“Ina gimbiyar take...?”
“Tana ciki tahana kowa ya shiga..”
Cewar batula babbar hadimar ta.
Kutsa kai jakadiya tai tashiga ciki, Tana shiga shaheeda ta kurma wani ihu hade da lailayo lafiyayyen zagi ta maka mata, Da doriyar jefa mata wani babban matashin kai dake kan gado,
“Subhanallah! Asssha gimbiya, Ni ce abu, Jakadiyar mai martaba, Ki temaka na kaiki wajen su Mama Huwaila ko kyaji sassauci kinji.”
“Wayyo Allah hajjaju gasunan zasu kamani.. wayyo .”
Haka shaheeda taita fada, Dakyar jakadiya ta kamota ta shiga lallamata kamar karamar yarinya. Har saida tasamu tayi bacci tukun Sannan, Suka temaka suka kaita sashen su Mama Huwaila.............
*GIM. KHADEEJA....*
Ina kwance ina kallon Chinese drama din love 020 naga message d’insa ya shigo wayata,
“Ki sakko ina parlorn kasa.....”
Ajiyar zuciya na sauke, Na hadu da gamo na ni dije. Banyi wata kwalliya ba don banga abunyi ba, Na dai shafa turaruka Na koma goga man lebe. Na zura abaya baka na yane kai na da mayafi. Sai dana bata lokaci kafin na fita na sauka kasan, Tundaga bene na hango shi a kasa. Ya zauna akujera yana danna wayar sa. Sanye cikin shadda sky blue, Yasha wata hula damanga. Wallahi kamar wani saurayi. Saboda yadda kwantaccen gashin bakin sa yayi masa kyau. Bansan sanda na gurde ba garin kallon sa, Sai ji na nayi ajikin mutum ya tallabo kugu na yana bina da kallo...
Kallon juna muke yi tamkar yaune rana ta farko da muka taba haduwa. Shi nasa kallon mai cike da soyayya ne tare da kulawa, ni kuma ina kallonsa ne ganin irin taimakon da ya bani cikin gaggayawa dan da tuni naci kasa wallahi. Iskar bakinsa ya hura min mai cike da kamshin mint, na lumshe ido ina kara bude kofofin hanci na dan jiyo kamshin.
“Zaki janyo min asara.” Naji ya fada a hankali.
Waro ido nayi na kalleshi da son jin karin bayanin wacce irin asara kuma? Dagoni ya yi tare da saka ni cikin kirjin shi, bakinsa kusa da kunne na yake magana.
“Idan kika fadi kika ji ciwo ai kinga nayi asara tunda zaki ji zafi.”
Ina jin haka nayi saurin ture shi ina yatsina fuska, kai tsaye na nufi gurin kujera na zauna ina kikkifta idanuwa kamar wata marar gaskiya. Kusa dani yazo ya zauna, sai kawai na samu kai na da jin wata irin kunyarsa, na kawar da kai gefe ina wasa da hannun kujerar.
“My love babu gaisuwa?” Yayi maganar yana son ganin fuskata amman na hanashi.
“An yini lafiya.”
Ya shafa kwantaccen sajan shi.
“Saffa - saffa dai tunda kin boye Kwana da kwanaki kin hanani ganinki.”
Uhmmm lallai ma wannan mutumin ni zaka sake rainawa wayo bayan ganin nawa da kake yi kare min lissafi kake shine zan yadda na ringa ganinka. Ya kuma matsowa kusa dani tare da rungumo ni zuwa gefen jikinsa, na shiga tutture shi amman yaki saki na.
“Ya isa haka my love, zance fa nazo ko kin manta.?”
“Haka daman ake zancen duk ka nanike ni sai kace yar air.?”
Sake matse ni ya yi a jikinsa bakinsa kusa da gefen fuskata yana fadin.
“No... No... No my love! Zance zamu yi irin na turawa. Ya gida dasu Ammi?”
Ya fada cikin son bagarar da wancen maganar.
“Ni fa gaskiya bana son irin wannan, turawa ai ba namu bane mu koma larabawa tunda daman a can kafi yin rayuwarka.”
Kamar na zuga shi sai kawai naji ya dakko ni gabaki daya tare da dorani saman cinyarshi, na shiga zillewa ya hanani koda motsi yana cewa.
“Dai dai kenan baby na, kinsan shi balarabe akwai...Iya tattali da kulawa akan abinda yake so, musamman ma mace.”
Lallai wannan bawan Allah yasan takan rainin sense, kiri-kiri yasan abinda nake nufi amman sai ya dinga bagarar da lamarina yana yin nashi.
“Ina son na samu lokaci na ziyarci dangin ki my love.”
Da sauri na juya Ina kallonsa cike da mamaki, ya akai yasan abinda yake cikin zuciyata? Kodai na yi masa zancen ina son zuwa gida ba tare da na sani ba? Kai Anya wannan mutumin baya amfani da aljanu wajan sanin abinda yake rai na? Sumbatar da ya kai min a gefen kumatu na sune suka sani dawowa daga gajeran tunanin da na shiga....
_Masu bukatar makeup.. Casual, special casual, simple glam, bridal makeup, fixing of lashes, gele and turban, modeling. Sai ya tuntubi BEELANAH BEAUTY.. Instagram handle: Beelanah_Beauty... Tana court road, Kusa da novomed, kano nigeria. 08034697302 Domin nemanta ko karin bayani sai a tuntubeta ta lambarta👈🏼Available to travel. #blush it up 🥂_
<><>
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
__I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_
_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_
_PG:23_
_BOOK:2_