← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 114

Sashe 52

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jakadiya ta tafi tana mamakin wannan kiran na lokaci d'aya. Shaheedah ta fara zuwa ta sanarwa, daman jiran kiranshi take yi taji shiru, hakan yasa tana jin kiran ta yi saurin tashi taje wannan dakin ta sanya wani kwalli da aka ba ta d'an so ake yi su hada ido da shi. Sannan taje ta dauki alkyabbar ta tayo waje, hadimanta suka biyo bayan ta cike da girmamawa.

KHADIJAA

____Ni kuwa ina zaune a cikin bayin nawa suna ta bani labarin wai basu taba ganin matar sarki tana hudd'a da bayin ta kamar wasu yan uwa ba iri na. Ina ta murmushi basu san ni babu abinda na sani a game da sarauta ba, dan haka zasu ga sabanin sauran dani. Jakadiya tayi sallama nace ta shigo, d'aya daga cikin bayin nawa ta kuma daga murya wajan ison da na yi. Ta shigo tana sunkuyar da kai tare da gaishe ni tana jinjina min ta kara da cewa.

“Allah ya taimaki amarya, farin wata sha kallon sarkin mu. Allah ya taimake ki turo ni akai na sanar dake cewa gwaggo ta Fada tana son ganin ki a can sashen mai martaba, Allah ya kara miki lafiya.”

Ras! Kirji na ya buga jin an ce sashen mai martaba. Ni kuwa na shiga uku, me zai kai ni gurin sa ni Dije? Kafin na samu amsa Jakadiya ta kuma magana.

“Allah ya taimaki farin cikin mai martaba, tace yanzu.”

“Ku... Kuma.. Ni ta ce miki?”

“Tabbas ranki ya dade, domin keda uwar gida tace a kirawo, yanzu haka na baro gimbiya ta shirya zuwa can d'in, saura ke yanzu.”

Wayyo Allah na ni kam na shiga uku, wallahi Allah bana son mutumin can bare har mu hadu. Tashin hankali ya bayyana a gare ni, jiki na ya fara kyarma ga wani tsoro da ya dirar min lokaci daya. Amman da na tuna tace Shaheedah ta tafi sai na fara kokarin tashi dan kar suce bani da kunya ko tarbiya ana kira na naki zuwa. Da yake tsoran dakin nawa nake yi, sai nace da daya a cikin masu yi min hidima taje ta dakko min hijabi na yana kan gado. Jin nace hijabi yasa Jakadiya yin magana.

“Allah ya taimaki amaryar mai martaba, kiyi hakuri zan dan yi katsalandan a cikin rayuwarki. Amman dai zai fi kyau kisa alkyabba, Allah ya kara miki lafiya.”

Haushi ya kama ni, saboda kawai ance naje sashen shi shine za a wani ce sai da alkyabba? Amman dan kar su dinga ganin gidadanci na sai na ce to, na tashi nabi bayan ta d'an kar ta fito, cike da tsoro na ce ta tsaya ni, na bude drawer na dakko guda daya nasa, duk da haka sai da na yafa veil a kai na saboda ba zan dora hular alkyabbar ba. Muka taso suma bayi na suka take min baya, hakan yasa naji wani gingirin gim, sai dai ban hana su ba dan bana son tsayawa sa'in sa dasu.

Wannan ne karon farko da na fito daga sashe na tun ran da aka kawo ni, duk da dare ne amman hasken da ya zagaye ko'ina a masarautar sai ka rantse rana ce. Gashi kowa harkar gabansa yake yi tamkar da rana.

Sai dai kuma me, mun fara tafiya daya biyu sai kawai naga tamkar an wuce ta kusa da ido na. Na rintsa ido bayan na tsaya cak ina karanto addu'a da kyar.

“Allah ya taimake ki, ince kodai lafiya?”

Na kasa yi mata magana sai kokarin daga kafa da nake yi amman na kasa, kafin kace menene tuni na yi wata irin faduwa, kai da ka gani kasan ture ni akai dan ko motsi bana iya wa. Hankalin su ya yi mugun tashi, tun kafin idanuwan mutane ya yo kan mu suka taimaka suka mai da ni cikin sashe na suna faman yi min fifita.

Jakadiya kuma ta ruga da gudu ta nufi wajan gwaggo ta Fada, lokacin Gimbiya Shaheedah har taje sai dai suna parlorn shi ba ta kai ga shiga ciki gurin Sarki Salman d'in ba.

“Allah ya taimaki ta fada ya ja da ranki uwar kowa.”

“Ina take?”

“Allah ya baki nasara, bayan mun fito dan zuwa kiranki, sai kuma aka samu matsala. Allah ya taimake ki gani kawai muka yi ta fadi, yanzu haka mun maida ita zuwa sashen ta.”

“Wannan wane irin masifa ne?”

Cewar gwaggo ta Fada cikin matukar mamaki, a ranta tana son gano wadan nan dalilan. Tabbas tasan akwai matsaloli a cikin masarautar nan, an raba sarkin kanshi da mahaifiyar shi, an shiga tsakanin shi da duk wani farin cikin sa. Da alama itama amaryar nan so ake a shiga tsakanin su, dama dazu a wayar da sukai taji yana tambayar ta waye Khadija a gare shi. Ai kuwa idan dai tsakanin su za'a shiga ba zata bari ba, daman tana son taga ranar da Allah zai sa Salman ya yi aure, gashi kuma ya yi dan haka ba zata bari a wargaza shi ba, sai inda karfin ta ya kare.

Ta mike tsaye tare da kallon Shaheedah daman ta tsani yarinyar nan, saboda bata da kunya ko miskala zarratin.

“Mai martaba bashi da lafiya yana a hannu Allah, ya rage naku kuyi masa addu'a idan kuna bukatar zama dashi dan kuci gaba da mulki. Idan kuma ya gundire ku to ku zuba mishi ido, ni na tafi.”

Tana kaiwa nan tai gaba abin ta, tana sane ta fadi haka tasan Shaheedah tana son mulkin sarki Salman, dan tasan idan ya mutu to dole ta koma b'ullo gashi dama babu d'a bare kuma 'ya. Hankalin gimbiya Shaheedah kuwa ya tashi matuka, ta nufi master bedroom d'in sai taga mijin nata kwance tamkar wani matacce, dan a tunanin ta ma ya riga ya mutu gaya mata ne kawai gwaggo ta Fada ba tayi ba.

Wani ihu ta saki tare da dora hannu a ka tana kuka tana ta shiga uku ta lalace, sai da Waziri ya dakatar da ita ya shaida mata be mutu ba sai dai yana cikin wani yanayi dan sai firgita yake. Sannan ne hankalin ta ya kwanta ta dinga tunanin kodai aikin su ne ya yi masa yawa har yake neman rasa rayuwarsa? Idan har Salman ya mutu ai ta shiga uku ba ta da sauran wani amfani a duniyar nan.

____Gwaggo ta Fada kuwa kai tsaye tasa aka raka ta sashen Dije, ta tarar da ita a takure jikin kujera tana nuna musu wani guri daban tana cewa.

“Gasu nan wallahi, gasu suna min dariya zasu kashe ni.”

Shigar gwaggon kuwa ta dago ta kalleta da gudu ta tashi ta nufi jikin ta tare da kankame ta tana cewa.

“Ki taimaka min Mama karsu kashe ni, dan Allah ki tausaya min ki fitar dani daga gidan nan bana s..s...s..son.....”

Gwaggo ta Fada taso shiga sashen Gimbiya Sa'adatu, amman ganin yanayi na yasa tace su kai ni motar ta da driver ke jiran fitowar ta. Bata tafi da kowa ba daga ni sai ita ko kayana bata dauka ba ta tafi dani zuwa gidan ta.

Tun a hanya take tofa min addu'a, ni kuma tunda muka fito daga masarautar naji na dawo cikin hayyacina. Kai na akan cinyar ta sai faman shafa min kai take yi, duk da ban san ko wacece ba, sai naji hankali na ya nutsu da ita. Karatun da take ta faman yi min yana sani nutsuwa wanda yaushe rabon da nayi shi saboda rashin nutsuwar zuciya da bani da ita. Muna zuwa aka bude gate, shima gidan tsarin na sarauta ne, sai dai bai kai girman masarauta ba.

Driver ya yi parking nan da nan wasu mata masu kaya iri daya su hudu suka iso inda muka tsaya, suka bude mana mota tana rike dani tace.

“Fito da bismillahi Khadija.”

Nayi kamar yadda ta umarce ni, muka sakko sannan suka rufe motar suna bin mu a baya kamar dai yadda ake yi a can gidan sarautar da na baro. Babu laifi gaskiya katon gida ne, muka shiga wani katon parlor wanda ya gaji da haduwa, kai ba kace tsohuwa bace a cikin sa saboda yadda aka kawata shi da abubuwan zamani. Guri na samu na zauna, ita kuma ta shiga wani daki, ba ta dade ba sai gata da wata sun dawo parlorn, gwaggo ta Fadan tace min.

“Ga yar uwa nan nayi miki, yar auta ta ce, sunan ta Maryama. Tayi aure tsawon shekaru tara Allah ya yiwa mijin rasuwa, bayan ta gama iddah ta dawo nan shekaru biyu kenan, yaran ta biyu Aliyu (haidar) da Aisha (Humaira) suna daki sun yi bacci.”

Daga ni har ita kallon juna mukai kafin ta maida kallon gurin gwaggo tace.

“Gwaggo wacece wannan din?”

Sai da taje ta zauna akan shimfidarta ta musamman, sannan ta janyo ruwa tasha tace.

“Wannan da kike gani Gimbiya ce. Bari na yi miki gwari-gwari, ita ce amaryar mai martaba, na dakko ta ne saboda da wasu dalilai.”

Da sauri Maryama ta kuma kallo na tana faman sakin murmushi da alama taji dadi da na kasan ce matar sarki Salman. Sai kawai naga ta durkusa a gaba na tana gaishe ni, na yi saurin riko hannunta ina girgiza kai na.

“Ki tashi dan Allah Addah Maryama.”

“Girmanki ne ai gimbiya Allah ya riga da ya baki. Naji dadi gaskiya kuma ina d'aya daga cikin masu son auran nan da mai martaba ya karo, Allah ya ja da zamanin ki gimbiya.”

Ni duk sai ta sani jin nauyin ta, gefe guda kuma haushi naji da take murna na aure shi.

“Ki raka ta tayi wanka a samu sababbin kayan bacci a bata tasa kafin gobe kije ki samo mata wasu da zata dinga amfani dasu.”

“Toh gwaggo, ai ni kin gama min komai wallahi da kika zo da ita nan. Bismillah gimbiya mu shiga cikin dakin.”
Chapter 52 · 0% Book details