← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 114

Sashe 85

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi maganar cikin wani salo da alama dai yadda nake maganar ya burgeshi ta yadda yake ta faman Murmushi. Nai masa shiru ni dai sai faman lasar lips nake irin na naci dadin nan, ko ganewa ya yi lashewa nake yi? Naga dai ya taso bayan ya karbi bowl din ya ajiye tare da nufowa jikina. Banyi aune ba sai ji nayi ya kwantar dani kan gadon yasa harshensa saman lips dina yana lasa, ni kuwa tsabar mamaki mutuwar zaune nayi Ina fito da kwayar ido cikin din bin mamaki.

Sai da yaji baya jin testing d'in komai sannan ya bar abinda yake a lips din, ya kalleni yana kwantar min da gashin gaban goshi na. Hakika yana matukar son baiwar Allahn nan, yana junta a duk wani sashe dake cikin jikinsa. Murya a raunane yace dani.

“Allah ya maki albarka.”

Dadi ya kamani jin an bani naci na koshi kuma an bini da addu'a lallai wannan mutumin be dauki duniya a bakin komai ba, yadda yake tarairayata Ina jin ko Mas'oud d'in da na kwallafawa rai ba zai min haka ba, musamman yasan Ina mugun son shi. Ji nayi ya dagani tare da sanya hannu ya dagoni na zauna sosai yace.

“Ki huta lafiya zanje sashe na zamu yi maganar daurin auren su Munaya dasu Abdulqadeer.”

Ban samu kwarin guiwar amsa masa ba saboda al'amuran sa sun fara girgiza tunani na. Ya mike a hankali ya nufi gurin kofar da ya biyo yana kallo na kamar baya son mu rabu haka ya hakura tunda ana can ana jiransa kar su fara kwashe masa albarka da sauke mai kwadon tsinuwa dan ba kirki gare su ba.....

<<<<<>>>>>>>

Da daddare saina samu zuciyata da yin wani irin rauni akan yin hidimarsa gareni. Na fara wani tunanin cewa shifa sarki ne, sarkin ma wanda ake ganin girman rawaninsa sama da wasu rawaninnikan a kasar nan. Shi d'in fa jinin milki ne d'an gaske, matashin sarki maiji da kuruciya da sanin darajar lokacinsa. D'an gatan da duk kaddara ta juya masa zukatan dangi zuwa ga kiyayyarsu akan mulkin duniya. Anya kuwa zuciyata da kalmomin bakina suna mini adalci wajan yi masa furuci.?

Ai koban girmamasa a matsayin miji ba ya cancanci girmamawa a matsayin na shugabana mai mulkin jahata. Ya cancanci girmamawa na matsayinsa na babba gareni a shekarun da kuma hankali.

Sarki Salman bashi da wata makusa a halittar jiki data mu'amular rayuwa. Tunda nazo gidansa bai taba munani da wani furuci na baki ba balle a aikace. Ya bani jin dadin rayuwa kamar kowacce mace dake ji da kanta a gidan. Ya bani girma irin na matarsa a idanun jama'ar masarauta dama bani ragamar kula da wani sirrin rayuwarsa. Idanma ta gaskiya za'abi nice na tura rayuwarsa cikin tawa a dole ta hanyar acting da nake yi saboda matarsa.

Tabbas Allah shine shaida ta, bana jin sonsa a zuciya ta. Amma kuma ban tsanesa ba. Sannan ina kawo masa maganar saki ne dan kawai na samawa kai na lafiya a wani lokacin. Sannan bazance bana son Mas'oud ba har yanzu. Sai dai sonsa ya ragu a raina sosai a yau d'in nan ba kamar sanda muna a tare ba. Bansani ba kodan bana ganinsa yanzu ne shi yasa oho.. Ko kuma saboda irin kulawar da Salman yake bani musamman ta dazu da ya shiga kitchen da kansa dan kawai ya faranta min....?

Iskar da aka huramin akan idanuwa ya sakani sauke nannauyan numfashi dan ban fargaba ashe na fada duniyar tunani mai zurfi. Da wannan damar Salman yayi amfani wajen kare min kallo tun dazun. Ganin ina kara zurfi ne ya sakashi maidoni cikin hayyacina.

“I love you Deejah".

Ya fada a hankali gab da fuskata dan ya rankwafo kaina ne. Da sauri nayi baya da jikina ina kyakykyafta idanu zuciyata na wani irin bugawa a karo na farko. A salon da yayi maganar ne yayi matukar tada tsigar jikina. Baya na cigaba dayi yana bina har na kwanta akan gadon shima ya kwanto kaina.

Idanu na zaro waje sosai zanyi magana yayi saurin dora yatsansa saman bakina yana kadamin idanunsa da suka sauya launi. Cikin sarkeni da su yace,

"Ban cancanci a soni bane ma'am?Deeja menene laifin ne dan naso abinda ya dace da ni?"

Da sauri na girgiza masa kaina ina kyafta idanu, dan yanda yake magana yana matukar tada min da tsigar jikina. Muryata na rawa na ce,

"Ni bance bana sonka ba. Kawai dai.....” Na kasa karasawa.

"Kawai dai me?"

Ya tambaya yana dora hancinsa a gefen wuyana da wani shegen Salo na saukar da numfashi.

Jikina ne ya fara rawa. Zan turesa ya rike min hanu yana cigaba da aika min salon dana ke ganin tsantsar mugunta ce.

Bakinsa ya dora saman kunne na ya dan ciza. zabura nayi amma ya sake danneni yana kara raunana muryarsa.

"Ki sanar min saboda me?".

"Kafi karfi na." Na bashi amsa cikin subucewar baki.

Da sauri ya dago yana kallona da idanunsa da suka sake komawa kalar tsoro.

"Khadijah banfi karfinki ba, kece ma kikafi karfina ai.” Saurin girgiza kaina nayi kwalla na cika min idanu.

"Mai martaba kaine kafi karfina. Kai fa sarki ne, sarkinma mai tarin abubuwan kwatance a gaban wasu sarakunan. Kai dan gatane mai tarin ilimi da nasaba. Kai jinin mulki ne dan masu mulki jikan masu mulki. Kai mai ilimi ne da tarin dukiy.......”

"Shiii...." Ya fada da sauri yana kada min idanunsa. Zai yi magana nima na girgiza masa nawa kan hawayen da naketa kokorin rikewa suka zubo min a kumatu.

"Ka barni na fadi abinda yake gaskiya dan Allah. Muna da banbanci sosai, kanada tarin abubuwan da suka ninka wadanda na fada a baya. Ni kuwa talakace, yar talakawa gaba da baya. Yar kauyen kayau. Bawani tarin ilimi ne da ni ba. Ba wata nasabar kwatance ce da ni ba. Bani da wani abunda tarihi zai nuna matsayin dangantaka ta. Tayaya kake tunanin zaman aure zai kasance a tsakanina da kai? Hakan tamkar tauyewa kanka da martabarka kayi a matsayinka na sarki. Sarkinma da ko a gaban wasu sarakunan sarki ne. Kayi hakuri matarka tafi cancanta da samunka dan itace ke gogayya da kai bisa duk wadannan abubuwan dana lissafa maka takawa. Ni kuwa ka barni na tsaya dai-dai matsayi na kamar zaifi dacewa da ni nim........."

Saukar tausasan labbansa akan nawa ya hanani karasa abinda naso fadan. A karan farko naji bazan iya hanashi yin hakan ba a gareni dan shi d'in mutum ne mai son ganin farin ciki na. Nima sai kawai na lumshe nawa idanun tare da kankamesa saboda tsumar da jikina kemin da gudun da zuciyata keyi tamkar zata faso kirjina ta fito. Haka shima Ina Jin tasa bugun zuciyar.

Tun ina daukar al'amarin nasa karami harya fara zarta gajeren tunanina. Dan kuwa da gaske sai ya tabbatar min tunanina gurbatacce ne. Sai da ya tabbatar nayi laushi bani da ko karfin yin numfashi mai nauyi kafin ya barni. mirginawa yayi ya koma kasa ya maidani saman jikina. Cikin wata kalar murya mai rauni da laushi yace,

"Duk wadannan abubuwan bazasu kasance nawa ba sai da ke gimbiyar Salman. Ki yarda kece mahadin rayuwar Salman bin Aliy. Babu ruwana dake wacece, Babu ruwana da nasabarki, babu ruwana da iliminki, babu ruwana da abinda wani zai fada a kanki. Ke nake so a hankanki. Tarbiyyarki ta isheni komai. Please ki yarda na nuna miki matsayinki a gareni Khadijah. Ki yarda na nunama duniya ke wacece a gareni. Ki yarda na shelantama masu mulki irina su san cewa ba sai mace tana da irin nasabarsu ko nagartarsu bane ta cancanci zama matarsu. Ki yarda nayi koyi da mahaifina Khadijah. Dan shima ya auri mahaifiyata da irin matsayin da kike ganin kanki da shi a lokacin da yake matsayin sarki. Wannan shine sanadin girmama kiyayyarta da tamu a cikin masarautar basannabas. Me yasa bazaki amince tarihi ya sake maimaita kansa ba a garemu dan mu sake zama mabudin karya lagon kaifin duk wani jahilin dake tunanin yar mulki sai dan mulki? Talaka sai dan uwansa talaka.”

Hawaye nake cigaba da zirararwa ina saurarensa. Ya sake dora bakinsa kan kunnenna yana rada sosai yace,

"Ki bama Salman bin Aliy bin Salman dama Khadijah. Na miki alkawarin a wata daya kacal sai na canja zuciyarki ta zama mahadin tawa."

Babu shiri na dago da sauri muka hada idanu. Wani sassanyan murmushi ya sakar min yana kashe min ido daya da dage gira yace,

“Na yarda da kaina.”

Sosai yanda yayi maganar ya bani dariya. Nai saurin fisge jikina na sauka daga nasa nai gefe ina murmushin daya subuce min ba tare dana shirya ba.

Shima murmushi yake yi dan har ina jiyo sautinsa. ya murgino ya kwanta a bayana yana sake fadada sautin murmushin nasa.

"Gaba daya y'ar jarida kin maida Salman kamar ba sarki ba. Ni mantawa ma nake da wata sarauta idan ina a gabanki. Da gaskefa a kanki na yarda sarki a cikin gida bawa ne matarsa ke zama sarkin. A waje ne kawai muke fankama da bude hanci.”

Ai bansan na fara kyalkyala dariya ba da wannan maganar tasa. Sosai na shiga yinta shima kuwa yana tayani. Nace,

“Karka saka yan masarautar nan su halakani lokacin mutuwata bai yi ba.”

"Ashe kuwa suma duk zasu halaka dan mayaki na gaske zan koma."

"Tab, ai nasan yanda kake din nan kullum a kwance ba karfi zaka yi ba.”

Nai maganar ina kokarin tashi zaune. Saurin rikoni yayi na fado kansa. Ya sake tura idanunsa cikin nawa yana wani kankance su.

"Karki damu, zamu shiga filin daga nan da lokaci kankani. Kinga sai ki banbance idan zan iya ko bazan iya din ba."

Ban fahimci inda ya nufa ba. Amma yanda yayi maganar ne cike da shakiyanci ya sani ji a jikina da wata manufa ya fada. Nai saurin kwace jikina ina fadin,

"Ni Dije meya hadani da yaki ina mace. Ai sai ku maza.”

Dariya yayi shima yana tashi zaune. Yace,

"To, lokacin ne dai zai nuna mana ai".
Chapter 85 · 0% Book details