Sashe 8
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ni da hakimi mun gama magana, Za’a cigaba da karatun nan, Sannan ‘yayayen ku su amfana kuma ku amfana dasu nan gaba. Amma babu tilas wanda yaga baya ra’ayi shikenan. Amma kada nan gaba nasara ta samu yaran da sukai karatun nan kuzo kuna dana sani. Zan baku kowanne takaddu na shiga makarantun nan guda bi-biyu ku bawa ‘yayan ku domin shine fom na gurbin karatun. Kunga masu wayo tuni ‘yayan su sunyi nisa da karatun, Kuma wannan makaranta da naku zasu fara itace Idan suka kammala zasu samu fannin shiga jami’oi. Hakimi ya tabbatar min cewa sarki dake birni yayi alqawarin samawa yaran mu guraben karatu a jami’oin su dake birni. Saboda haka yanzu zan bawa kowannen ku takardun nan guda biyu. Ruwan ku ne ku sanya su a makarantun nan, Ruwan ku ne ku kyale su suyi ta hargitsa mana gari, Tunda kunnu na bani da martaba a idanun ku..”
“Tuba muke ranka ya dade..”
Cewar malam sagiru dake gefen mai gari a durkushe. Sauran suma suka fad’a da karfi Kan su a kasa. Mai gari yaja tsaki kafin ya janyo takaddun a gefe ya shiga kiran sunayen su yana babba su. Har akazo kan Malam Bashari mahaifin Dijangala. Mikewa yai ya isa gaban mai gari ya durk’usa kana ya mika hannun sa cikin girmamawa. Mai gari ya mika masa yana murmushi,
“Malam Bashari, Har abada nasan baka cikin masu yimin zambo cikin aminci. Ba zaka taba zuwa kayi dani ba awani wajen. Tilasta ka akai, Kaje a yan cikon masu korafi, Ko’ina ne zan shedaka wallahi..”
Malam Bashari yayi murmushi kafin yace da mai gari,
“Godia nake yallabai, Allah ya saka da alkhairi.”
Mai-gari yayi murmushi kana ya mika masa takaddun guda biyu. Hannu biyu Malam Bashari yasa ya karba, Da ganan aka shiga muhawara kowa yana tofa albarkacin bakin sa akan makarantun da yaran su zasu fara yi. Kafin a watse kowa ya kama hanyar sa. Malam Bashari ya taho gida zuciar sa ayyana yadda Gajiyalle zata karb’u maganar. Kafin ya k’arasa gida yaci karo da dandazon yara anata tafa hannaye,..
Fada ya kaure tsakanin Dijengala da Ummin Nasiru mai guga. Sai kaurewa suke suna tima juna a kasa. Na kururuwa kafin na daga hannu na watsa baya.
“A hayye! Ke Ummin gwaigwai, Ba tsoron ki nake ji ba. Da wani gahin ki a tsaitsaye kawa hammatar dan iska. Banza bazara iskar damuna.”
Na karasa fada ina karkadawa Ummi hannu. Ummin ma taja shewa kafin ta finciko ni muka kara haurawa,
“‘Ni an gaya miki tsoron ki nake ji? Kazama kawai me warin kwata.”
“A hayye nanaye! Kece kazama ai. Banziya wadda ke hamamin doyi. Ummi gwaigwai. Yanzun sai na caskala ki a wajen nan.”
Na karasa fada ina jan tsaki. Na shatalo kafar Ummi na nakata da kasa. Ummi ta hau kuka, Dai dai sanda Baffa na Malam Bashari yazo wajen. Duk rashin ji na ina tsoron Baffa na sosai, Ko kadan banason b’acin ransa.
“Kai ku bari, Maza kowa ya tafi gida, Tashi kinji! Yi hak’uri. Bata hak’uri, Ummi na muje gida..”
Baffa na ya karasa fada yana nuna Ummin Nasiru mai guga da hannu, Cuno baki na nai gaba, ciki ciki nace,
“ ‘ki hak’uri”
“Yasin ca tai ‘ki hakuri ba Yi hak’uri ba..”
Ummi tafada tana tafa hannaye, Zare min idanu Baffa yai alamun na bata hak’uri. Wayyo Allah na. Bana son bata hak’uri, Idan ba Baffa ba, Ko Gajiyalle ko Idan nayi ba dai dai ba shine nake bada hakuri, Amman ya za’ai itace da lefi ace na bata hak’uri. Nasha mur kana na juyar da kai na,
“Baffa yar gala-gala muke yi, Kaga gidan dana zana kuwa? Kawai Ummi tazo ta tarwatsa mana ta tattake. Kuma ace na bada hak’uri? Haba Baffa dan Allah kada kace na bata hak’uri.”
Baffa ya janyo hannu na gefe ya dafa kai na kafin yace,
“Wanda yabada hak’uri baya faduwa Ummi na, Ko bake bace da laifin kiyi hak’uri kinji? Ki bata hak’uri, Saboda mutanen wajen nan siyi koyi dake. Kinga nan gaba za’ai shedar ki.”
Daga kai nayi badan wai naji dadi ba sai dan gudun bacin ransa, Har gaban ta naje, Na wulkita idanu na na zabga mata uwar harara, Na mata kallon zata sani bata sha ruwa ba, Kafin na watsa hannu baya na buga zani hade da murgud’a baki nace,
“Kinci saar Baffa na wallahi, Da wallahi sai na caskali ki, Nayi kullin tara sisi dake, Gajabura kawai. Badan halin ki ba.. Kada Allah Ubangiji yasa ki hakura. Aikin banza kawai. Mts! Allah ya...b..”
Baki na ya shiga min nauyi, Har ga Allah banason bata ha’kurin nan. Amma ala dole na bata Saboda Baffa yace dole ne na bata. Na bata rai kafin na sanya karamin danyatsa na na sosa hanci na. Dakyar naja iska. Wai ni Dijengala ni zan bawa wata hak’uri.? Iska na sake ja na sauke kafin nace,
“Kiyi hak.. h.. hakuri.”
Ina gama fada nai gaba ina hawayen bakin ciki ganin yadda Ummi ke murna harda shewa, Tab ai kuwa bashi taci. Sai na yagalgalata narantse da Allah . Baffa ya cimma ni, Na cuno baki gaba dak’yar nace,
“Sannu da zuwa Baffa..”
“Yauwa yar baffan ta.. ko kefa! Gwara da kika bata hak’uri kinji? Kinga mutanen dake wajen laifin ta zasu gani.. Mahakurci mawadaci.”
“Toh Baffa..”
Na bashi amsa bawai don maganar sa ta hige niba, Gida muka higa , Gajiyalle na tsaye a turken dabbobin ta tana kirga yawan su, Kullum haka take yi sai ta kasafce kansu hankalin ta yake kwanciya. Daganan ta koma kan kajin ta da zabbin ta. Tabe baki nayi, Nayi gaba abuna. Baffa ya karasa bakin dakin sa ya zauna dakyar yana salati. Wasu takardu ya zaro a aljihun wandon sa dake lilo zai yage ya ajiye akan taburma,
“Salamatu.. (Sunan Gajiyalle)”
“Na’am Malam! Ya akai?”
Tabashi amsa tana daga tsaye gandar-dar..
“Kya dai zauna ko? Abun arziki ne ya tunkare mu.”
Gajiyalle ta washe baki. Nima na ajiye robar dana kamfaci ruwa na kwasa a guje. Ban dire a ko’ina ba sai gaban Baffa. Duk azato na duddugar tsire ya sayo ko Kan babban kifi. Gajiyalle ta dankaramin harara nima na rama ina gatsine..
“Guzumar ubanki! Kaga yar bankadaddiya.”
Na mike ina cuno baki,
“Yasin Baba ta ba bankadaddiya bace ehe, Allah ya jikan ta.”
Tayo kai na zata dake ni na goce ina watsa hannu baya, Mudi ya shigo yana jin rediyon sa ta naci. Cikin daga murya yace,
“Ke ga wani yaro can awaje yana kuka wai kin jefamas taya a kwata. Shi da yayan sa..”
“Tashi kije ki san yadda zaki ki dakko masa tayar sa, Uwar yan jawo masifa. Wannan yarinya sam bakida kirki.”
Tabe baki nayi na kalli Baffa kafin nace,
“Kana ji ko Baffa, Ina cikin tafiya shi ya fara tsokana ta. Musa ne fa dan Malama Harira me siyar da wainar yar bagalaji. Haka kawai ya tsokane ni wai Dijangala tsogalgala me kama da zankala ‘koki. Shi ne ni kuwa na kwace tayar dayake wasa da ita nai cilli da ita a kwata. Ai ba lefi na bane ko?”
Baffa na ya cire tagumin. Kafin ya mike ya fuce kawai, Ina jiyo shi shida Musan da yayan sa. Da alamun hak’uri ya basu. Can naga ya dawo ya zauna. Ya kira Mudi shina ya zauna.
“Yauwa Salamatu ga takardu nan daga birni sarki ne ya mana hanya daga shugaban kasa. Tallafin karatu ne da yaran mu zasu yi. Kyauta har su kare su shiga gurbin jami’a..”
Gajiyalle taja tsaki kafin ta mike tana zabgawa baffan mu harara,
“Ai karatun arna? Kan babban bala’i! Yasin ba dai agidan nan ba? Karatu fa kace? Mudi ko zakai boko?”
Mudi ya mike yana girgiza kai,
“Ni lodin mota zan fara. Gajiyalle zata sayamin mota idan na kara manyan ta. Bazanyi boko ba gaskia “
Tab tunowa nayi nima naga yadda ake boko a talabijin din gidan su Nafisa. Yara kamar a bursun din kauye. An hanasu Fita anata koya musu shirme wai shine karatu. Mikewa nayi nima na dire tsallen albarka, Kafin na kwararo rantsuwa na dire ina watsa hannu na,
“Gaskia bazan yi bokoko ba, Yan bokoko ba basa karatu basa sallah, Sai Karatun arnaye. Idan nayi boko na nutse.. “
Baffa ya duka yana rok’on mu,
“Ku temaka min kuje karatun nan. Wallahi Za’a amfana. Ina jin kunyar mai gari na mayar masa da takardun nan. Salamatu kisa baki.”
Gajiyalle taja tsaki akaro na ba adadi kafin tace,
“Salon iskanci akeso a koyawa yaran karkarar nan. Suyi ta cikin shege ko? Akan me Za’a ce yaran mu suyi boko? Saboda hanyar neman abincin mu su lalace ko? Gaskia Mudi bazai yi boko ba. Idan yar ka zata yi to? Amman dai ai Gwara Kiyi talle da boko ko Dije?”
Kad’a Kai na nayi na dashe baki.
“Sau dubu miliyan Gwara nayi talle da dai nayi boko. Bazan yi ba gaskia. Ni talle zan yiwa Gajiyalle. Na girma ayi aure na ko Baffa?”
Baffa na yayi ajiyar zuciya kafin ya dube ni dakyau yace,
“Yanzu da kiyi karatun gwara kin d’au talla kina yawo a gari? Ba kince min kina sha’awar yadda kike sauraron na radiyo idan suna magana ba? Kuma kikace na Abun kallon gidan kansila ma yana burge ki. ? Kinason ki rika ri’ke musu abun da suke magana ko? Yanzu bakyaso kin watsar ba zaki cinma burin ki ba?”
Tunani na shiga yi, Gaskia bazan iya zama kamar a bursun ba, Gwara nayi tallen.
“Nide gwara tallen..”
Gajiyalle taja guda da shewa kafin tace,
“Yauwa yar gari. Zanci gaba da baki kayan talla kina yi min.”
Baffan mu ya kad’a kai hade da mikewa ya dube ni,
“Bazan tursasa ki ba. Allah yaba da sa’a.”
Yana gama magana yai fucewar sa. Ni kuwa dadi nake ji zan fara ci gaba da talla ina samun kudin kashewa koda cikin dabara ne. Acikin satin Gajiyalle tafara doramin tallen kayan koli dana turaruka da take sarowa a birni. Inata talle na har aka bude makaranta. Nayi mamakin ganin kawaye na duk sun fara zuwa. Na sheke da dariya na kance,
“Mahaukata, Banda shirme me akai da boko? Sun zama arnaye. Harda Siyama kawata aminiyata. Lalle siyama batada wayo. Tabdijan.”